Skip to content
Part 5 of 41 in the Series Jini Ya Tsaga by Oum Nass

“Dama duk wanda ya sayi rariya yasan zata zubar masa da ruwa. Ni kaina nasan ba zaka iya siyan abu mafi girma ba sai ka tsaya kana zaɓen ƙarami dan kace abu ƙarami shine mai lada.

Kamar dai yanda kullum kuke cika mutane da wa’azinku.” Ta ƙarasa maganar tana yankar cinyar kaza a bakinta.

Ƙarasawa yayi kusa da ita, fuskarsa ɗauke da murmushi ya zauna  a kusa da ita, yana harɗe ƙafafuwansa, da kuma ɗaukan kofin lemon da ke gabanta, ya kurɓa.

“A tarihin rayuwata ban taɓa jin labarin Amarya ya zauna tana cin kazar aurenta ba kamar ke.

Koda ace ta ci ɗinma tana cine ta sigar lallashinta da kuma yi mata magiya, amma sai gashi ke ba’a miki tayiba ma kin hau cinta.” Abdul-Mannan ya faɗa yana murmushi.

Ɗago da kanta Hafsat tayi tana murmushi itama “Shi yasa kenan ka siyo kaji ƙanana dan kana da labarin amare basa cin kajin aurensu?”

Kansa ya girgiza har a lokacin murmushi na kwance akan fuskarta “Na siya ne dai-dai da aljihuna.”

“Uhm Sheakh Abdul-Mannan amma duk labarin da ka samu na ƙin cin kazar amarya, hakan baya hana asha romonta koda ace bata ci daga abun da aka sunnanta ma angonta bata  shi ba.”

Idonsa ya waro yana kallon Hafsan da itama shi take kallo fuskarta ɗauke da murmushi.

“Hafsat wai bakya jin kunyata da nauyin faɗar ko wata magana a gabana?”

“Idan naji kunyarka da wa zan yi magana? Bayan a yanzu duniya ta sheda mun zama abu ɗaya ni da kai.

Komi nawa daban yake Abdul-Mannan, ban yarda na yi rayuwar gidadanci da aron halayyar da ba tawa ba.”

“Kina so ki ce min wanan shine zahirinki?”
Kai ta gyaɗa masa tana lumshe ƙanannun idanuwanta “Komi da ka ga a tare da ni nawa ne! Kana so kace min ba’a baka labarin ko wace ni ba ka yarda ka aure ni?” Ta ƙarasa magana tana tauna ƙashin haƙarƙarin kazarta, wanda ta cinye ta tas.

“Yaushe rabonki da ki ci kaza?” Ya tambayeta yana murmushi da ƙoƙarin sauya hirar tasu. 
  “Daƙiƙa ɗaya da ta wuce.” Ta faɗa tana dariya.

“INa nufun kafin yau.”

“Da yake dai gidanmu na malamai ne kullum akanyi ƙoƙarin maida baƙin yawu. Amma ban saniba ko almajiri na samun damar ci kullum kamar yanda malaminsa ke ci.”

Ta faɗa tana goge bakinta da tushu ɗin da ke kan table ɗin gabanta, sanan ta ɗauki ruwan lemo ta sha.

“Nagode da ka sunnanta abun da aka sanar da ku. Saura kuma ka tambaye ni akan abun da ya shafi addinina.”

Bai kalleta ba ya janyo sauran kazar da ta rage masa, wuya ne sai kuma makafakin kazar da ta barshi, amma duk ta cinye kazar har guda biyu.

Kallon Hafsat ɗin ya sake yi da mamaki wanda ita bata san me yake ba, dan ta naɗe akan kujerar da ke palon nasu.

Ruwan lemon ya kurɓa sanan ya tattare naman ya shigar da shi kitchen ɗinsu.

Har ya dawo tana zaune bata motsa ba “Ki je kiyi alwala za muyi sallah.”

“Ina da alwalata.”

Tsayawa yayi ya kalleta “Duk tauna kajin da kika yi da sakin layin da kika yi amma kice min kina da alwala?”

