Skip to content
Part 51 of 53 in the Series Ko Da So by Fadimafayau

Shirye shiryen biki ake tayi gadan gadan musamman ma daga bangaren Dr ƙaraye wanda ya zaman masu wani babban shagali, kai kace bikin fari ne zaiyi. Duk kan su a cikin zumuɗin ranar bikin suke da son ganin Hafsah duk da ya nuna musu ita a hoto. Mum kamar ma tafi Hafsa murna da wannan bikin, shirye shiryen kawai take, kana ganin ta Kaga wadda ke cikin farinci kai kace autar tata auren fari zatai, sam kamar ta mance Hafsan da ta taɓa aure harda yara huɗu. Kayan lefen da aka kawo suka kuma sanya Mum cikin farinciki yanzu take ji aranta Hafsan zatayi aure. Yadda kowa ke murna da auren yasa hankalin Hafsa kuma kwanciya da son ganin auren nata, ayanzu ko tunanin Muktar baya faɗowa ranta.

Gabaki ɗaya abun duniya ya ishi su Abdallah. Zaune suke cikin ciyayin tsakar gidan sunyi jigum abun tausayi suna shawara da junan su, Faruk ya dube su yace, “in gobe mun tashi daga school, zan fita kamar zan siya abu sai ku biyo ni. Mu je mu roki Abiy ya bawa Mami hakuri, ni wallahi bana son ta auri wani, shikenan inta auri wani fa bamu san gun wa zamu zauna ba.”

Abdallah ya dan kalle shi ya tabe baki. “i aint going nowhere. Basu damu ba. Especially Abiy, ai a gaban mu Mami tayi ta bashi haƙuri har faɗuwa tayi anma muna dawowa daga asibiti still bai haƙura ba ya koremu. Ba ruwansu da rayuwar mu ai, tunda gashi itama Mamin tafiya zatai ta barmu.”

Duk wayon Abdallah da irin iya maganarsa da iyayen suke gani yafi Faruk wayo, sai Faruk din yau ya fishi tunani. Sannan shi bai kai Abdallah taurin zuciya ba. Shi din Umar ne mai zafin faɗa amma me kyaun zuciya da tunani. Ya tsura masa ido sannan yace, “Kan mu zamu yiwa ai. They’re our parents and they’re not perfect. Ko ba zaka je ba, ni zani. Kulthum are you in?”

Ta gyada kai alamar eh.

Numfashi Faruk ɗin ya furzar tamkar wani Babba kan ya cigaba.

“Mami tafi son Abiy kuma tafi son mu. Kawai dan Abiey ɗinne yaƙi haƙura.” Kauthar ta fada, ta qare da yar dariya wadda tasa Abdallah bacin rai.

Cikin kufula Abdallah ya ce. “Ba wani tafi son wancan mutumin da baya sonmu ina kuma kawai yaƙe yake in ya ganmu, He seems to be struggling to contain his anger towards us, anma Mami taƙi fahinta, bata damu damu ba.” Ya tashi.

Kallon juna sukayi kawai kafin su bi Abdallah da ido wanda gaba daya ya tashi daga caring Ya Abdallahn su da suka saba dashi. “Mudai zamu ko yaya?” Kausar ta faɗa tana duban babban yayan nasu Faruk ya gyaɗa kai kawai alamun “Eh”

*****

Rashida ce zaune cikin cikakkiyar sutura har da dan kwali da kwaliyyarta zaune a tsakar gida tare da Inna suna cin gyada. Gefen ta kuma Hajara ce wadda itama tazo gida. “Wai Inna haka zaki zubawa Yaya ido yana abubuwa kamar ba namiji ba. Shi yace ba zai dawo da ita ba kuma ki duba kiga ko sau daya bai je ganin yaran ba. Ai dole su tunzura.”

Inna ta ja numfashi mai nauyi sannan tace, “kune yan uwansa, ku ya kamata ku bashi shawara. Don ni har yau ban san meye dalilinsa ba, yarinya me hankali…” ta tsaya tana tunanin yadda Hafsah take girmamata da duk abunda ya shafe ta. Ko sau daya ba zata ce ga sanda Hafsah tayi mata ba daidai ba haka kuma a duk yadda take ganin zamansu da Mukhtar ba zata ce taga alamar zasu taba iya rabuwa ba. Kaddarar su ba karamin mamaki take bata ba.

