Skip to content
Part 14 of 26 in the Series Kauthar by Jeeddah

Da safe kin yarda su hadu tayi, duk da cewa jikin nata ya warware amma sai ta tura mishi da sakon cewa ba zata je wajen aiki ba saboda bata jin dadi.
Tana jin motsinshi lokacin daya fita yin kari, har ya kammala ya sa kai ya fita ba tare daya nemeta ba. Taji ranta ya dan sosu, ko babu komi dai ai ya cancanci ace ya lekata ya ga yadda ta kwana.

Tana nan zaune tana wannan mitar a ranta sai ga sakonshi.,

“kina da tabbacin ba zaki ba shawarata ta jiya ba a go? Sai in ga kamar shawarace mai kyau ai na baki ko?”

Ta kada idanu, wai ita za a yiwa wayo ita da ba karamar yarinya ba. Ta maida mishi da sakon,

“A’ah, nagode.”

Ya maidata mata da,

“Amma dai kin san duk wayon amarya sai an sha manta ko?”

Ganin da tayi neman magana ne kawai yake yi da ita yasa ta kyaleshi bata mayar mishi da amsa ba.

Ba a jima ba ya kara tura mata wani sakon da kalaman daya kunsa yasa taji kamar kasa ta tsage ta nutse ciki, ta kashe wayar tayi jifa da ita gefe zuciyarta na bugawa. Watarana dai idan ba sa’a ba sai AbdulMalik yasa zuciyarta tayi bugawar da ba zata kara harbawa ba.

Zuwa can bayan ta kammala duk abinda zata yi, ta kira daya daga cikin yan ofis dinsu ya tura mata ayyukan da zata yi, ta zauna anan gida tana yi.

Sai washegari sannan ta koma wajen aiki.

Mugun tsarewa take yi, ta ki ba AbdulMalik wata fuska da zai gani ya kai mata maganar kawai. Shima ganin yadda take tsarewa ne yasa bai kara nemanta da wata magana ba.

Ta riga ta gama kudirin a karshen satin zata je Abuja, tana da tabbacin Anty Aisha ta dawo saboda hutunsu Lukman ya kare, kuma idan ta kira layinta na kasar waje baya shiga.

Don haka ranar Alhamis take fada mishi tana so taje gida karshen sati. Yayi shiru yana kallonta a nutse. Lokacin suna zaune akan dinning suna cin abinci.

Kai ya gyada, yace, “ok, Allah Ya kaimu. Zanyi kokari a samar miki tikitin safe. Nima da ba don ayyukan da nake dasu ba, ai da mun je mun gaida Annah har ni.”

Bata taba zaton zai barta kai tsaye ba, musamman ganin cewa basu rufa watanni uku da yin aure ba. Da har ta gama shirya irin ta’asar rashin kirkin da zata mishi, amma sai ya sagar mata da gwiwa, ta kasa cewa komi.

Ya tsaya yana kallonta cikin alamun tambaya, da kyar ta iya kakaro yawun bakinta ta furta mishi “na gode”

Ganin alamun tana cikin wani yanayi shi yasa bai sake ce mata wani abu ba.

Zuwa washegari kuwa har ta gama shirin duk da zata yi. Ta hada jaka guda shake da kayan makulashe da tande-tande data tanadarwa su Mahmoud. Hai-hai take gari ya waye ta sa kai tayi gaba.

To kuma sai a yammacin ranar suka yi bakin da basu zata ba.

Da wuri ta koma gida ranar. Bayan an fito daga masallaci, abinci ta ci, ta koma daki ta kwanta. Cikin ikon Allah sai barci yayi awon gaba da ita.

Wajen karfe uku aka je mata da sakon cewa tayi baki. Tayi jimm a ranta tana tunanin wasu bakine haka? Ta dai ce a kaisu falo a basu abin sha tana zuwa.

Tashi tayi tana mika da layi cikin gajiya, bandaki ta fara shiga ta wanke fuskarta kafin ta fita.

Tun kafin ta karasa falon take jin hayaniya da maganganu kasa-kasa. Sai ta tsaya cak tana cire aids dinta daga kunne tana kara gyarawa, wai don kada aje su suke mata karya tana jin ba daidai ba.

Bata san sanda ta kwasa da gudu ta karasa cikin falon ba.

