Skip to content
Part 24 of 26 in the Series Kauthar by Jeeddah

Kwana biyu da dawowarta ne bayan ta gama hutawa, daren ranar Laraba ta tsinci kanta a gaban madubi tana kara duba shirin barci da tayi.

Jar doguwar rigar barci ce a jikinta wadda ta sauka har kasa, sai dai tun daga kugun rigar ta gefen cinyarta na dama a tsage yake har zuwa kasarta. Saman rigar kuma da lace aka yi shi, yayin da hannun rigar ya kasance dan siriri hannun spaghetti.

Data kara kallon kanta, ita kanta sai taji tana burge kanta saboda yadda rigar tayi mata wani irin kyau na daukar hankali.

Sai dai kunyar zuwa da wannan shigar wajen AbdulMalik take yi ta tsaya a gabanshi. Musamman yadda rigar ta fitar mata da surarta sosai. Cinyarta gabadaya a waje take, haka saman rigar babu abinda ta bari na kirjinta, gashi daga baya ma gabadaya shape dinta ya fita.

Tun bayan dawowarta, zama suke yi abinsu lami lafiya lau tamkar dai wasu sababbin aure. Ta riga data maida komi baya ta ajiye makamanta, da gaske dai mijinta take so ta kama ta rike da hannu bibiyu.

Ta gama amanna da cewa babu wani wanda zai so ta so na gaskiya kuma na tsakani da Allah kamar shi. Mutum ne shi dake sonta tun karfinshi, wanda kuma baya boyewa a ko’ina ne. Bauta mata yake da karfinshi da dukiyarshi. Yana kuma girmamata, yana muhimmanta duk wani abu daya danganceta. To ita kam me zata roki samu a wajen namiji da yafi wannan? Ai babu.

Shi yasa suna dawowa ma ta amshi ragamar duk wata hidima tashi ta rike kam da hannuwa biyu. Ita take mishi girki, ta mishi gyaran daki da sauran hidindimunshi. Sai dai a yan kwanakin ta kasa sakin jikinta dashi sosai. Lokuta da dama da zai dangana da ita da sunan sumba ko runguma, sai ta samu ta zame cikin dabara. A gado kuwa ko kallon inda take yayi sai ta hau kankame jiki tana karkarwa. Shi kuwa sai ya kai idanu ya zuba mata yana so yaga iyaka gudun ruwanta.

Yau dai kam, ta gama yankewa ranta ta gama gudu da jin tsoron. Yau dai kam tana so ta amsa sunan kasancewarta cikakkiyar matar AbdulMalik Nuhu Kwangila

Shi yasa ta shirya mishi lafiyayyen abinci wanda ta tabbatar da cewa yaji dadinshi sosai. Tayi kwalliyarta mai daukar hankali ta riga da zani pieces -shigar da bata cika yi ba, wadda kuma tafi burgeshi- ta kashe dauri. Ya kuma yaba. Tunda ta zauna zaman cin abinci har suka gama, bakinshi bai gaji da yaba mata ba, kamar yadda idanunshi basu bar kanta ba.

Ba tare data tsaya dogon nazari ba don ma kada ta canza shawara, ta dauki doguwar hijabi ta zura a jikinta ta rufe har sawayenta, kofa ta dumfara gadan-gadan tana jin zuciyarta na bugawa.

Tana kai hannu jikin kofar da niyar budewa, sai taji ana kokarin turowa. Ta dan ja da baya tana kallon AbdulMalik daya tura kofar yana kokarin shiga dakin hannunshi jaye da karamin trolley na abinci da aka jera kananun farantai da kofuna a kai.

Ya maida kofar ya rufe yana kallonta da wani irin kallo da yasa taji kafafunta suna kokarin fara rawa.

Juyawa yayi ba tare da yace komi ba ya karasa tura trolley din zuwa tsakiyar dakin. Inda yaja karamin teburi dake tsakiyar dakin ya fara jera farantai da kofunan. Tana tsaye tana kallonshi har ya gama cikin alamun tambaya.

Ya juya a kaikaice yana kallonta, “da wannan tsayuwar ai da alwala kika dauro kika tayani nafila.”

Tayi duru-duru kamar mai neman hanyar tserewa, sai kuma ta sadda kanta tace cikin murya kasa-kasa, “ina da alwala”
Ya tashi tsaye hannuwanshi biyu a hade, yace, “great! Bismillah to!!”