Tun ranar da Mukhtar ya fadawa Rashida saki ta shiga hankalinta. Ta sani sarai mijinta yana kokari da kula da ita. Ta sani ita ta dorawa kanta wannan hakin ko in kula. Ba tare da kowa ya ja ta ya sake mata nasiha ba tayi wa kanta fada. In har Mukhtar zai iya rabuwa da Hafsah duk kyan halinta toh lallai ba karamin hakuri Nura yake yi da ita ba. Sana’ar ma da ake ta fama da ita tayi sai gashi tazo neman jari. Tuni tayi amfanin da kongon bayan gidansu wanda Nura ya bata ta zuba kaji take kiwo abunta bayan te nemi gafarar sa. Ranar Nura kamar ta mishi babbar albishir. Da ta lura ma sai taga kamar yafi ji da ita ma akan amaryar.

Ita kam kamar don ita aka yi sakin nan don ya zamar mata silar gyaruwa duk da bata san dalilin faruwarsa ba.

Suna nan zaune dai suna tunane tunane Mukhtar ya fado gidan. Sai da yaje sallah ya dawo sannan yazo ya zauna hade da ajiye musu ledar tsire.

“Shi nama, Allah yayi masa wata daraja…” Hajara ta fadi tana kai loma. Dukkan su suka sa dariya.

Rashida ta tabe baki tace, “kamar ba kya ci a gida.”

“Hnmm ai baki san tsire na daban bane? Yo ni ban taba jin dadin nama ba sama da tsiren siyarwa da kuma kebab din anty Hafsah.”

Sunan Hafsah da ta kira ne yasa ta saci kallon Mukhtar wanda ya nuna halin ko in kula. Sosai yake bata mamaki yadda ya zama lokaci guda. Ita kanta Hajara ta sha gwada son dake tsakaninsa da matarsa ta hanyoyi da dama amma baya raga mata. Tsaf yake nuna mata cewa matarsa tana da kiima sosai a wajen sa. Ta rasa mene abunda ya faru haka.

“Ku gama santin in baku wani albishir.”

Inna ce ta kalle shi wannan karan taga alamar yana su ya nuna ai cike yake da farinciki. Sanin halinsa yasa ta san kawai yana nema ya yaudari kan sa ne amma bari de taji.

“Kai dan Allah Yaya. Kace Hajj ka biya mana.” Hajara ta fada cike da tsokana.

Ya karkata hularsa yace, “na sami matar aure.”

“Ayiririri…” Rashida tayi guda ta dora da. “Ashe da rabon anty Hafsah zata dawo. Kai Allah na go…”

Bata karasa ba ya katse ta. “Sunan ta Sarah. Sarah ce zabina.”

Kamar wanda ya fadi wani abun tashin hankali haka duk suka yi jigum suna kallonsa kawai dukkan yakini da tunanin zai dawo da Hafsah ya fita a ransu.

“Allah Ya sanya alkhairi.”

*****

Sati biyu aka saka bikin Hafsah da Dr Karaye. Sosai take ta shirye shiryen zama matarsa don ya gama tsarata ta tsaru. Duk da haka kuwa ranar da aka saka musu ranar aude kasa bacci tayi. Tunanin yaranta duk yabi ya cikata. Ta sani a farko babu yadda zatayi ta tafi dasu. Sai dai me? Bata son barin su ko na kwana daya ne. Ya zasuji yanzu? Da suna hakuri zama babu babansu yanzu kuma ace itama bata nan? Kuka ta dinga yi tana tunanin mafita a daren. Ganin ba zata taba iya kiran Mukhtar ta roke shi ya dinga zuwa ba yasa ta hakura. Ta yaya ma zata roke shi bayan daidai da sabulu bai taba kawowa don a kula masa da yaran sa ba.

A haka dai ta hakura ta lallashi kanta kawai a barsu wajen mummy har zuwa sanda zata san yadda zata shawo kan angonta su dinga zuwa mata ko hutu ne don ta san da takura ne ma yasa ba zata dauke su ba. Tana son daukan Aiman amma bata son yayyin suji babu dadi. Da kyar dai ta tausasa zuciyarta ta hakura.

Tun da aka fara shirin biki wanda mummy ta zage tana ta order, Hafsah ta sa a ka kai yaran gidan Anty Ameera.

Kallon wayarta take yi kafin ta turawa Bilkisu message.

Seriously? Na fada miki an sa rana amma ba zaki zo ba?

Bayan wasu mintuna sai ga reply din Bilkisun yazo.

Kiyi hakuri bestest, I’m quite occupied. Ina samun sarari zan zo. Ya za’ayi ace babu ni a wannan shagalin?

Reply din sam baiyi wa Hafsah dadi ba sai kawai ta ajiye wayar. Kar dai haushinta Bilkisu take ji har yanzu. Ita sam ta kasa gane kanta tun kafin ma Tariq ya mata confessing. Gaba daya Bilkisu ta dan ja baya da ita. Duk da suna samun haka wani lokacin kowa sha’anin rayuwa ya shige masa amma wannan karan sai taga kamar dai Bilkisun haushinta take ji.