Ta ci karo da Mahmoud da Lukman suna yan wasanni a kasan carpet, yayinda Anty Aisha take zaune akan kujera, ta dora kafarta daya akan daya cikin basarwa da ginshira, wani abu game da ita da yake matukar cin ran Kauthar. Amma a wannan rana dai, sai ta nemeshi ta rasa.

Tayi wur-wur a tsakaninsu, ta ma rasa wane bangare zata nufa.
Lukman yana daga ido yayi tozali da ita, sai ya kwala ihun murna ya zabura ya nufeta. Itama sunan nasu take kira cikin tsananin zumudi da murna. Sai dai bata san yadda aka yi ba sai taji ta tsinceta durkushe, a jikin Anty Aisha, su Mahmoud kuma sun mata rumfa.

Wani abu mai kama da sanyi da natsuwa suka fara ratsata, sai taji idanunta na ambaliyar ruwan hawaye.

Allah kadai Yasan iyaka lokacin da suka dauka a haka, kafin ta daga kanta daga jikin Anty Aishar, ta kamo hannuwan yaran suka baje anan gabanta. Ta kasa ko sakin hannunsu ne balle su matsa daga inda take.

Ta daga kai a kunyace tana kallonta, haka kawai take ji kunyar matar ta lullubeta.
Tace, “Anty sannu da zuwa, ya hanya?”

Kallo take kare mata a nutse tana ganin irin canjin data samu cikin yan watannin. Akwai wata natsuwa da girma a tattare da ita wadanda babu a lokacin data bar gida.

Kodayake, dama dai an ce aure yana canza mutum, kuma ta yarda da hakan.

Tace, “lafiya kalau Kauthar. Kin ganmu babu sanarwa ko?”

Ta girgiza kai a hankali, “ai nima goben da nake so inje, har na kammala shirina tuni”

Anty Aisha ta daga baki cikin mamaki, sai kuma tayi murmushi. Tace, “nagode Allah da bamu yi sabani ba, tunda muma da sai goben zamu taho amma su Lukman suka dameni.”

Murmushi tayi a sanyaye kafin ta tashi da kanta ta shiga kicin. Nan da nan ta cika musu gabansu da kayan marmari dana tande-tande. Ta kuma ba kuku kalar abincin da take so a dafa wanda tasan Anty Aisha din tana so. Ta koma inda ta tashi kusa dasu Lukman ta zauna.

A lokacin ranta fes yake da farinciki wanda ta kasa boyewa. Duk rashin son hayanitarta, sai gata suna hirarsu har da shewa da tafi, gabadaya sun karade falon da hayaniya.
A haka suka tsinci muryar AbdulMalik a kansu. Ta juya da sauran murmushi akan fuskarta tana amsa mishi sallamar.

Ya jima da shigowa, kawai tsayawa yayi daga bakin kofa yana kallonta cikin mamaki. Rabon daya ganta cikin irin wannan farinciki da annashuwa har ya manta. Yaushe rabon data kalleshi fuska da murmushi da fara’a irin wannan? Rasuwar Fahima kamar wata annoba ce data tattare gabadaya wani farinciki da walwalar Kauthar ne ta tafi dasu gabadaya. Amma watakila har yanzu akwai sauran wannan hali nata, carefree, free spirit, wanda a take yayi alkawarin sake dawo mata dasu duk ma inda suka shiga.

Ya karasa har gaban Anty Aisha ya durkusa yana gaisheta cike da alamun sarakunta. Ta amsa cikin fara’a tana tambayarshi ya aiki. Mamaki ya kusa dankarar da ita a zaune lokacin da taji cewa shi da kanshi ne yaje airport ya daukosu. Ta manna mishi harara a sace, shi kuwa ya bita da murmushi.

So yayi ya basu waje ya tafi, amma Anty Aisha ta hana. Dole ya zauna cikinsu suna hira. Da yake su Lukman basu da matsala kuma wayayyun yara ne, babu alamun bakunta a tattare dasu. Haka suka saki jiki, sai gashi cikin kankanin lokaci ana ta raha da hirar ban dariya abin gwanin ban sha’awa.

A zaune take dangargar a kan kafet, ta mayar da kanta baya ya jingina da kujerar da Anty Aisha take kai a zaune, kiris ya rage ta dora kanta akan cinyarta. Kusanci makamancin haka bai taba hadasu da ita ba. Amma a wannan lokacin, sai taji wani kawa zuci yana ratsata, ta samu kanta da furta ina ma, ina ma ace… a cikin zuciyarta.

