Skip to content
Part 8 of 48 in the Series Ko Da So by Fadimafayau

Har sun wuce Salisu ya riƙo shi “Please kazo muje yau ɗaya dai”

Kallon agogo Muktar ya yi ” na faɗa ma so nake in kwanta da wuri”

Tsaki Salisu ya yi ” kwanciya at this time kofa magariba ba’ai ba, ko kuma baka sallah ne yau?”

Haushi ne ya kama Muktar “kaifa ɗan iska ne wallahi, to wanki nake son inyi in maka short test ɗin da na musu and ina son duba Google”

Watsa hannu Salisu ya yi ” ba zancen iskanci nasani ko ka fara al’ada ne, yanzu muje in mun dawo zan taya ka wankin”

Dafe kai Muktar ya yi ” wai ana dole ne?, ni kasan sam bans son sabgar ƴan mata wallahi, bare ma ƙaramar yarinya irin Maryam ba in da zani”

Jan sa Salisu ya fara “wallahi sai kaje” jin ya rantse yasa Muktar kawai bin sa s baya rai a bace, shi in za’ai komai kar asashi sabgar mata.

Tsaye suke ƙofar gidan su Maryam ɗin Muktar ya harde hannun sa a yalwataccen ƙirjin sa, fuska a ɗaure, Salisu ne ya matso “dan Allah Malam ka taimaka ka saki ranka karka tsoramun ita” hararar sa Muktar ya yi, fitowar Maryam yasa shi fasa faɗar abin da zai ce, ya ɗan saki fuskar sa kaɗan.

Fuskar ta ɗauke da fara’a ta ɗan rissina ” lah Malam yau da kai aka zo ina wuni?”

Kafin ya amsa Salisu ya yi caraf ya ce ” eyye mai nake son gani wato idaniyar bani suka fara gani ba wato to walllahi kishi nake”

Dariya ta yi “Haba Masoyin Maryam kaima kasan kai na fara gani wai in fara girmama shi matsayin baƙo” ta faɗa cikin salon tata yaudarar, “anma kayi haƙuri bari inkuma fitowa” ta faɗa kamar zata juya .

Murmushi ya yi ” ai nasan ni kika fara gani” taɓo Muktar ya yi wanda ya yi saƙaro yana kallon su, kallon da bazaka iya cewa na mamaki bane ko na jin haushi ” Malam tana gaida ka kayi tsit”

Murmushi Muktar yayi ” ba shiru na yi ba jira nake ku gama soyayyar sai in amsa” kunya ce ta rufe Maryam ko da Muktar bai koyar da ita ba a secondry shiɗin bai da kalar raini bare kuma malamin ta ne.

“Koma dai mene ni karka sa ta dena magana zo ka tafi,” Salisu ya faɗa yana ɗan ƙoƙarin tura shi.

Murmushi ya yi “dadai ni na kawo kaina shine za’a koren, Malama Maryam mu kwana lafiya” ya faɗa kafin ya bar gun.

Har ya wuce ya dawo duda gari ya fara duhu amma hakan bazai sa ya kasa gane ɗaya cikin ƙannen sa ba duk inda ya ga wani, Hajara ya hango lafe jikin dutsen dala inda ya raba layin da gidaje yayin da Garba ke tsaye jikin gidan yana kallon ta kwatar da ta raba siririn layin ta musu tsakani dariya kawai take da alamu hirar ko abin da ya faɗa ma ya mata daɗi.

Rai ɓace Muktar ya ƙarasa sam bata ankara da shi ba lokacin da yake tawowa sai muryar sa ta ji “Uban me kike ana” a tsora ce ta bar gun da ɗan gudun ta ba tare da ta tsaya bashi amsa ba.

A fusace ya juyo ya kalli Garba wanda ya yi tsuru tsuru “yanzu in ƙanwar ka ce zaka ji daɗi wani kato ya jawo ta zance wani gurin ba ƙofar gidan ku ba?”

Sosa ƙeya Garba ya hau yi ” wallahi ba cutar da ita zan ba nifa auren ta za..””

Ɗaga masa hannu Muktar ya yi “zaka aure tan ka kasa jurewa a baka damar zuwa gida zance, malam ka fita sabgar ta tun kan ƴan sanda suyi mana iyaka” fuuu ya bar gun

Ita kuwa Hajara tana zuwa gida ɗaki ta shige hankali tashe sam batayi tsammanin ganin yayan nata a hanyar ƴan Kado ba tunda tasan sam baya yin area ɗin shi yasa ma ta ce su dinfa haɗuwa da Gaban anan.

“Ke Hajara!!!” Ya faɗa cikin hargowa lokacin da ya shigo gidan “kina ina ne ko sai na fito da ke na tattataki ki”

Jiki a saluɓe ta fito gaban ta na faɗuwa sam bata son abu ya haɗata da yayan nata bare irin wannan, cikin faɗa yake magana ” wato da na ce ki fita sabgar yaron nan shine kika koma binsa wani gurin ko, wato ke ba zaki iya maraicin ki ba”

Cikin rawar murya ta ce ” wallahi yaya Inna ce ta aikeni ƴan kado gurin Musa mai kilishi shine nagan shi tsayawa ta kenan mu gaisa kazo gun Allah” ta faɗa tana ɗaga hannu sama.

