Cike da k’osawa da maganar yace “Ki daure ki sanar dani abun da ya faru”
Hawayen dake saman fuskarta ta goge ta cigaba da-cewa,
“Wani mugun Alhaji ne, ya-yiwa ‘yata fyad’e, saboda taje da takardun gama makarantar ta, ya sama mata aiki, shine yace washegari ta dawo bayan ta komane abun ya-faru, kuma ya d’auketa yasa-ta a bayan mota ya jefar da ita a wani wuri, kwananta biyu ba’asan inda take ba, wasu mutane maza biyune suka tsinceta!!..”
“Innalillahi wa’inna illaihir raji’un, yaushe Nigeria ta lalace haka?, abunda ke faruwa acikin tatsuniyoyi shine yake faruwa a zahiri, tayaya kuke tinanin Allah zai kyallemu, mai k’arfi yana dannewa marasa k’arfi ‘yancinsu, neman aiki da ilimin ka-ma yazama bala’i a nigeria. idan namiji ne zai nemi aiki sai ya-biya tarun kud’ade kafin a d’auke shi aiki, idan mace ne dole sai anyi amfani da wani ‘bangare na halittar-ta, kafin a iya d’aukan aiki. Tayaya muke tinanin allah ze barmu haka ba tare da ya jarrabe-mu ba. duk wata annoba da bala’i mune muke janyo-shi dakan-mu.. dole gomnati ta tsaya tsayin daka domin gyaran kura-kuran al’aummar ta..Hamm baiwar allah yanzu me kike so!! ayi kayi?”
“Bani da kud’in da zan iya shari’a dashi, da ina-da karfi da wllh saina-biwa ummita hakkin zuluntar-ta da yayi!,, amma allah ya’isan nan de ita take rabashi da jama’a, nima ita zata rabani dashi!!”
ajiyar zuciya ya sauke, tare da cewa “Allahn da ya’isan nan gaskiya-ne kuma shi yake raba kowa da kowa.. Amma ki kwantar da hankalin-ki ni zan tsaya miki kuma na kwatowa ‘yar ki ‘yancin ta dake kanki da kike tinanin baki da yadda zaki..”
murya a raunane tace, “Kai kuma wanene?.”
“Ni deputy commissioner-nan ‘yan sanda ne, yanzu-yanzu na dawo daga India, nazone domin na gudanar da binciken kisan da aka-yiwa commissioner-nan ‘yan sanda na wannan jihar. sai kuma nazo na tarar da wannan maganar.”
Da sauri intasar ta kalleshi, cike da mamaki, deputy commissioner-nan ‘yan sanda wanda zezo daga india, shakka babu gashi ba’indiye, amma ya-iya hausa haka?. hmm shakka babu yau zan-cika kundina da rahoto, ya kamata na fara tun daga yanzu!!, baki ta bud’e da nufin zatayi magana, sai kuma ta fasa.. kai.. Ina bai kamata nayi magana tun daga yanzu ba, dole nasan waye shi na gano ya mu’amalarsa take da mata. duk acikin ranta tayi wannan maganar
Cikin tsananin takaici ya ciga-ba da magana Abdul malik Ibrahim Ahamad sunana, shekarata sama da goma acan ina aikin gudanar da bincike, wanda yau na dawo na tarar da wannan al’amarin da ya-faru dake!!,
“am I think, this is the first time for me to depend you before the court”
Na rantse da allah mama, wallahi-wallahi billahillazi la’ila ha’illahuwa, na d’auki al-washin ko wanene, sai hukunci ya hukuntashi, bashi da karfin mulki, bashi da karfin kud’i, bashi da abun da zai kare kansa da shi, da yardar allah sai na d’aukarwa yariyar-ki fansa, sai na gurfanar da koma waye a gaban shari’a..
“Yana fad’in haka ya fice daga ward d’in a fusace, bai wani dad’e ba ya dawo, tare da wani doctor, a wannan wurin aka sallamesu, fita sukai tare da likitan yana fad’in zan turo da mota akai ki gida.
“Sai a d’auko ita yarinyar taki a kawota asibiti.
Na gode allah ya-saka da alkairi..
Da amin ya amsa.
Intasar ta biyo bayansa, tana fad’in yalla’bai, plz ka taimaka-mun da contact d’inka!!
“Ba-tare da ya juyoba yace bani da waya.
Haba yalla’bai mutum kamar-ka ace bashi da waya?”