Tashi tayi ta shige ɗakinta ba tare da tayi masa magana ba, shima nasa ɗakin ya shiga sanan ya girgiza kansa, al’amarin Hafsa sai ita. Amma kuma duk abun da tayi bai ji ransa ya ɓaci ba, asalima ji yayi wata sabuwar ƙaunarta na shigarsa, dan ya fahimci harda ƙuruciya ce ta ke damunta.

Bayan ya shiga ɗakinsa ya cire kayansa ya shiga wanka, daga nan ta ɗauro alolarsa, ya saka doguwar zaleka fara ƙal a jikinsa, bayan ya shafe ko ina na jikinsa da mai da kuma turare. Abdul-Mannan mutum ne ma’abocin ƙamshi da son turare, baya sake da ƙamshi da tsaftar jikinsa.

Cikin nutsuwa ya futo ya nufi ɗakin da Hafsat ɗin take anan ya sameta ta futo daga wanka itama, tana sanye da ɗan ƙaramin tawul a jikinta, wanda iyakarsa gwuiwarta, santala-santalar cinyoyinta sun futo farare da su.

“Ya Rabb!” Ya faɗa lokacin da yaji wani abu ya tsirge masa tun daga tsakiyar kansa har zuwa yatsan ƙafarsa.

“Wai dama haka malaman suke su shigowa mutane ɗaki babu sallama?” Ta faɗa tana harararsa da murguɗa bakinta, yayin da ta ja dogon hijabinta ta zurma a jikinta.

“Idan kinsa kayanki ki zo ɗakina ina jiranki.” Ya faɗa yana fucewa a ɗakin.

Baki ta taɓe ta ɗauko wata doguwar riga marar nauyi ta sa a jikinta, bayan ta shafa manta mai ƙamshin daɗi, kaɗan ta fesa wani turare da Adda Halima ta bata shi. 

“Ni a duniya ina mamakin wanan tsarabe-tsaraben da su Adda Halima suka sani. Komi ace ayi idan miji ya kiraka, kada ka tafi babu ƙamshi.

Wallahi da ace banda wani shiri akansa da babu wanda ya isa ya sani na tsaya ina ɓatawa kaima lokaci. Kana ganinsa da shanyayyun idonsa ya iya shigowa ɗakin mace babu sallama.” Ita kaɗai take magana kamar zata tashi ɗakin saboda masifa ta fice ta shiga ɗakin nasa.

Sanda taje ɗakin har ya shimfiɗa musu sallaya hakan yasa ta hau ba tare da ta masa magana ba.

Shima bai tanka mata ba, dan har a lokacin yana jin jikinsa babu laka.

Raka’a biyu ya jasu daga nana ya shiga karanto musu Addu’a tana kiran Ameen. Yanda yake zazzago larabci abun sai ya ɗan birgeta kaɗan, duk da ta san ko waye mijin nata. Shafawa yayi itama ta shafa, kamar gaske.

Daga nan ya juyo ya ɗora hannun damansa akanta ya shiga yin wata sabuwar addu’ar, jikinta ne taji yayi sanyi tana jin ko wata ƙofar gashi na jikinta na buɗe, wani sabon tsoro na ratsa zuciyarta.

Tsoron abun da bata san ko na miye ba, ga kuma sanyin da ko wata laka ta jikinta yayi.

Sai da ya gama sanaan ya shiga tambayarta akan abun da ya shafi addininta tun daga sallah da kuma karatunta.

Yasha mamaki da yaki ko mi ya tambayeta ta sani, duk da cewa yasan waye mahaifinta, ya kuma san tsayuwarsa akan addininsa da ma rayuwar yaransa.Ajiyar zuciya ya sauƙe “Alhamdulillah! Madallah da samun mace ta gari.” Ya faɗa yana ɗaukarta a hannunsa kamar wata jaririya wanda yasa Hafsat buɗe idanuwanta tana kallonsa.

Idonsa ya kanne mata guda ɗaya “Amaren da basu ci kazaba ma ana shan romonsa. Ya kikaga amaryar da ta ci kaza har ta tauna ƙashinta?”

