Soyayyar Mukhtar a jinin ta take, a zuciyarta take. Duk yadda taso ta yakice son shi daga ranta ta kasa, daina kuka abun ya gagareta. Cike take da haushinsa amma duk da haka zuciyarta da shi take bugawa a ko wanne sakan da yake wucewa. Nisawa tayi tana sosa idanunta wanda yanzu sun gaji sun bushe. Ta kalli agogo taga biyun dare. Mikewa kawai tayi ta tafi daura alwala. Ko da ta dawo tayi raka'a biyu sai ta janyo wayarta ta buɗo messages dinsu da Mukhtar ta soma karantawa cike da kewar sa da ciwon rai.
Ke zan. . .