Ganin she already had alot on her plate ne yasa ta saka issue din a bayan mind dinta ta tashi tayi sallah sannan ta kira aunty Ameera don taji yaran.

“Subhanallah sis, i hope Sadiq bai tayar miki da hankali ba. It’s gonna be fine, yanzu nake son kiran ki dama. Wallahi Faruk da Kulthum ne bamu gansu ba.”

Gaban Hafsah ya yanke ya fadi. Da kyar ta sami jarumtar bata amsar cewa tana zuwa. Tuni ta hau mota ta wuce school dinsu. Tana ta ganin kiran Dr Karaye ma amma sam bata da nutsuwar da zata dauka.

Isarta school din ta tarar da yadda ake ta yiwa me gadi fada wanda bai ma san yaran sun fita ba. A gefe ta hango Abdallah rike da Ayman. Da sauri ta karasa wajen sa ta ja shi gefe.

“Ina suke. Ban son kwana Abdl, na san sun gaya maka.”

Ya tsura mata ido sannan a hankali ya juya. Cikin bacin rai Hafsah ta fusgo bayan rigarsa wanda ya qara tunzura shi amma yayi shiru bai ce komai ba. Tayi juyin duniya yaqi bata amsa.

“I’m gonna be mad ka sani. Meya same ka haka?”

Ya daga kafada. “You don’t care Mami. Ki dena magana kamar kin damu damu.”

Kamar a cakawa Hafsah mashi a zuciyarta haka taji. Cikin diririce wa ta kalle shi gami da sauke gwiwarta kasa ta riko kafadunsa.

“Me kake cewa ne haka Abdallah.”

Idonsa cike da hawaye yace, “sun tafi office din Abiy…” da haka ya yi gaba can inda su Sadiq suke ya bar Hafsah durkushe a gun, jikinta duk yayi sanyi.

Anya zata iya yin auren nan kuwa?

Da kyar ta tashi taje inda su Sadiq suke tace, “Yaya don Allah ku tafi gida. Zanje na same su. Kar a bari mummy taji please.”

Ba tare da karin bayani ba, Sadiq ya fahimce ta. Cike da tausayin ta ya gyada mata kai sannan ya kama hannayensu tare da yiwa matar sa inkiya su tafi.

Hafsah motar ta ta nufa. Bata kama hanyar ko ina ba sai office din Mukhtar.

*****

Tunda ta qarasa building din take jin gabanta yana faduwa. Sau daya ta taba zuwa. Ranar ma mantuwa yayi kuma aiki ya sha kan sa ya saka ta kai kasa contract papers din da kanta. A hankali take hawa benen tana karanta sunayen offices din har tazo in da ta ga sunan sa.

Duk sanda zata ji sunan sa sai zuciyarta ta doka masa. Duk sanda tayi tozali dashi, bata manta ranar da ta fara son shi. A duk sanda suka zauna waje daya kuwa soyyayar sa sabuwa take koma mata amma sai gashi yanzu sun rabu. Duk yadda taso ta tsayar da numfashin ta kasawa tayi saboda wata irin fargaba ce ta kama ta. Amma fargabar tafi yawa ga tunanin makomar rayuwar yaranta. Ta sani cewa son Mukhtar dashi zata shiga kabari saboda zuciyarta kamar tare a haka halicce su da ta ta. Sai dai a yanzu ta yarda ko da so kana iya hakura da mutum don har abada ta hakura dashi. Son nan dai da take masa baya tafiya… duk da kuwa son da take wa Dr Karaye. Shi Mukhtar, a dabi’ance take son shi gami da wasu dalilan da halayensa da suke burge ta. Dr Karaye kuma ta fara son shi ne da ta bashi dama. Mukhtar just seized her heart unannounced.

A hankali ta kwankwasa kofar tana ture tunanin da yake ta mata yawo a kai.

“Come in.” Taji muryar wata ta bata amsa. Ta dauka zata ji wani abu amma sai taji wayam. A kasan zuciyarta ta godewa Allah ta murda handle din.

Idanunta akan wata kyakkyawar budurwa ya sauka. She’s a few inches shorter than Hafsah. Kalar fatar ta ma kusan kalan na Hafsahn ne.

Tana da kyau daidai nata.

Sanye take cikin doguwar rigar yadi wadda dinkin ya dan kama daga sama sannan ya baje a kasa. Tayi rolling din mayafinta ya dan sauko.

KKausar na gefen ta tana shan ice-cream suna ta dariya yanayin su ya dace sosai ita kanta Hafsan da ba ita ta haifi Kausar ɗin ba zata rantse wannan matashiyar ce ta haife ta.

A ruɗe Khausar ta miƙe tana fadin, “innalillahi Mami..” Ta faɗa office ɗin Muktar wanda suke zaune shida Faruk yana riƙe da hannun yaron da alamu lallashin sa yake.