Sallaya ya dauka ya shimfida musu guda tare da jagorantarsu suka yi sallah raka’a shida ta nafila. Bayan sun gama ya juya ya dafa kanta ya fara jera addu’o’i masu tsayi. Sun jima a haka kafin suka shafa suka tashi. Ya ninke abin sallar ya maidashi inda yake ya ajiye.

Ya wuce gaban teburin daya shirya kaya ya zauna cross legs. Har lokacin tana duke a inda suka yi sallah tana raba idanu.

Sai daya fara bude farantai taji kamshin gashin nama mai tsananin dadi ya hade dakin, duk da ta cika cikinta sai da taji yawunta ya guda.

Ya juya ya kalleta, wani dan murmushi mai sauti ya saki, “wai anan zaki yi ta zama ne Kauthar? Zo ki gani,” ya furta yana mai mika mata hannu.

Tashi tayi a hankali ta nufi inda yake gabanta yana bugawa. Sai da taje zata zauna, ya dakatar da ita, fuska a dan hade yake kallonta, “ai cire wannan zumbulin abun zaki yi Hajiya. Wai ba don ni aka yi kwalliyar bane? To menene kuma na rufewa? Ina ce so ake yi in yaba? To in ban ga kwalliyar ba me zan yaba kenan? Wannan zumbulelen abun da kika dora sai kace wani tamfal? To in fada miki gaskiya in dai shine bai burgeni ba sam!”

Ta turo baki, “to ni dama ce maka nayi don kai nayi kwalliya? Shirin barci kawai nayi ba wani abu ba!”

Ya kara yin murmushi, “naji, yanzu dai cire wannan abun ki gani ki zauna mu ci abinci, yunwa nake ji…”

Yadda yake maganar yana kare mata kallo, da wani abu can karkashin maganar tashi da yasa taji cewa ba akan abinci yake bada zancen ba ya kara mata fargaba. Tayi tsaye tana kallonshi bata da niyyar yin abinda ya fadi.

Ya hade fuska nan da nan, “kin ga kada fa ki bata min lokaci. Ki cire hijabin nan ko kuma idan na taso nan Allah ba ita kadai zan cire ba!”

Idanu ta zaro tana kallonshi, “you wouldn’t dare!”

Yayi wani irin murmushi, idanunshi har wani sheki suke cike da mischievousness, “Kauthar, wani lokacin kina bani dariya wallahi! Kin fi kowa sanin abinda zan iya aikatawa matukar na furta hakan. I keep my word.”

Tsayawa tayi kallonshi cike da barar-rabi. Gani tayi ya fara nade hannun jallabiyar jikinshi da yake mai dogon hannu ce, yana kokarin tashi. Ta yaye hijabin gabadaya tayi wurgi da ita ta zauna a gabanshi a sukwane. Ya saki yar dariya yana girgiza kai, “ai da kin tsaya kin ga aiki da cikawa!”

Gashin nama ne aka yi mai ruwa-ruwa, ga kuma fruits da aka yanka kanana masu zaki, da kwalin yoghurt na Hollandia. Shi da kanshi ya fara ciyar da ita duk da yadda ta so musawa.

Janta yake da hira ta barkwanci wadda tasa ta saki jikinta nan da nan, bata san lokacin data dage ta ci naman nan sosai ba da fruits din.

Dariya take yi sosai lokacin da yake bata labarin zamanin yarintar shi dasu Na’ima. Ta kai kofin yoghurt bakinta tana kurba. Ji tayi ya dakata da maganar da yake yi, ta tsaya tana kallonshi curiously.

Idanunshi kur a kirjinta inda yoghurt ya dan zuba yana gangarawa. Kallon da yake mata a lokacin, kallone da bata taba gani a idanun wani da namiji ba. Ko a wajenshi, bata taba gani ba. Kallone na tsantsar yunwa, stark hunger kamar ta zakin daya kwana ya wuni bai ga nama ba. A lokacin jinta ta dinga yi kamar ita ce naman, AbdulMalik kuma zakin.

Hannu na rawa ta ajiye kofin a kasa ta fara ja da baya a yadda take ganin yana matsawa inda take. Matsawa biyu tayi ya sanya hannu ya dafa kafadarta, ya tsaidata a waje daya.
Wani irin tsoronshi ne ya dirar mata a zuciya a take. Wata irin rigima take hangowa a tattare dashi wadda bata tunanin zata iya daukarta.

Ta daga bakinta da yake rawa, “Yaya…”

Yayi saurin kai yatsa bakinta yana katse mata maganar da tayi niyar yi, idanunshi kur a cikin nata yake girgiza mata kai, “please, yau dai Kauthar, yau dai ki barni haka nan. Nayi hakurin, nayi kawaicin, na rufe idon, not anymore! Ji nake kamar idan kika hanani muradina yau ba zan iya wayar gari ba. Don Allah ki barni haka nan Kauthar!”