Sai da aka kira sallah sannan hirar ta tashi. AbdulMalik ya dauki yaran suka tafi masallaci, ita kuma da Anty Aisha suka yi tasu sallar anan.

Bayan Isha’i duk suka hadu wajen cin abinci, aka zuba musu sakwara da miyar ganye, ga farfesun kayan ciki, sai lemun kwakwa da abarba da aka hada.

Ta sake sosai da sosai cikin yaran, abinci taci sosai wanda ta jima rabon da ta ci kamar shi.

Ana gama kwashe kaya Anty Aisha ta nemi da zasu tafi masauki ita da su Lukman, in yaso da safe sai su dawo. Ta kuwa ce da wa Allah Ya hadasu idan ba da ita ba? Fir ta ki yarda. Tace sai dai ko su zauna anan, ko kuma ta bisu. Rigima dai har sai da AbdulMalik ya shiga ciki sannan ta lafa. Shi ya samu ya shawo kan Anty Aisha ta yarda zata kwana a wajen da aka tanada don baki.

Bayan an kaisu, an kai musu duk wani abun bukata tun daga kayan barci dana wanka da danginsu. Kauthar ta koma dakinta itama ta watsa ruwa ta rage kayan jikinta.

Marasa nauyi na sanya na barci. Ta sake yiwa dakinsu Anty Aisha tsinke.

Daban aka ware mata nata, su Lukman kuma suna daya dakin na kusa da nata. Haka suka sake haduwa suna ta hira har dare ya raba.

Anty Aishar na zaune akan kujerar mirror tana gudanar da ayyukanta ta cikin waya, bata cika sanya musu baki ba sai jifa-jifa.

Sai data ga dare yana neman rabawa sannan ta kora yaran suka tafi.

Ta kurawa Kauthar idanu a tsanaki, wadda ta ma kara mike kafa a inda take, bata da alamun motsawa gaba balle baya.

Tace mata, “dare yayi Kauthar, yakamata ki tashi ki tafi haka nan kema, kada mijinki ya dinga nemanki.”

Ta daga kai a hankali tana kallonta, “Anty Aisha, a yau dai kam, babu wani barci da zan iya yi idan har ban ji ko ni din wacece a gareku ba ke da Daddy. Daga ni har ke kuma mun san cewa kina ja min rai ne a bisa wani dalili naki, wanda ban san ko menene ba!”

Shiru tayi cikin nazari tana kallonta kafin ta nisa, tace, “ba ja miki rai nake yi ba Kauthar, wannan sensitive abu ne da kamar yadda na fada miki, ba zai fadu ta waya ba. Shi yasa nayi takanas nazo. Amma yanzu dole mu barwa safiya tunda dare ya riga yayi. Da wani idanu kike zaton mijinki zai kalleni idan na rike mishi mata a bisa son raina? A uwar banza?”

Cike da zakuwa ta daga baki tace, “ai ba ma zai sani ba, tunda ba daki daya muke kwana dashi ba. Yana dakinshi nasan ma yayi barci tuni!”

Sai data gama maganar ta fahimci baram-baramar da tayi, Anty Aisha ta kai hannu ta rufe bakinta cike da tsananin mamaki, sai tayi kus kamar wadda ruwa ya cinye, ta lafe a gefe guda tana raba idanu.

Tsabar mamaki yasa Anty Aisha ta kusa minti bata iya magana ba, sai daga baya ta hau tafa hannuwa, tace, “hukumullahi laa ajabun fihi! Yanzu dama Kauthar abinda yake faruwa kenan? Dama abinda kike kitsawa kenan? Wata da watanni, hankulanmu sun kwanta muna ganin kin hakura da komi kin fauwalawa Allah lamuranki ashe ke ba haka bane a gareki? Kina so ne kice baki dauki umarnin Daddynki a bakin komi ba face maganar hotiho hayakin wuta?! Tunda dai dama ni ba wani tasiri gareni a wajenki ba!!”

Ranta ya baci kwarai, irin bacin ran data jima bata ga kwatankwacinshi a tattare da ita ba. Sai ta sadda kanta kasa, wata irin kwalla ta cika mata idanu, duk yadda taso akan ta danne sai ta kasa lokacin data sake hada idanu da Anty Aishar da take kallonta a fusace, murya na rawa da bari a can kasan makoshi, tace, “mijin Anty Ummy ne fa!!”

