Skip to content
Part 8 of 8 in the Series Kudi Ko Rai by Mustapha Abbas

Cikin ƙanƙanin lokaci Hajiya Sabuwa ta fara ganin dishi-dishi, wani irin jiri ya fara kwasar ta, kawo yanzu dai ta fara gane inda al’amarin ya sa gaba, ita ma so suke su kashe ta.

Cikin ƙarfin hali ta sake buɗe baki tana duban Cika Aiki ta ce da shi, “Ɗan iska mugu, ashe kai suka sa ka kashe min ɗa sannan nima suka turo ka ka kashe ni, Zinatu har rayuka nawa za ku kashe saboda KUƊI?”

Cika Aiki ya sa ƙafarsa mai sanye da gabjejen takalmi ya yi mata ɓarin makauniya a fuska, yana faɗin, “Ka ga shegiyar tsohuwa da kwakwazon tsiya?”

Hajiya Sabuwa ta ɓingire a wajen hanci da bakinta suna zubar da jini, wannan karon bakinta ya mutu murus, babu kukan da take bare ta samu damar magana.

Cika Aiki ya juya gefen sa ya ɗauko ɗan karamin filo a kan kujera ya sunkuya, ya ɗora mata shi a fuska kana ya sa ƙafarsa ya danna filon, tun Hajiya Sabuwa tana sa hannunta tana ƙoƙarin ture ƙafar tasa har abin ya gagare ta ta fara shure shure, tuni dai rai ya yi halinsa.

Duk abinda ke faruwa Zinatu na tsaye tana kallo, yanzu dai ta tabbatar sun gama da matsalar Hajiya Sabuwa sai me?

Washe Garo

Tun daren jiya har kawo yanzu zuciyar Habib ke ta kai kawo kan tunanin wanda ya sanar da Hajiya Sabuwa labarin abinda ya faru cikin awa guda kacal, a iyakar tunani da bincikensa kaf bai gano kowa ba, sai dai ko shi Suraj ɗin ne ya faɗa mata kafin ya wuce, to amma ta wacce hanya zai sanar da ita, sai dai ko ta wayar salula, amma dai a iya saninsa Hajiya Sabuwa ba ta da wata alaƙa da wayar salula.

“Ka sani ko daga baya ta yi? Wata zuciyar ce ta sanar da shi hakan, tabbas komai zai iya faruwa, domin tabbatar da gaskiyar l’amarin ya zame masa wajibi ya yi bincike a wayar Suraj, ko ba komai zai iya ganin kira na ƙarshe da ya yi ko a ka yi masa, wannan tunanin ya haddasa masa miƙewa tsaye daga kwancen da ya ke.

A gaggauce ya shirya ya fito ya kulle gidan. Sai da ya fara biyawa ya ɗauki Zinatu tukunna sannan suka wuce.

*****

Su biyu ne suka yiwa teburin da’ira, wanda idan ka ɗauke ƙaton kwalin lemon Eva da yake saman sa sai wasu kofunan glass guda biyu dake maƙwabtaka da shi babu komai a kai.

Habib ya ɗaga kansa yana duban Cika Aiki da ya tunkaro inda suke zaune a lambun shaƙatawar ɗaya daga cikin gidajen hutawar mallakar Alhaji Mustapha, dai dai lokacin da ya ƙaraso gaf da su ne to Zinatu ta yi masa nuni da da wata kujera dake gefen su, ya gyara wa kujerar zama sannan ya zauna, Habib ya miƙa masa hannu suka cafke duk a lokaci guda kuma ya sa hannunsa guda ɗaya cikin aljihu ya fiddo wayar Suraj ƙirar Samsung ya miƙa masa.

Habib ya karɓa ya danne makunnin wayar har sai da ta kawo sannan ya ɗaga, bayan ya bar ta ta gama duk loading ɗin da za ta yi ya shiga dialled call, suna na farko da idanunsa suka fara gani ne ya sa shi ɗagowa ya kalli Zinatu wadda ita ma shi take kallo cike da alamun tambaya a fuskarta.