Eh haka tsarina yake!!
“oh god gaskiya wannan tsarin bai-yiba..
Ok toh zaka iya mun lif ka sauk’eni a gida.
A’a bana d’aukan mata acikin motana..
ga wannan ki hau abun hawa!!
batare da ranta yaso hakan ba, cike da-jin haushi’ tace “ka barshi kawai ina da kud’i a wurina!!
Murmushi yayi har saida baiwar dimple d’insa ta bayyana, ban ta’ba yin kyauta ba, an-ce dani a’a ba!!, kuma idan na fitar da abun da ya shafi kud’i bana mayar dashi.
Hannu biyu tasa ta kar’ba tare da cewa, “na gode”
Murfin glass d’in motar ya rufe tare da yiwa motar key ya-tafi.
Bayansa tabi da kalloh, a ranta tana fad’in, wayyo allah, wannan anya kuwa, zan-samu wata makama dangane dashi kuwa?. hmm in kasan wata ai bakasan wata ba. hmm dubeshi kamar wayayye, amma cikin kansa duhune” hmm zaka fad’a tarko-na.
Agogon hannunta ta matsa, murmushi tayi saboda ta tabbatar da komai ya-yi saving akai. hmm saini INTASAR Mahamood Abdullahi, ‘yar jarida mai fikira.
Cike da mamaki take bin sabbin kud’in da ya-bata da kalloh, daloli-ne guda biyar. murmushi tayi tare da zura-su cikin jaka!!
Saida ya-biya ta masallaci, ya gabatar da sallar azahar, kai tsaye katuwar ma’aikatar ‘yan-sanda ya nufa, ma’aikar ‘yan sanda babba wacce aka tsara-ta aka kawata sosai!!,,
Nan-take jami’an tsaron suka kewaye shi..
Cike da girmamawa suka sara masa
Kai ya-jin-jina musu alamar girmamawa
Wani daga cikin ‘yan sandan yace “Barka da zuwa yalla’bai, babban jami’in tsoron bincike”
Murmushi yayi tare da juyawa kai tsaye zai wuce cikin babban office d’in..
“Yalla’bai!! Yalla’bai”
da sauri ta nufo inda yake gadan-gadan, wani babba daga cikin ‘yansandan ya tare ta, da nufin hanata karisawa inda yake!!
Cike da mamaki yace da Police d’in, “Kyalleta ta k’ariso..”
Murmushi tayi har fararan hak’oranta suka bayyana!! cikin jin dad’i tace, “Na gode yalla’bai..Sunana Intasar Mahamood Abdullahi.”
Cike da k’osawa yace,
“Nasani”
“Okay…”
“A-garin ya-ya kika zo nan, waya fad’a miki nan zan-zo” .
“Hmm kana mamaki-ne?.”
“Kwarai”
“Hmm ai tun lokacin da ka baro cikin wannan asibitin na tabbatar da nan zaka, zo!”
Kallo d’aya yayi mata ya kauda kai.
“Rankai dad’e meze hana mushiga daga ciki?”
“a yamutse ya kalleta tare da cewa, “Ba bukatar hakan fad’i abun da zaki fad’a.”
“Hmm gaskiya Yalla’bai, ka burgeni a wancan lokacin, halayyar-ka, d’abiun ka na mutanan kirki ne, shine na buk’aci ka bani contact d’inka, a wancan lokacin.
amma kace baka da waya, Amma nasan kawai k’arya kai-mun…….”
saurin rufe bakinta tayi da tafin hannunta..
Karki zak’e da yawa domin offishin ‘yansanda kike, kar ki kuskuren aikata wani abu ba dai-dai ba, idan ba haka ba aikina zai-fara takan-ki..
Hmm nasani, jami’i, kama mutane a wurin ka ba abu ne, mara sauk’i agare-ka ba.
duk ba wannan ba ga, takaduna nan, sa hannun sanaiya nakeso, tunda ka hanani contact number d’inka.
Cikin rashin fara’a, ya karba ya sanya mata hannu,
Murmushi tayi tare da cewa Abdul malik Ibrahim Ahamad, gaskiya kai jarumi ne acikin hukumar ‘yan-sanda
mika mata yayi tare da cewa, “ba abune mai-kyau ‘yan mata suna zuwa ofishin ‘yan sanda ba.
Yalla’bai gidan-ka fa?..
bana-so mutum yana magana, ba bisa k’a’ida ba, ki kiyaye!!
to shikenan yalla’bai!!