Sai ta dargwaje da kukan data dade tana son yi. Abin nema yake yafi karfinta, har ta rasa da wanne zata ji.

Amma maimakon amsar tata ta taushi zuciyar Anty Aisha, sai ma kara tunzurata da tayi.
Cikin daga murya tace, “to sai aka yi yaya? Iye? Wahayi ne aka miki da kin auren mijin nata? Ko kuma aya zaki bani da hadisi da suka haramta hakan? Ashe ma ke baki da tunani Kauthar? Ya ina yabonki sallah kuma alwala zata gagareki? Me yasa kika cika son kanki ne Kauthar? Kina so kiyi wasa da damar da Allah Ya baki, wai don kawai kina auran mijin Fahima? Abune da yake rubutacce, wanda koda tana raye ko bata raye sai anyi shi matukar Allah Ya kaddara hakan! Kenan lokacin ja zaki yi da hukuncin Allah?!”

Kukanta ta cigaba da yi cikin kunar rai ba tare data dakata ba.

Itama sai ta tsagaita da nata fadan, ta zauna tana kallonta tana sharar hawaye har kukan ya dan tsaya, sai sheshhekar kuka.

Wannan karon a nutse ta fara yi mata magana, tace, “wannan ba wayo bane ko kuma dabarar da zata fishheki ba Kauthar sam. Ita rayuwar nan ta duniya morarta shine hakuri da kuma yarda da duk abinda kaddara zata jefo maka ne. Kin karbar hakan kamar nuni ne da yin tawaye ga hukuncin da mu da muka dauki kanmu a matsayin iyayenki muka miki, da kuma kaucewa umarnin Allah. Ko kina tunanin Daddynku zai ji dadi idan yaji haka?”

Ta girgiza kai da sauri.

Ta sake cewa, “to ni kin hango alamun farinciki a tattare dani yanzu?”

Nan ma ta sake girgiza kai.

Tace, “good! Don haka nake so ki taushi zuciyarki, ki kuma rike a ranki cewa ba ki bane ko tsana yasa muka aura miki AbdulMalik face sanin cewa shi din mutum ne mai nagarta, zai kuma rike ki da hannu biyu walau muna Raye ko bama nan. Ina kuma mai baki tabbacin cewa ita kanta Fahimar da ace tana raye, to wallahi babu wanda zai kaita farincikin kasancewarki a matar mijinta, saboda tasan halinshi tasan tarbiyarshi, kuma tasan da cewa zai baki duk kulawar data dace.

Yanzu kinga dare yayi sosai, don haka kije ki kwanta. In shaa Allah nayi miki alkawarin gobe idan Allah Ya kaimu zan warware miki zare da abawa. Hakan yayi miki?”

Ta gyada kai a sanyaye, ta kai hannu tana share hawayen fuskarta.

Tashi tayi tana yi mata sai da safe ta wuce.

Har ta kai bakin kofa taji tana kiran sunanta, ta juya a sanyaye tana kallonta.

Tace, “nayi miki alkawari, nima kuma ina so kiyi min alkawarin cewa daga yau ba zaki kara raba shimfidarki data mijinki ba komi wuya komi rintsi, ni kuma zanyi farinciki da jin hakan matuka!”

Jikinta yayi sanyi kwarai, ta kasa iya daga baki ta amsa sai kai data jinjina alamun tayi.
Ta sakar mata murmushi a tausashe, “na gode Kauthar!”

Su duka basu da sauran abin fada, don haka ta karasa daga kofar ta fita.

Kicin ta shiga, ta wanke fuskarta a jikin sink, ta bude firjin ta dauki gorar ruwa ta kafa a baki, bata dakata ba sai data shanye shi tas. Ta jefa robar cikin dust bin ta jingina da firjin din hannu rabbe a kirji tana maida numfashi daya bayan daya.

Allah kadai Yasan iyaka lokacin data dauka a haka, kafin taja kafafu cikin sagewar jiki ta fita daga kicin din.

A kofar dakinta ta tsaya, tayi duru-duru cikin rashin madafa, kafin ta tsallaka ta wuce, a karo na farko, cikin saninta kuma da niyya, ta tunkari kofar dakin nashi gadan-gadan kamar yaki.