Ɗauke idanun ta daga kan Sara Hafsa ta yi tare da Kallon Office din sannan ta ce. “Mukhtar?”

“Yanzu zai fito. Please sit. I’m Sarah, his secretary.” Saran ta faɗa

Tunda ya bude kamshin turaren ta da bashi da karfi amma duk inda yaji sai ya daki hancinsa ya fara ji. Zuciyarsa ta buga sosai fiye da tsammanin sa.

Tsaye take a gefen Sarah tana saurarenta, kamar ko yaushe tana sanye da Abaya da take matukar karbarta. Fuskar nan banda lipgloss babu komai amma ba karamin daukar hankalinsa tayi ba. Ko kusa ba zai hada ta da Sarah ba. Gashi ta mugun kara kyau, fatarta sai sheqi take ta faman yi. Haka ma har yar kiba yaga tayi. Gaba daya sai yaga ta zamar masa sabuwa. Ko da suna tare baya ganin wata mace in ba ita ba. Kawai sai ya sami abunda zai ga babu ya irinta. Hafsahn sa daban take. Soyayyar ta ta dinga taso masa har sai da yaji kamar yaje ya ce tayi hakuri ta zama matar sa. Da kyar ya jawo kafarsa zuwa gare su sannan ya gyara murya.

“Sarah B, UmAbdallah.” Ya nuna mata Hafsah. Cikin wata irin kunya da jin nauyi har ma da kishi Sarah ta kalli Hafsah kafin a hankali tace.

“Mun gaisa.” Da haka ta sulale ta bar office din.

Shiru ne ya cigaba da kewaye su har sai da Faruk ya raba, “Mami don Allah kiyi hakuri.”

Ta kalle shi ta dauke kai. “Mami kiyi hakuri ba zasu sake ba.” Mukhtar ya fada yana kallon yaran.

“Ka kira ta ta fita dasu akwai abunda zan gaya ma.” Ta fada cikin bada umarni. Kamar wadda ta yiwa abu haka ya kama hannunsu da kansa ya kaiwa Sarah. Bai jima ba ya dawo.

“In kana son custody dinsu mummy zaka je ka samu. In baka so ya kamata na sani domin bana son a rabawa yarana hankali su rasa inda zasu fuskanta a rayuwa.” Ta fada numfashinta a harhade.

Ya nisa. “Yanzu har kin manta da rayuwar mu, aure zakiyi saboda baki tausayi na Hafsah?, Yanzu ba zaki iya bani lokaci ba, haba Hafsa…… Dan Allah kiyi haƙuri mu mayar da auren mu,”

Cikin hasala ta ɗaga masa hannu.

Tambayar ta bata rai matuka bata san sanda tayi losing temper dinta ba ta tara zazzago masa masifa.

“Baka lokaci fa Muktar kana nufin tun daga sakin har iddar ba lokacin da zaka iya mayar dani ba, ko kuwa shekara biyun da nayi duk bai isa ba, eh aure zanyi. Auren soyayya me zafi. Tausayi har kana da bakin magana? Sanda ka yanke igiyar auren mu ka tsaya tunanin rayuwarmu ko ka tsaya tausayina ko na yaranka? Nace ka tsaya ne, Mukhtar?”

Kuma ɗaure fuska ta yi. “Ina rokanka ina kallon cikin idonka lokacin amma baka dube ni ba. Bayan nan har tsawa ka daka min akan kar na sake maka maganar mayar da auren mu. Da kanka fa ka raba mu ba tare da nasan lefin me nayi maka ba Mukhtar. Ashe dama tukwicin son da nake maka shine nasha wahala? Duk dawainiya da dakon sonka danayi ai baka duba shi ba. Toh don me zan dakatar da rayuwata saboda kai? Kai ne autan maza ko me? Wai har ma kana da bakin maganar tausayi.”

“Hafs…”

“Ka dakata bana son jin amon sunana a harshen ka. Ka jima da fita a raina wallahi Mukhtar. I gave you all my youthful years amma baka gode ba. Ka min babbar illa a rayuwata but alhamdulillah na samu wanda yasan darajata. Na samu wanda ya ke da zurfin tunani da hangen nesa gami da yin uzuri. Ko ma mene dalilinka na saki na, bana son ji. Sai dai ka sani in har zargi na kake yi akan abunda ban aikata ba kuma kayi hukunci akan sa, toh wallahi ban yafe maka ba. Kuma kar ka taba tunanin zan yafe maka har karshen rayuwata.”

Sosai ta zage tana ta amayar da dukkan nauyin da take ji a ranta. Fuu ta fice tare da jan hannun yaranta sukai waje.

<< Ko Da So 49Ko Da So 51 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×