Skip to content
Part 18 of 41 in the Series Jini Ya Tsaga by Oum Nass

A hankali rayuwa ta fara garawa, kwanaki na tafiya lokaci na gudu, a haka har Hafsa ta gama iddarta ta fara kasuwancin a gidan Adda Halima, tana saro atamfafo da kayayyaki. Tana bawa ƴan albashi idan wata ya yi su bata kuɗinta.

Kowa yasan wacce Hafsa, tana da kirki wani lokacin, wani lokacin kuma bata da shi, ataƙaice dai za a iya cewa zuma ce ita sai da wuta.

A kuma tsakanin lokacin ta rufe maganar Abdul Mannan da yaranta, koda Adda Halima ta mata magana ko ta kira ta ji lafiyar su, sai ta wurga mata wani kallo.

“Yaran da suke tare da babansu da ahalinsa me zai dame su da har za a damu a kansu?” Idan ta faɗi hakan sai Adda Halima ta girgiza kai kawai duk da ba zata haƙura ba sai ta ƙara mata wata maganar.

“Duk da haka akwai hakkinsu a kanki Hafsa. Ina jiye miki tsoron kada hakkin yaran nan ya tambaye ki, dan na riga da nasan ba zaki taɓa samun miji kamar Abdul Mannan ba.”

“Sai dai idan ba wannan Hafsa ba. Amma ina tabbatar miki zan samu fiye da Sayyadi a rayuwata ta gaba.”

“Koda kin samu ba zaki so shi kamar shi ba.”

Dariya ta yi mai sauti tana girgiza kanta “Har yanzu ban san mene ne so ba. Kuma bana jin akwai namijin da zan so a tsawon rayuwata.”

Girgiza kai kawai Adda Haliman take “Za mu jira lokaci dan ya banbance mana hakan.” Daga haka ta yi shiru tana nazarin rayuwar Hafsa. A gidan bata da matsala da kowa, sai dai idan abin ya motsa bata ragarwa abokanan zamanta, wadda kuma take gasa musu magana take hidima da yaransu. Wadda hakan yasa ta saba da yaran, tana da son yara, tana da barkwanci da surutu.

Ta saba da mutanen unguwar da ƴan garin, wasuma a unguwar Adda Halima bata san su ba, har mamaki duk da ta gama sanin Hafsa. Sai dai mamakinta bai tsaya a haka ba, har sai da taga yadda Hafsa ke kurɗa kurɗan kowanne irin kasuwanci idan ta ga akwai samu. Takan yi Abincin siyarwa, daga kan shinkafa da miya da wake, zuwa tuwon shinkafa da miyar ganye. Sai farfesun kayan ciki.

Har kwangilar biki take na abinci zuwa na kayan maƙulashe. Ita kam ta rasa wani irin zafin nema ne da ita.

“Zama babu juyawar kuɗi kamar zama ne a cikin koma ta mutuwa.” Maganar Hafsa a kullum kenan. Wadda tasa ta haƙura ta ƙyaleta. Har kuma a lokacin bata waiwayi gidan su ba, sai dai jifa jifa tana jin wayar Adda Halima da Alhaji Malam, sai kawun yara idan ya kirata.

Dama-dama takan kaiwa Ummanta ziyara garin Boɗinga inda take aure.

A cikin haka ne ta haɗu da wani Alhaji Mukhtar ma’aikacin gwabnati ne, yana da mata biyu da yara biyar, uwar gidansa ce mai yara uku sai Amarya mai yara biyu.

Bai yi ƙasa a gwuiwa ba ya samu Malam Alhassan mijin Adda Halima da maganar, ya bashi izini ya fara kiran Hafsa.

Ba shine namiji na farko da ya fara cewa yana son Hafsa ba tun bayan gama iddarta, sai dai shine wadda ya yi sa’a har ta saurare shi, ba dan tana son sa ta amince ta aure shi ba, sai dan gajiya da ta yi da zama a gida ɗaya, duk da tana son zuwa Jega. Amma kullum a waya sai sun mata zancen aure, har dai Alhaji Malam yake cewa Malam Alhassan ya dawo da ita nan jega akwai mazan aure idan babu a can.