Ya maimaita haka murya a can kasa har bata fita da kyar, kamar kuma mai tsoron taji shi. Ko kuwa don ya gama kusantar tane, bakinshi daf da nata, gwiwoyinsu na gugar juna?

Ba zata iya fada da baki ba, don kuwa babu ma kalaman da zata kwatanta abinda ya biyo baya.

Illa iyaka tace AbdulMalik ya nuna mata wata irin kauna so pure da bata taba tunanin wani bawa zai yiwa wani irinta ba.

Rawar jiki ya mata sosai, ya mata sambatu da sanya albarka, sai da taji tausayinshi ta kai hannu ta rufe mishi baki.

Duk da azabar da take ji, hakan bai sanyata ta juya mishi baya ba. Ta barshi yayi abinda yaga zai iya, ya sauke duk wata kauna daya dade yana dako a cikin ranshi.

Ya zube a gefenta yana sauke wani irin nannauyan numfashi. Ko ita daya ganawa azabar daya ganawa, bata tunanin numfashi ya mata wahalar fita kamar shi.

Sai daya jima a haka, kafin kuma ya juya ya jata cikin jikinshi yana share mata hawayen da take zubarwa yana zubda mata kalaman so da kauna wanda tasan har lokacin a cikin maye yake bai gama saukowa ba.

Cikin sarkewar murya tace mishi, “ruwa!”

Da sauri ya tashi ya dauko robar ruwa da basu fasa ba, ya dagata ta zauna tana cije baki don kuwa ba karamin jiki take ji ba, ya kafa mata a baki ta kafa kai tana sha.

Yace, “sha ruwa baby girl. Allah Ya shayar da ni da ke da iyayenki da iyalanmu bakidaya ruwan Alkausara ta dalilin wannan kyautar da kika yi mun!”

Bata iya ce mishi komi ba sai komawa da tayi ta kwanta tana maida numfashi wahala.

A daren bai barsu sun koma sun kwanta ba, ya shiga bandaki ya hada ruwa. Ya daddabeta don har ta fara barci, ya taimaka mata tana kuka da shagabwa da komi ya kaita bayi ta gasa jikinta sosai kafin tayi wankan tsarki.

Kafin ta gama har ya canza musu bed sheet duk da cewa ba wani lalacewa yayi ba sosai.

Riga da wando ta sanya na barci ta koma tayi kwanciyarta bayan ya bata paracetamol da ibuprofen ta sha.

Tana jinshi yana kai kawo tsakanin dakin da bandaki, ta yada kai ita dai ta hau barci. Ba ita ta tashi ba sai asubahi. Nan ma tana yin sallah ta sake komawa ta kwanta.

Ranar kam ko wajen aiki bai fita ba. Har daki ya kai mata abin kari. Tayi wanka ta shirya, ta zauna taci abinci. Sai tattalinta yake yana nan-nan da ita. Motsi daya tayi sai ya tambayeta lafiya?

Haka suka yini a gidan har zuwa dare. Tun tana dari-darin kada a koma gidan jiya, har dai ta saki jikinta ganin bai ma nufeta da wannan zancen ba. Don haka ta saki jikinta suka sha barcinsu sosai.

Suna gama sallar asubahi ne kuma yace ba wannan zancen. Tunda taji yana lalubenta ta fashe mishi da kuka, tayi magiya da rokon ya barta don Allah ta warke, cewa yayi ai dama sai a hankali zata warke.

A haka ta fahimceshi a wani irin mutum mai tsananin kyautatawa mace da bauta mata, zai kula dake kamar jaririya, haka kuma yana da kawaici da kauda kai akan abubuwa da dama, amma wannan abu daya, shine baya da hakurinshi kuma baya da kawaicinshi.

Data fahimceshi a hakan sai itama ta dage take binshi a hakan. Ta sakar mishi jikinta sosai, sai suka zama abu guda daya. Ta zama shi ya zama ita.

Satinsu biyu a gida suna barzar amarci abinsu. Sunyi wani irin kyau sunyi bul-bul dasu kamar kajin gidan gona. Wata irin kauna da soyayya mai tsayawa a rai suke gudanarwa kai kace a lokacin ne suka yi aure. Sun samu fahimtar juna sosai a dan takaitaccen lokacin fiye da lokacin da suka yi a lokacin tana gida da kuma zamansu na farko-farkon aure.

