Skip to content
Part 1 of 2 in the Series Ina Matsalar Take? by Rahma Sabo

Tsoro, ‘yan adam na cikin halin tsananin ƙunci, fargaba, da kuma rashin tabbas. Haƙiƙanin gaskiya an jarrabi al’ummar wannan ƙarnin da zarmiya haɗi da son zuciya a kan ɗan abin da bai taka kara ya silmiye ba. Mafarkanmu a kullum su ne kuɗi, mutuncinmu ya ta’allaƙa da me mu ke da shi, ƙarafen Nasara a wannan zamanin sun zamto ƙarshen zance sun yi shuhura haɗi da kaiwa ƙololuwar daraja da kuma mutuntaka. Kai bara na yi maka ta shashasha ko kai sauna ne muddin ka na da sukuni a kan kalle ka a matsayin ka zarce aula musamman ma a ce za ka damƙa ka miƙa; kai ko zama za kai da mutane ka rinƙa shero mu su muddin ka na da arziƙi za su yarda da zancenka.

Hatta da rayuwa a yanzun ta zamo a bar sayarwa, ran ɗan’adam ƙiri-ƙiri za ka ga an kasa a tire ana neman wa za ya saya. Kai kanka da ka ke da ran ba a ƙi a zauna ana musayar ciniki da kai a kan yadda za ka samu ran naka ya kuɓuce ba.

Ga tsananin matsi ta fannin tattalin arziƙi mu na fuskanta. Ƙunci ya yawaita a zukatan mutane ga tsananin tsoro da fargabar me gobe za ta haifar, idan fita ka yi ba ka da tunanin za ka komo gida. Idan ka na cikin gidan tsoro ka ke ka da baƙaƙen baƙi su ka kawo maka ziyarar bazata. Na rasa ta ina matsalar ta ke, a gurin shuwagabanni ko kuma mabiya? Kullum tambayar da na ke watsawa kaina kenan tambayar da na haƙƙaƙe ba ni ba wani na ma bai da amsarta.

Kullum cikin bibiya da saƙa zaruruwan labaraina na ke, duk a ƙoƙarina na son lallai sai na binciko ya abin ya ke? Kuma yaushe ne za a gyra.

Zaruruwan labari ne masu mabanbanta ma’ana da kuma jirkitacciyar fuska, ƙulla tarin zarurruka labarin da na saƙa abu ne mai sanya tsuma da kuma janyo alhini daga mabanbantan zukata. Ma’anar ɗaya ce ga wanda ya dube su ta fuska ɗaya; ta wata fuskar kuma zarurruka labarin sun sha banban da juna. A kuma loto guda zan saƙe duka zaruruwan na kuma tayar da ginshiƙin labari mai ma’ana guda ta kowace fuska.

Rikirkitacciyar unguwa ce ta talakawa da kuma masu rangwamen gata, mai ɗauke da rukunan gidaje a marmatse da juna, tsananin cunkusuwar da unguwar ta yi zai fara baka shayi da kokonton anya kuwa ɗan’am ɗin da ke rayuwa a unguwar nan ya na samun wadatacciyar iskar oxygen kuwa. Idan kuwa su na samu to tabbas su na yiwa Ozone mummunar ɓarna, kasantuwar su na aika mata da iskar nan ta carbondioxe hakan ba ƙaramin gudunmawa zai bayar gurin janyo ɗumamewar yanayi ba. Duba da yadda unguwar ta cunkushe babu gurin da tsiro zai samu mafaka. Ikon Jallala gagara misali.

Ɓarin unguwar daga hannun dama bola ce a tsube ta tsume har ta mayar da gurin tamkar dagwalo babu kuma wanda ya damu da ya gyra. Magudanar ruwan unguwar ta toshe ta ko’ina ruwa samawa kanshi hanya ya ke, hakan sai ya tuno min da waɗansu baitukan wani mawaƙi da ya ke cewa.

” Shi ruwa ba kai ke gare shi ba,

muddin ka hana shi hanya ya wuce,

zai hankaɗe ko ma waye ya wuce.”

Ya kamata a ce mutanen unguwa sun haɗu sun yi gangami sun yashe magudanar ruwan nan, ita kuma gwamnati ya kamata a ce ta kawo mota ta kwashe mu su bola ko domin rage yawaitar cutttuka masu saurin yaɗuwa kamar su: amai da gudawa, zawo, zazzaɓin cizon sauro da dai sauransu. Sai ka rasa takamaiman inda matsalar ta ke.