Baki ta buɗe da niyar magana sai dai hakan ya gagara domin tuni ya shigar da bakinsa cikin nata, ya kuma kashe musu futlar da ta haska ɗakin.

*****

Ta daɗe tana jin labarin maza da ƙumajinsu, amma bata yarda cewa  kamar Abdul-mannan zai iya sa ƙarfi ya keta ta ba, kamar yanda sauran mata ke bada labari.

Ta yi takaicin zamo warta a matsayin jinsi mai rauni da ta kasa hana Abdul-Mannan kaiwa ga buƙatarsa ba, ta yi kuka ya fi sau a ƙirga, ta wanke jikinta da dirza shi da sabulu kamar zata sauya fatar jikinta.

Sai dai bata daina jin zafin da ke ratsa jikinta ya sauƙaƙa ba. “Tabbas da sa ke.” Ta faɗa tana share hawayen kan fuskarta.

“Ya yi kusa ace na fara zubar da hawaye na akan ɗan wannan al’amarin.”  Ta faɗa a karo na biyu a lokacin da take zubawa kanta ruwa.

Ta futo daga toilet ɗin daga ita sai ɗan guntun tawul a jikinta, a lokacin shi Abdul-Mannan yaana tsaye akan abun sallah yana gabatar da sallar dare.

“A haka kamar waliyi.” Ta faɗa tana wuce shi da raɓawa ta bayansa.

Ɗakinta ta shige ta saka doguwar rigar barci, sannan ta bi lafiyar gado, har a lokacin zuciyarta bata daina tafasa da abun da Abdul-Mannan ya mata ba.

“Ashe dai mazan haka su ke a riga.” Ta faɗa tana tuno kalar azabar da ta sha. 

“Ni kuwa idan ban gasawa Wannan mutumi aya a hannuba me na yi kenann a duniyar?” Ta sake faɗa  tana ƙwafa anan barci ya ɗauketa tana saƙa da ƙullu na mugun zare.

Asubar fari ta ji Abdul-Mannan na tashinta, yana buga fulon da take kwance a kai “Hafsat! Hafsat ta shi kinji asuba ta kawo kai.” Ya faɗa yana sake bibbiga fulon nata.

“Haba mana Abdul! Duk kalar azabar da ka min a daren nan bai ishe ka ba sai ka zo ka tashe ni ka hanani barci.”

“Lokacin sallah ne ya yi, ki tashi ki yi ni zan tafi masallaci.”

“Oh to ni sai ajima zanyi, dan har yanzu ƙasusuwana ba su dawo daga raguza sun da ka yi ba.

Shine dan kinibibi ka sha rawani a kai kamar ba abun da ka iya.” Ta faɗa tana yamutsa fuskarta da jan bargo tana lulluɓai kanta.

“Ni ne na ke Kinibibin Hafsa?”

“Akwai wani mai rawanin ne bayan kai. Ni ka tafi ka hananin barcin wahalar da nake.” Ta faɗa juya masa baya.

Kai ya girgiza ya fuce a ɗakin a zuciyarsa yana mata Addu’ar neman shiriya.

Har yaje masallaci ya dawo tana kwance, lokacin gari ya fara haske domin sai da ya tsaya ya yi wa’azi sannan ya dawo.

Da mamakinsa bai ji motsinta ba, hakan ya sa ya shiga ɗakin nata  ya sameta har a lokaci tana duƙunƙune a cikin bargon.

Bai ce mata komi ba ya ajiye rawaninsa a gefe, sannan ya cire jallabiyar da ke jikinsa, ya rage daga shi sai wando iya gwuiwa da kuma shimi.

bargon ya janye a hankali sannan ya cicciɓeta ya ɗauke ta shigar da ita toilet, ya sa ta a cikin ruwan da ke ƙaton baho.

A furgice ta buɗe idanuwanta tan  kiran “Wayyo Allah!” Ganin Abdul-Mannan a gabanta ya harɗe hamnu a ƙirji yana dariya yasa ranta ya ƙara ɓaci.