Tsaki yaja ” nidai shawara zan baki da ki ɓata sunan ki gwanda ki ce ya fito a aurar dake kowa ya huta” ya faɗa tare da shiga ɗaki ba tare da jiran amsar taba.

Inna ce ta kalle ta ” Gaskiya ya faɗa miki gwanda ki ce ya fito kowa ya huta, ni da ki jaza min masifa a gari, ƙarim wani zagin a unguwar na ban muku tarbiyya ba gwamma ko bashi ne in ɗauko inmiki kayan gado”

“Allah inna kawai gaisawa zamuyi yaya yazo…” Harar ta kawai Inna ta yi ta kasa karawa.

*****

Yes shigo ya faɗa lokacin da take buga ƙofar Hafsa ce rike da riguna kala biyu ta shigo ɗakin wanda baka jin komai sai ƙamshin air freshener mai sanyaya zuciya ɗan ta shi zaune Usman ya yi daga kwanciyar da ya yi ya dube ta ” to sarkin damu mene kuma, kinsan dai ba ɗin ki nake ba ko?”

Murmushi ta yi ” kai yaya Usman nima ba ɗin ki na kawo ma, tayani zaɓa wanne zai fi mun kyau zamu je ɗan wani outing ne.”

Zaro ido ya yi ” what are you mad ke da waye” dariya ta yi “kalli fuskar ka to ni da Hidaya da Bilkisu ne” ajiyar zuciya ya yi ta wasa “oh na ɗauka keda wasu ƙatti ne yanzu mutun ya jawowa kansa”

Dariya tasa mai ƙarfi ” kaji Yaya Usman da kuri sai kace zaka iiya wana abu”

Kwafa kawai ya yi ” Allah yarinyar nan kin rainani walllahi, wannan ta fi kyau” ya nuna ta hannun daman ta.

Kallon ta ta yi na sakanni ” No wannan ta fi” ta faɗa kafin ta fice girgiza kai ya yi wannan yarinyar da matsala take da tasan wadda take so zata zo damun sa.

Bai gama tunanin ba ta dawo “baka ban gudunmawa ba, jiya naje gidan yaya Sadik ya bani nasa saura kai” ta fada tana miƙa hannu.

“Ni mai zan baki?, Shi ai rich man ne ni kinsan am broke, Lecturers are not rich”

“please joke aside miƙo sauri nake” ta faɗa tana miƙa hannu

Hannu ya sa a aljihu ya ciro kuɗi kan ya ce wani abu ta amsa Thank you Yaya” ta faɗa tare da yin waje murmushi ya yi tare da miƙewa ya rife ƙofar sa kafin tazo tace shi zai kai su.

Ta yi kyau sosai zakai tsanmanin biki zasu, a nutse take sakkowa daga bene ” Mum na tafi” ta faɗa lokacin da ta leƙa ɗakin Mum ɗin,” ina kuma zaki?”

Murmushi ta yi ” tunfa last week nake ce miki zamu ɗanje cin abinci da su Hidaya jiyama na faɗa miki”

Fitowa Mum ɗin ta yi ” kuma ahaka” ta faɗa tana kallon ta

Kallon kanta Hafsa ta yi alamun mai na yi.

“Yanzu ke sai ki fita da tsunmokaran nan?”

“Lah Momy tsummokara fa, waɗan nan ɗin?”

Banza Momy ɗin ta mata tare da yin sama hakan yasa Hafsan bin bayan ta wasu kayan ta canja mata sanadin tana sauri yasa ta kasa musu ta karba ta canja tare da yin waje suka nufi gidan su Bilkisu, Umman su ta fara tozali da ita a falo cike da fara’a ta amsheta suka gaisa kafin ta wuce ɗakin su Bilkisun.

Ƙanwar Bilkisun na kan gado tana kallo a system ta shiga tana ganin ta ta hau murmushi suka gaisa “kardai ki cemun bata kintsa ba?”

Murmushi Ummi ta yi “yanzu ta shiga wanka” mita Hafsa ta fara ” lallaima matar nan da kinsan baki shirya ba shine zaki yi ta azazzala ta”

Shigowar Bilkisun ya sata sake sabuwar mita yayin da Bilkin ta mata shiru, kamar minti goma ta tsaya gaban ta to ai saiki shiru na shirya taso mu tafi daga nan suka wuce gidan su Hidaya, ko gidan basu shiga ba ta fito dan duk ta fisu son a fita.

Sosai sukai yawo sun sha hotuna kamar ba gobe, sunci har sun ture shi kansa driver din nasu sai da ya samu nasa rabon dan har guziri ya yi, guri wurin huɗu sukaje kafin su yanke shawarar komawa gida, a ƙofar gidan su Hidaya ma dakyar suka rabu sabida sabuwar hira da ta ɓarke.

<< Ko Da So 7Ko Da So 9 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×