A tsakkiyar unguwa wani ɗan tsukakken gida ne, mai ɗauke da ɗakuna ƙwara biyu cal. Kallo guda za ka yiwa gidan ka yi na’am da cewa kinko ya samu gurbin zama a ciki. A zaune a cikin ɗaya daga cikin ɗakunan gidan, mace da namiji ne su ke tattaunawa fuskarsu ɗauke da zallar alhini da damuwa.

Cikin muryar kuka matar ta ke magana da mijin ta ce,”yanzun haka za mu zuba idanu, rayuwar Safwan ta salwanta?”

“To Amina ya za mu yi da abinda ya gagari wuta? In ji kishiyar ƙonanna. Ganin idanunki kullum fafutuka ta yaya za ai na ji ko na ga wanda zan samu labarin yaron nan a gurin shi, ba na barci ba na cin cikakken abinci kullum yawo na gidan radiyo ko na talabijin amma shiru ki ke ji wai malam ya zari shiryawa.”

Cikin yankewa da rashin tabbas ya ke maganar. A ɗatace ta kalle shi har yanzun kwarmin idanunta da hawaye ta ce.

“Ni yanzun addu’ata ma Allah ya nufa a ce masu garkuwa su ne yi awongaba da shi, su kira mu mu ji ko nawa za a ba su”. A hanzarce ya miƙe ya dakatar da ita cikin sauri ya ce,” ki na cikin hayyacinki kuwa? Yanzun ina mu ke da taro ko sisin da za mu bawa ‘yan garkuwa? Mu da abin da za mu saka a bakan salati ma ya ke zame mana jangwam, ki yi gaggawar tofar da baƙin miyau ka da kallon hadiri ya sanya ki wanka da kashi.”

“To na ji, kuma na janye”. Ta faɗa a hankali, amma kuma ƙasan ranta na ayyana cewar da wata jagwal ɗin ƙwamma wata. Ita a yanzun ta gwammaci kiɗi a kan satu, domin ko banza idan ‘yan garkuwa su ka ɗauke shi za su tausaya masa kuma ma ko banza al’ummar manzo za su agaza da kuɗin fansa.

Shi kuma tunanin shi na bashi cewar tabbas matar tashi, ta samu motsuwar ƙwaƙwalwa sakamakon tarin damuwa da ke cunkushe a ƙirjinta. Ga nashi hasashen da kuma hasashen kowane aƙili bai hango inda garkuwa da mutane ta zamo mafita ba.

Hanyar da za ta miƙa ka waje ya nufa a kasalance ba tare da ya ce mata ko kanzil ba. Tafiya ya ke tamkar zai kife, zuciyarsa na saƙa masa abubuwa da dama buri da fata a gare shi ina ma a ce hawaye zai fito masa tamkar yadda ya ke fitowa matarsa? Ya fi ta jin takaici ya kuma fi ta shiga damuwa don ko babu komai ita ta na samun sa’ida ta hanyar zubar da ruwa daga idanu.

Tafiya ya yi ta tsawon milamilan da idan ka turke shi da bindiga ba zai taɓa iya zayyane maka ƙiyasinta ba, kawai a binda zai iya sanar maka shine ba ƙaramin nisa zango ya yiwa gida ba. Har ya gota gurin da kaɗan idanuwansa su ka yi masa tozali da galurar fenti da kuma tambarin giwa, cikin hanzari ya doshi gurin zuciyarsa ɗauke da tsantsar farin ciki ya ɗan safarar da ke tafiya a cikin sahara babu gida gaba bare kuma baya, guzuri ya yanke jallo ya ƙafe. Kwatsam ya ci karo da sassanyar ƙorama(OASIS) a gefe kuma ga bishiyar dabino da Allah ya wadata ta da nunnanun ‘ya’ya(fruit).

“Malam dakata! ba ka san nan ofishin ‘yan sanda ba ne, za ka danno mana kanka tsaye?” Ɗan sandan da ke gadin gurin ya dakatar da shi. Tun daga nan murnarshi ta fara juyawa ciki.

“Na sani”. Ya mayar masa da amsa haɗi da yunƙurin danna kai, ko ma ta halin ƙaƙa.

“An faɗa maka caji ofis ɗakinka ne da za ka shiga yayin da ka ke so?”

“Na san ba ɗakina ba ne, buƙata ce ta gaggawa na ke da ita”. Haƙurinsa fa zuwa yanzun ya soma kaiwa ƙarshe, burinshi kawai ya bar shi ya shiga. Ɗansandan kuma cigaba da kare ƙofa, domin ya fara kokonto da shakka a kan mutumin nan.

“Malam idan har ba ɗan ta’adda ba ne to tabbas motsattse ne kai.”