Nan ma ta bata kamar mintuna biyu kafin tayi Shahada ta kwankwasa. Tayi shiru na yan dakikai tana jiran taji wani motsi amma shiru, ta kara bugawa nan ma shiru.

Sai ta sauke ajiyar zuciya ta juya, a ranta tana fadin ai tayi kokari, kuma Anty Aisha ba zata kamata da laifin komi ba.

Cikin rashin sa’a sai taji alamun an bude kofa. Ta juya a nutse tana kallonshi.
Shima kallon nata ya tsaya yana yi. Jallabiya ce a jikinshi ruwan toka mai taushi, kuma dai da alama daga bayi yake tunda ga karamin tawul nan a hannunshi yana goge sumar kanshi.

Ganin idan ba magana tayi ba watakila zasu iya shekarewa a haka, bayan ita kuma bata da abin cewa, sai kawai ta raba ta gefenshi ta shige dakin.

Yayi sarara yana kallonta fuska dauke da mamaki daya kasa boyewa.
Ita kuma tayi tsaye tana karewa dakin kallo. Komi yayi na dakin, babu hayaniya balle tarkacen da basu dace ba.

Italian bed ne makeke wanda yake shirin cinye bango guda na dakin duk da girmanshi kuwa, ya sha zanin gado mai kyau ruwan navy blue. Akwai kujerar hutu a gefen gadon, amma ba zai yiwu mutum ya kwanta har yaji dadin barci ba a kai. Don haka ta wuce kan gadon kai tsaye, ta wuce can karshe ta kwanta. Har da jan bargo ta rufe jikinta rikif.

Ya jinjina kai yana kallonta murmushi yana kubce mishi a sirance.

Inda ya baza kayan aikinshi akan desk ya nufa, yana furta, “wannan shi ake kira karfin hali fa wai barawo da sallama! A zo gidanka a nuna an fika rawa? Kodayake dai nasan zuwan na dolene ba kuma don ni ba aka yi shi, Allah dai Ya shiwa Anty na mai kaunarmu albarka!”

Tana jinshi tayi kim ta kyaleshi. Har ya kammala abinda zai yi ya kashe wuta ya bar marar haske, bata motsa ba. Shima sai bai takura ba, ya tsaya a daya gefen yayi addu’a ya tofa, ya rufa da bargo bayan yace mata, “kada dai ki manta da addu’a, sai da safe!”

Bayan dan lokaci taji numfashinshi yana fita a hankali alamun yayi barci, sai lokacin ta muskuta, tayi addu’ar itama ta shafa.

Ranar barci sama-sama tayi shi. Asubar fari kuwa ta dire daga gado kamar wadda ake mintsina tayi waje.

AbdulMalik da motsinta ya tasheshi, ya bita da kallo yana dan murmushi cikin girgiza kai, wani abin idan Kauthar tayi sai ya ma rasa abin cewa.

Duk basu fita wajen kari ba sai wajen karfe tara da rabi. Suna gamawa kuma ya dauki yaran suka tafi zagaya gari.

Dama karin sama-sama tayi shi, bata iya cin wani abin azo a gani ba. Don haka Anty Aisha tana tashi, itama ta ture plate din sandwich toast din gabanta tabiww bayanta.

A gefen gadonta suka zauna, Anty Aisha ta dauki handbag dinta ta bude ta ciro da wani hoto. Data lura da kyau, sai taga ai irin hoton data dauko ne a dakin Daddy.

Anty Aisha ta daga mata hoton tana nuna mata,

“kamar yadda kika sani, wannan Mahaifinki ne Isma’il, wannan ni, wannan Adidat, mahaifiyarki, sai wannan Nuhu ne, baban AbdulMalik, wannan kuma…” ta nuna mata mutumin data kasa ganewa, “…Sunanshi AbdulFatah”

Shiru tayi tana kallon Kauthar, yayinda itama tayi shiru tana kallonta cikin zakuwa.
Kai ta girgiza a hankali tana mai lumshe idanu, ta sake budesu ta dire akan Kauthar.
Murya kadaran-kadahan take ce mata, “wannan labari ya faru ne fiye da shekaru ashirin da biyar da suka wuce, a lokacin muna makarantar university ta Wukari dake Jahar Taraba..!”

Tuna baya shine roko! (Takori)

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Kauthar 13Kauthar 15 >>

4 thoughts on “Kauthar 14”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×