Jin hakan ba ƙaramin haushi ya bawa Hafsa ba, nan take tace Alhaji Mukhtar ya fito.

Aikuwa bai yi ƙasa a gwuiwa ba ya fito ɗin, suka je har Jega neman aurenta. Tare da Malam Alhassan.

Alhaji Malam yace Malam Alhassan ɗin ya yi wakilcin auren nata ba sai ta dawo nan jega ba.

Ya yi godiya ƙwarai da karamcin da ya samu ba a ɗauki lokaci ba aka ɗaura auren Mukhtar Sulaiman da Hafsat Kamaludden Muhammad.

Auren da take jinsa ta yi shi ne na jeka na yi ba wai dan tana son sa ba, tun farko sai da Adda Halima ta mata magana akan auren da zata yi ɗin.

“Wannan rayuwata ce Adda Halima. Babu wani abu na cancanta da zan tsaya dogon nazari da zaɓa ga maza, domin dukansu abu ɗaya ne, babu na zinaren da za a ɗaga aga sheƙinsa.”

“Kin riga da kin bar farin zinarenki Hafsa. Domin bana jin akwai namijin da zaki samu fiye da Abdul Mannan a tsawon rayuwarki.”

“Na samu Mukhtar Sulaiman. Ya kamata ki sani Hafsat ba kamar ke ba ce Adda Halima. Bana da ra’ayi irin naki, da haƙurin sadaukarwa akan abin da baya ɗaɗa ni da ƙasa.”

“Shima wannan ɗin ba sonsa kike ba Hafsa. Kada ki ɓata masa lokaci ki cutar da rayuwarsa.”

Baki ta taɓe tana murza gashin girarta da hannunta, ba tare da ta yi magana ba.

“Ki daina barin igiyar sheɗan na jujjuyawa zuciyarki, Hafsa. Domin alkhairi ke bibiyar rayuwarki, ki guji gayyato sharrin da ke dilmiyar da wuya.”

“Na gode da kulawa.” Ta faɗa maganar tana jinginar da kanta da lumshe idanuwanta.

Bayan kwana biyu Malam Alhassan ya kirata ya mata nasiha daga nan ya umarceta da ta shirya yau za a kaita gidan mijinta, dan bai da ra’ayin zaman mace a gida bayan an ɗaura aurenta.

A daren Adda Halima da abokanan zamanta suka raka Hafsa, bayan sun zaga da ita wajen matayensu da damƙa amanar Hafsa a hannunsu.

Suka tafi suka barta da mata fatan alkhairi.

Zan iya cewa zaman Hafsa a gidan Mukhtar zamane da za a ce babu yabo babu fallasa, domin da fari kam ta kwantar da kai ƙwarai, ta shimfiɗa kyakkyawar soyayya a zuciyar mijinta, wadda yake ji a duk duniya babu wadda ya kai shi dace da mata. Ga girki kala kala da take masa wadda duk ranar girkinta, yaran gidan ma sun fi ɗoki.

Matansa da suke ji kamar za su kasheta da kinshi, da baƙin ciki, suka shiga yada mata magana a son ransu.

Bata kulasu domin hankalinta ba kansu ya ke ba a yanzu, sai dai takan ja yaransu a jiki ta musu alherai da ɗinki, domin ko da aka yi auren nata ta ci gaba da sana’arta ta kayayyaki da kuma yin kwangilar abincin biki. Saɓanin su da suke zaune ba siyar da komai.

Ganin yadda take jan yaransu a jiki da musu alkhairi yasa suka zubar da makamansu, musamman da suka ga duk yadda suke mata abu bata fasa yiwa yaransu magana da kuma yi musu alheri, baka idan ƴan uwansu suka zo kamar zata goya su dan daɗi da musu tarba ta alkhairi, wani lokacin sai dai suji kiran iyayensu akan alkhairin da Hafsa ta aiko musu.

Wannan yasa suka rage mata habaici da kuma takalarta faɗa duk da cewa bashi ne maƙasudin dakatarwar tasu ba, illa mayar musu da martanin da ta yi da kuma nuna musu hannu.