“Ni ba na cikin guda daga waɗanda ka lasafta, ni dai wanda damuwa ta yiwa kanta a zuciya ne kuma ganin wannan gida ya sanya farinciki a zuciyata ina jin tamkar matsalata ta kau.” Zuba masa idanu ya yi tamkar ya samu majigi, har ya kai inda ya ɗiga aya sannan ya magantu ya ce,”da fari ka bada abinda za a sayi takardar rubuta jawabi, sannan na shigar da kai ciki su rubuta maka sannan su saurare ka.” Girgiza kai ya yi, haɗi da sanya hannu a aljihun wandonsa ya zaro aljihun duka biyun ya ce,” ka ganni nan ba ni da ko ƙarfanfana, yarona ne da ya ke matuƙar taimaka min gurin gudanar da al’amuran yau da kullum baƙaƙen ‘yan ta’adda su kai awon gaba da shi, yau kimanin sati uku kenan”. Sai yanzun ya kai dubansa izuwa gare shi, wasu yamutsattsun riga da wando ne da tsabar koɗau da kuma annakiyar da su ka sha sun fice daga hayyacinsu sun kai intihar da komai ƙwarewarka gurin gano ƙwaƙwaf ba ka isa ka tantance shadda ce ko kuma yadi ba, wuyan rigar ya sha maho da wani irin zare mai kalar haraswa. A ƙafarsa kuma wani suɗaɗɗen silifas ne wanda ya sha faci, amma fa da laida.

Cikin sakannin da ba za su gaza talatin ba ya gama ƙare masa kallo, sannan ya yamutsa fuska haɗi da kautar da kansa wai shi wari ya ce,” malam ba ma maraba da irinka a nan.” Cikin firigici da kuma tarin al’ajab ya ce,” ɗana na ce maka ya ɓata na zo kuma na shigar da rahoto ne.”

“Sai me don ɗanka ya ɓace? Yau ga hauka da naɗe-naɗe wai ɗanwake ya yi arba da tubani, halan mu mu ka sace ɗan naka? Ko kuma so ka ke mu shirya bataliya mu shiga gari yaƙi sabo da an ɗauke ɗanka? Wannan shi a ke kira da shakulatin ɓangaro wai ungulu ta yi arba da mushen mota.

Malam ka yi gaggawar ɓacewa daga nan, ko kuma na buga maka wannan kulkin da ke hannuna.”

Kallonsa ya yi yadda ya ga ya na muzurai tamkar zai yanki babu, ga kuma zabgegen kulki a hannunsa ya na juyawa ya san tabbas idan ya ƙara mintuna biyu a gurin ya na iya buga masa a binda ya haƙƙaƙe kuwa ya bugi banza. Cikin saduda da karayar zuci ya juya ya na faɗin,”girma da arziƙi su ke sanya akayo ɗaukar kaya a ka.”

Zuwa yanzun ya riga da ya gama amincewa ranshi cewar ɗansa fa ya gama salwanta, a shirmen tunaninsa caji ofis shine guri mafi kusa da idan matsala ta taso maka za ka yi gaggawar zuwa domin a kawo maka ƙarshenta cikin gaggawa. Sai dai kash! idan har ba ya ɓace a lissafi ba; wannan ita ce ta biyar da ya halarta a na masa tayin kuɗi. Shin wai kuɗi ya fi ran ɗan ƙasa ne? Wannan wace iriyar ƙasa mu ke ciki? Mu na bautawa ƙasarmu da lokacinmu da jininmu da kuɗaɗenmu amma ita na lokaci ƙalilan ta gaza kare mu. SHIN WAI A INA MATSALAR TA KE NE?

Haka ya cigaba da sagaraftu haɗi da galantoyi a cikin gari, wanda tun daga ranar da Safwan ya ɓace kawo yau iya aikin da ya samarwa kansa kenan. Muddin ya je gida babu shi ko labari mai daɗi a kansa ya san idonsa idon matarsa ba za ta taɓa bari ya kurɓi daɗɗan ruwa ba. Kiran sallar magaribar da akai ne ya tunasar masa da bai ko sallaci azuhr ba, cikin hanzari da sassarfa ya ƙarasa masallacin da ya jiyo kira a zuciyarsa ya na gaggauta neman gafara a gurin mai duka.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 3.7 / 5. Rating: 14

As you found it interesting...

Follow us to see more!

Ina Matsalar Take? 2 >>

15 thoughts on “Ina Matsalar Take? 1”

  1. Ibrahim Adam Dan Sarauta

    Ikon Allah Sai kallo inji masu iya magana.
    Wannan labarin ya tuna abubuwa da yawa da suka faru a rayuwa.

    Ina matsalar ta ke?.

  2. Waw! 😍 ❤💃

    Sannu da kokari yar uwata. Allah ya kara dumbin basira da hazaka, tabbas na ji salo cikin burgewa

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×