Kallon wayar ta kuma yi a karo na biyu ganin sunan Tariq na yawo kan wayar yasa gaban ta kuma faɗuwa kallon agogo ta yi goma saura na dare wani tunani ne ya faɗo mata, wataƙil yana ɗaki Rauda ta ɗauki wayar wannan yasa bata ɗaga ba kiran Tariq na katsewa na Dr ya shigo murmushi ta yi sai dai shigowar Abdallah yasa kan ta ɗaga ta nuna masa gefen gadon alamun ya zauna kafin ta ɗaga.
Da sallama ta ɗaga wayar amsawa ya yi tare da faɗin "sarauniyar birnin zuciyata mun wuni lafiya?," murmushi ta. . .