Juyawa yayi ba tare da ya k’ara kallon inda take ba.
Kusa da wani jami’i tazo me sanye da bak’ak’en uniform tace, barka de sir!!
yauwa madam!!
nazo ne domin wancan bak’on jami’in, da alamu yau yazo, gashi kalarsa kalar wayayyu, amma kamar ta ciki dikim ne” wai-shin ko ban had’u bane?.
“Hmm kin hadu’ mana, kefa zazzafar gaske ce?.
Ok na gode, amma ko zaki iya taimaka mun na ke’be dashi?
Dariya kawai yayi tare da cewa, me ze-hana mu ke’be nida ke, ai nima na had’u!!,
Eh tabbas ka had’u amma bakai nake ra’ayi ba. tana fad’in haka ta juya ta fice daga ma’aikatar.
Yalla’bai ance mun kai tsayayyan jami’ine, daga shigowar ka Nigeria, har ta d’au d’umi, gaskiya abun ya burge kowa, daga zuwan-ka ka fara gudanar da aikin-ka yanda ya kamata. gashi ka-fara taimakon al’umma.
Yalla’bai gacan kundin laifun wanda ya buge wannan tsohuwar matar ya gudu..
“Wai yace bada-saninsa hakan ta kasance ba, kuma tsoruta yayi shine ya gudu”
“hmm wato ya fake da jin tsoro ya gudu, hmm to ku sake shi kawai!!
a sake shi kawai..
a sake-shi kuma Yalla’bai?. mun riga da mun-shigar da bayanan karar cikin takaddun laifuka irin nashi.
amma uzurin-sa ba uzuri bane yalla’bai!!!
“Ok hmm to ku yage takardar ka-gane.
wani daga cikin jami’an ne yazo kusa da wannan cikin rad’a yace, hmm ka-gani, ai kace mana tsayayye ne shi?.
Nima-nayi zaton haka..
Wani babban jami’i ne, ya shigo cikin girmamawa yace, yalla’bai wannan kundin yana kunshe da duk wasu bayanai da suka shafi kisan marigayi G.I.G.
“. “Hmm ni an gaya-ma nazo nan ne dan na binciki kisan marigayi G.I.G ne?”, nida nake-so na more lokutana da nishad’i na wasu watanni, “daga zuwa-na zaku wani fara taramun aiki?” ya karisa maganar tare da jefa kundin saman wani k’aton decks d’in dake gaban-shi!!
Kai tsaye wani kayataccen office ya nufa wanda aka ta-nadar dominsa!!
Kallon jami’an dake biye dashi yayi tare da cewa zaku iya tafiya, cikin biyayya ga umarnin-sa suka fice
wani daga cikin-sune ya dakata cike da girmamawa yace yalla’bai sunana Ma’aruf, wannan kuma CUSTOM ne, sunan-shi mrs faruq ahamad cibiyar bincike ne ta had’aka dashi domin yayi maka hidima..
Ok “toh” hakan ya zama sirri na d’an wani lokaci..
Toh yalla’bai..
Wancan kundin da ajiye a waje, kar wani ya motsa-shi koda-da in’ci d’aya ne, amma ina buk’atar duk bayanan dake cikinsa ta cikin na’ura ta..
Cike da girmamawa yace ba komai yalla’bai.
kuma ina-son duka bayanai akan duka jami’an da suke aiki nan. halayen-su, kundin dake bayanan aikin-su, nan da kwana biyu..
Toh yalla’bai!
‘. “Dazu kafin na fito a gida, wani ya kirani, da na duba true caller sunan-shi, sai aka nuna mun sunan-shi Ubaidullah Muhammad Adam!!”
. “d’an gidan minister’n kud’i ne”..
“kana nufin minister na yanzu?”
“Eh yalla’bai d’an-gidan minister n kud’i ne, kuma babban d’an kasuwa ne yana-da babban asibitin kanshi, sannan ya shara da yin oder ta miyagun kwayoyi ana shigo masa dashi ta jiragen sama”..
ajiyar zuciya ya sauke, tare da cewa “Mu’ajiye wannan a gefe!! ka tara-mun dukkan jami’an dake waje yanzun nan.”
“Ok yalla’bai.”
Cikin hanzari ya fice tare da gabatar da abun da aka sanya shi!! bai wuce minti uku zuwa biyar ba ya dawo, tare da fad’in kowa ya kammala.
tare suka jera suka fito, a gaban-su ya tsaya tare da sanya hannusa cikin aljihu. cikin kuzari ya fara magana.