“Abdul kashe ni kuma kake son yi bayan notunan da ka gama kunce min a daren jiya?”

Kai ya girgiza “Lokacin sallah ya wuce Hafsat. Zan iya jure komi a wajenki amma banda sakaci akan ibada.”

“Aikuwa da sake an bawa mai rago ƙafa. Abdul ka shirya rigima da ni kenan?”
Kafaɗarsa ya ɗage “Na shirya dai zaman aure da ke Hafsat, cikin daɗi da rashinsa, domin ina sonki sosai.” Ya faɗa daga haka ya juya ya barta a banɗakin.

Kitchen ya wuce kai tsaye ya fara musu abin kari, duk da shi ba wai gwani ba ne wajen girki amma dan ya birge Hafsa ya fara kokawar fere dankalin turawa, garin ferewa ya yanke hannunsa da sabuwar wuƙa, ya fara yarfe hannunsa saboda azabar da ya ji.

Amma duk  da haka bai haƙura ba, ya wanke jinin ya ɗauko bandeji ya rufe ciwon, wajen suya ma mai ya yi ta ƙona shi, amma sai da ya gama, a suyar ƙwai kuma ya ɓata lokaci, dan bai san me ake sawa a soya ba, ganin dai yaana ɓata lokaci ga bai ji motsin gimbiyar tasa ba kawai sai ya soya shi haka.
Ya kashe gas ɗin bayan ya tafasa musu ruwan  sai fara’a yake, a ransa yasan yau ya na da ladan sanya matarsa cikin farin ciki. Zai kuma mata ba zata.

Ɗakinta ya shiga ya ganta ta ci uwar kwalliya cikin atamfa riga da siket, ɗinkin ya bi jikinta ya sake futo da kyanta ƙwarai, kasancewarta mace  kyakkyawa mai diri.

“Masha Allah, kin yi kyau sosai Uwargidana.” Ya faɗa yana ƙarasawa kusa da ita.

Fari ta yi da idanuwanta tana yawata shi, sannna ta kalle shi “Na daɗe da sanin ni kyakkyawace Abdul.”

Kansa ya gyaɗa kamar dolo “Kayan sun miki kyau.” Ya sake faɗa a karo na biyu.

Hannunta ɗaya ta ɗaga ta fara girgiza yatsanta manuni “A’a ba kayan ne suka min kyau ba Abdul, ni ɗin ce dai na musu kyau.”

Ta faɗa tana takawa cikin salo da yanga, duk jikinta na jujjuyawa, sannan ta ɗaga hannunta tana nuna jikina “Ko makaho ya laluma ni yasan kaya su ke buƙatar irin jikina Abdul Mannan.”

Kansa ya gyaɗa yana tasbihi da shu’umancin Hafsat.

“Masha Allahu la ƙuwwata illa billahi. Ko da muna da kyau ance mu suturce jikinmu. Duk kuma gadararmu akan kyau ɗin ba za mu yi yawo tsirara ba.

Kinga kenan mu ke buƙatar kayan ba shi ke buƙatarmu ba.” Ya yi maganar da murmushi akan fuskarsa.

“Shima zai buƙa ce mu Abdul.”
“Zo mu je ki ci abinci, sai mu yi magana akan hakan.” Ya ruƙo hannunta suka futo har zuwa gaban daining fuskarsa ɗauke da fara’a ya ja mata kujera ta zauna.

Sannan ya fara zuba mata abincin, tana ganin abinci ta fara jin cikinta na hautsinewa.

“Wannan me ye AbdulMannan?”
“Soyayyan dankali ne.” ya faɗa yana ɗaga shi.”

“Turƙashi wannan ai sai dai a kira shi da baƙin gawayi…” Ta faɗa tana rufe bakinta saboda ƙarnin da ƙwan da ya cika mata hanci.

“Wannan ƙwan ruwa ne ko na sarari  ya addabe ni da ƙarni? Kai Abdul ba zaka kashe ni da wannan cimar ba.” Ta faɗa tana tashi ya bita da kallo.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Jini Ya Tsaga 4Jini Ya Tsaga 6 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×