Tun dawowarta bata koma wajen aiki ba, shi dai idan ya tashi da safe zata hada mishi abin kari mai rai da lafiya, ya ci yayi nak, ta rakashi har bakin kofa ya tafi.

Zata koma ta gyara abinda zata gyara, sai ta kira Anty Aisha ko su Lukman ko su Zainab su sha hirarsu.

Da rana ma haka zata shirya abincin, idan ba zai dawo ba da ranar sai ta bada akai mishi ko kuma ta dauka da kanta ta kai mishi. Wani lokacin ma sai ta zauna a can ta jirashi har ya gama sai su koma gida tare.

Bature wai yace, “to get a man’s heart is to get through his stomach” to kuwa ta samu zuciyar tashi ita kadai. Tana da tabbacin idan ma zuciyoyi biyu ke gareshi to a sukwane zai damka mata su. Tunda ta kama girkinshi ta rike gam, ga kuma kulawar da ita take bashi. Duk wani abu daya danganceshi ko yan uwanshi tana kambama shi tana kuma taka-tsan-tsan da bacin ranshi, sai shima yake girmamata din yake kuma takatsantsan da nata bacin rai. Riritata yake kamar kwai.

Ranar assabar ta kasance ranar karshen mako, babu aiki. Basu tashi ba sai wajen karfe goma na safe. Ita ta fara farkawa, ta zame daga jikinshi a hankali don kada ta tasheshi saboda taga barcin nashi yayi nisa sosai.

Bayi ta shiga ta wanke bakinta da fuska, a gaggauce ta fada kicin ta hau fito da abubuwan da zata bukata don ta hada musu abin kari mai sauki saboda sun makara, ga uwar yunwa da take ji kamar me.

Chips take soyawa na dankali, data gama kuma sai tayi vegetable sauce. Normally da egg sauce take hadawa, amma yau gabadaya sai taji bata son kwan, tunaninshi ma kadai har wani tukukin amai taji yana kokarin sanyata.

Tana aikin take tunanin dalilin daya hana bakonta zuwa. Duk a lissafinta satika biyun da suka wuce yakamata ta ganshi amma har zuwa yanzu shiru take jinshi, kuma lokaci zuwa lokaci dai ta kan ji dan kartawar mara alamunshi. Bata zurfafa tunanin nata ba ta tabe baki, tunda taji dama ance ai mu’amalar aure tana canza tsarin abin. Watakila dalilin kenan.

Sai data shirya komi akan teburin cin abinci sannan ta wuce dakinta tayi wanka. Da yake mai aiki taje ta gyara musu falo kafin su fita, ita kadai suka bari cikin ma’aikatan da Kauthar din ta sallama wadanda suka hada da mai girki da kuma masu gyaran dakuna, aka bar mai gyaran falo kawai da masu ban ruwa shukoki. Su kuma wadanda aka sallama ta hadasu da kudade masu tsoka da zasu tallafesu.

Riga da wando ta sanya masu fadi na shan iska, ta dora hula tare da zura silifas a kafarta ta fita hannunta rike da wayarta.

Tana niyar ta je ta tasheshi idan ma bai tashi ba, sai kuma ta ci karo dashi dai-dai yana fitowa daga dakinshi. Don haka suka runkuta zuwa kan dinning.

Suna cin abincin ne ta kalleshi cike da marairaita, tace, “Yaya don Allah wannan satin ka barni inje gida, ina kewarsu Lukman da yawa.”

Yayi dan murmushi, yace, “kwantar da hankalinki, ban fada miki da wuri bane don kada ki gaji da jirana, amma in shaa Allah zan dauki hutu cikin wannan satin, zamu je Abuja muyi sati a can. Hakan yayi miki?”

Ta gyada kai da sauri tana dan tsallen murna cike da farin ciki.

Don haka a cikin satin ya dauki hutu daga kamfaninshi, ya barshi a hannun amintattun ma’aikatanshi, su kuma suka yiwa Abuja tsinke.

Zo kaga murna wajensu Lukman da Anty Aisha. Ta rasa ina zata jefa Kauthar taji dadi, duk inda ta gilma binta take yi da ido kamar ta sungumeta haka take ji saboda irin kyan da tayi. Hankalinta ya nutsa da kauna da kulawar da taga AbdulMalik yana mata wadda ya kasa boyewa. Ta kuma ji dadin hakan.

Sunyi sa’a Daddy yana gida, kuma wani abun mamaki sun jima a bangarenshi ana ta hira ta ban dariya da nishadi.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Kauthar 23Kauthar 26 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×