“Kune kuka ɗauki namiji wani tsiya da kuma abin ado, amma ina tabbatar muku da cewar ni bani da hauka da jahilci na ɗaukan miji komai a rayuwata, da har zan tsaya ina faɗa da mace ƴar uwata a kansa. Idan kun kwantar da hankalinku ba zama ne ya kawo ni ba, idan kuma kuka tashi hankalinku to ni ko guguwa ta sara min.”

Haukace musu ta yi wadda yasa su yin tsamo tsamo kamar tsimman da aka jiƙa.

Sai da ta shekara ɗaya a gidan zuwa lokacin kowa ya santa, ƴan unguwa da jama’ar gidan, dangin Mukhtar na sonta ƙwarai da ƙaunarta, musamman da ta kasance mace mai alkhairi duk wadda ya zo baya tafiya hannu rabbana sai ta bashi wani abin alkhairi ya tafi da shi.

A lokacin kuma ta fara laulayi ta samu juna biyu, bayan lokaci ta haifi yarinyarta mace kyakkyawa da ita. Aka mai kamar babanta, ta ɗauko hasken mahaifiyarta.

Murna a wajen Mukhtar ba a magana, da ƴan uwansa, wa yarinya sunan Mahaifiyarsa, ake ce mata Bunayya.

Bayan nan sai da ta ɗauki shekara biyu ta ƙara haihuwa ƴa mace wadda ya sa mata sunan Adda Halima, hakan yasa ake kiranta da Ummi.

Haihuwar Ummi da wata uku Mukhtar ya yi mummunan hatsarin mota a hanyarsa ta dawowa daga waje aiki.

Mutuwarsa ta girgiza Hafsa ƙwarai, duk da bata sonsa tana gaf da barin gidansa, amma sai mutuwarsa ta zame mata kamar fasuwar ƙwai. Ta yi kuka, kuka mai yawa, na tausayin yaranta da kuma abokanan zamanta, musamman ƴan uwansa da ya kasance shine komai na su, shine kuma ke ɗaukan duk wani ɗawainiyar rayuwarsu. 

Daga jega ƴan uwanta suka zo, sun koka da jajanta al’amarin da ya faru da Mukhtar mutumin kirki.

Bayan gama takabarsu ne ta dawo gida da zama bayan ta ajiye kayanta a gidan Adda Halima. Bata daɗe a can ba ta dawo sokoto dan ba zata iya zama a jega ba. 

A lokacin ne kuma ta sake auren wani miji mai suna Adam, yana da mata ɗaya da yaransa biyu, itama taje da nata yaran, zamansu bai wani ɗore ba, domin shi yaron ne mai rawar kai, da kuma nuna ware ware akan yaransa, haka yasa Hafsa ta nuna masa kalarta, wadda ta zame masa wuta shi da yaransa.

Ƙarshe dai suka rabu babu abin arziƙi. wata biyar ta yi a gidan a daddafe bayan ta gama gana musu izaya shi da matarsa da yaransa.

A lokacin ne kuma Mijin Adda Halima ya kamu da rashin lafiya, wadda dama yana fama da ciwon sugar sai ya kwantar da shi.

Haka suka shiga jelan asibiti dai mako biyu ya yi Allah ya karɓi rayuwarsa.

Wannan mutuwar tafi kowacce mutuwa dukan Hafsa, ta girgiza dangi da ahalinsu Hafsa.

Bayan an yi bakwai ɗinsa Alhaji Malam ya tisa Hafsa gaba suka koma jega.

To a nan ne ta ci gaba da zubawa matansa rashin kirki kala-kala har dai  shima bata ƙyale ba, wadda ta tara masa mutanen unguwa tana cewa zata yi ƙaransa dan baya adalci.

Wadda hakan yasa ta dawo gidan Adda Halima da zama, bayan an raba musu gadon su ta siyi gida sun koma ita da yaranta….

BACK TO STORY

<< Jini Ya Tsaga 17Jini Ya Tsaga 19 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×