“Wane specter ne a baya ya kula da lamarin kisan mai-girma G.I.G?.”
“Yalla’bai nine!”
wani dogo baki daga cikin-su ya fad’a!!
“. “Wayar-sa da yayi amfani da ita, ta k’arshe meyasa baka d’aukota ba?”
“Ban sameta a wurin da akai kisan bane Yalla’bai Sannan haka nayi tambaya acikin anguwa amma ba’a sameta ba”.
“Ina so na had’u da mataimakin G.I.G ada Muhammad al’hasan, wanda shine yasa ido akan al’amarin”.
. “Yalla’bai, yaje ganin likita Australia bashi da lafiya”
Ma’aruf ne yayi saurin cewa
“A’a Yalla’bai, a kullum idan mun-je kame cikin wani babban club da yake yamma da gari ina ganin-shi a can”..
“a hasale especter’n yace
“Kana da hujjah akan hakane, eyehhh?”.
murmushi Malik d’in yayi tare da takowa kusa dashi yana fad’in,
“Yadai da sauri haka, ya-ka tunzara da wuri haka? nida nazo nan bai-kamata na-nuna cewar ina aiki ba?
ku shirya mana zuwa club gobe, ba sai muje mu gani ba, bawai kuma dan bincike ba, kawai muma zamuje mu shanahhh ne, ko kuka-kace?..”
ya k’arasa maganar yana murmushi”.
“Kowa ya-tafi na sallame-shi Ma’aruf ka-sameni a Office.”
Yana fad’in haka ya juya, cikin kuzari yake taka stairs d’in har ya haura zuwa office d’insa.
dai-dai lokacin ma’aruf ya shigo Office d’in,
“Yalla’bai gani”
“Kawo-mun shayi..”
cikin wasu dak’ik’un mintina ya shigo office d’in rike da plast d’in shayi. acikin d’an karamin mug d’in ya zuba masa ruwan coffee d’in tare da mi’ka masa.
Kar’ba yayi yana fad’in, “Ban yarda da wannan Especter d’in nan naku ba, saboda haka, ina-buk’atar kasa mun idoh akan-shi alamunsa kad’ai sun nuna cewar munafiki ne, tabbas akwai wata a k’asa.. Maganar zuwa club ba gobe zamu-yita ba, yau zamuje a shirya mana patrol amma maganar ta kasance cikin sirri.”
“In-sha Allah!!”
“Sannan wannan takardar dana-ce, daku a yageta, ku mayar da report akan wani case da aka-yiwa yarinya fyad’e. daga-nan zamu shigar da k’arar maganar zuwa kutu..”
. “To yalla’bai.”
“Ni yanzu zan koma gida, zuwa karfe takwas na dare zan shigo!!.”
yana fad’in haka ya d’auki d’an mukullin motarsa ya fice..
Saida ya-biya yayi sallar la’asar kafin ya-koma gida, a falo ya-same su dukkan-su, zama-yi a kujerar da take fessing d’in mami.
Sannu malik, amma gaskiya ban-ji dad’i ba, daga zuwan-ka ko abinci, baka tsaya ka-ci ba. ka wani fice,, ina kaje?.
“Uhmm wllh mami, na biya asibiti ne na duba wata mara lafiya, motace ta bugeta, lokacin da aka d’auko ni daga airport, amma jikin-nata da sauk’i. Wllh mami wannan matan abun tausayi. tana bani labarin halin da suke ciki na tausaya mata.
“Meya-faru da ita?”
Wllh Momy, sun had’u da yaudarar wani alhaji ne, yayi-wa yariyar-ta fyad’e akan taje da takardun neman akin-ta.
“What fyad’e kuma-du yaya?”
“Yeah, but amma nashigar da report zuwa office d’in mu, kuma ina sa-ran zamu turasu kotu”.
Innalillahi wa’inna illaihir raji’un!! Fyad’e, fyad’e, fyad’e, a yau nasamu case d’in fyad’e yafi kashi biyar, na kar’ba wasu amma ban kar’ba wasu ba! Ya malik zuwa gobe zan shirya, ka kaini gidan-su yarinyar, naga ya-take, plz Ya Malik dan allah ka dam’kamun case d’in -nan a hanuna, kuma nayi alkawarin zan tsaya musu agaban shari’a…
Matar Sadiq