“Ya kira wata mai suna Maryam,” lokacin kiran ƙarfe takwas da minti arba’in da bakwai, sun yi magana ta tsawon mintuna ashirin da huɗu, lallai cikin lokacin ya faɗa mata abinda ya faru, a tunanina ita ta sanar da Hajiya Sabuwa, tabbas hasashena zai iya zama gaskiya, idan kuwa haka ne an bar baya da ƙura.” Habib ya faɗa kana ya yi shiru yana ta ƙoƙarin tuna ko wa ce ce Maryam a zuri’ar su Suraj.

“Maryam, wa ce ce kuma Maryam?” Zinatu ta faɗa a fili da zuciyarta.

*****
Har Maryam ta koma gida hankalinta bai kwanta ba, lokacin da ta iso ƙofar gidan su ƙarfe tara da rabi har da mintuna.

Ta tarar da ƙofar kamar yadda ta bar ta lokacin da za ta tafi a kare, a hankali ta tura ƙyauren ya buɗe sannan ta sa kai cikin tsakar gidan, Hasken fitilar lantar ki ya haska mata mahaifiyarta da ke kwance a inda ta bar ta tana ta sharar barci abinta.

Kai tsaye ɗakinta ta zar ce, ta cicciɓo katifar ta ta dawo tsakar gidan ta shimfiɗa kusa da ta Umman, sai da ta je ta kullo gidan sannan ta dawo ta kwanta, ita kan ta tasan ba lallai ta iya barci ba.

Zuciyar ta sai kai kawo take a kan halin da Suraj yake ciki, tabbas ƙarar da ta ji ya yi a lokacin da suke waya ɗazu da kuma irin yadda ta ji ya ɗauke wuta lokaci guda suna cikin magana kafin ƙarar ta biyo baya, hakan yana nufin wani mummunan abu ya faru da shi.

Ta gyara kwanciya a kan katifar, Wannan wace irin rayuwa ce? Ku riƙa neman sai kun haye kan dukiyar mutum lokaci guda, ba ku da gadonsa, kawai saboda tsabar son zuciya da burin tara abin duniya da yin arziƙi ko ta halin ƙaƙa, har ku riƙa neman salwantar da rayukan bayin Allah da ba su ji ba, ba su gani ba.

Maryam ta share hawayen da suka fara ɓulɓuowa daga idaniyarta, ita mutum ce mai saurin bayyana rauni, abu ƙalilan ke taɓa mata zuciya, a lokaci guda ta ji wani tausayin halin da Mashkur da mahaifinsa suke ciki ya ƙara kama ta.

Kamar yadda ta yi tsammani kuwa a daren ranar sam ba ta iya yin barci ba har zuwa wayewar gari, Umman tana lura da yadda take cikin damuwa, da ta tambaye ta sai ta ce da ita wata ƙawar su ce a ka yi mata waya ta rasu, don babu yadda za ayi ta gaya mata halin da ake ciki, musamman da ta san cewa; ko kaɗan Umman ba ta ƙaunar alaƙarta da Suraj, ba don komai ba sai irin halaiyar da yake da ita a lokacin baya, bata iya manta halin rashin ɗa’arsa, don haka muddin ta ji batun nasa ne babu abinda zai hana ta yi mata gugar zana.

Da za ta tafi makaranta ne ta biya ta gidan, har lokacin ƙofar gidan a kulle take kamar daren jiya, wannan ya tabbatar mata har yanzu Hajiya Sabuwa tana can ba ta dawo ba, ko me ya faru? Allah ne masani, ta share ƙwallar da ke ƙoƙarin zubo mata duk a lokaci guda ta sauke jakarta da ke rataye a kafaɗa ta ɗauko wayar ta a ciki.

*****
“A cikin wayar Suraj suka samu duk wasu muhimman abubuwa da suka shafi Maryam, ta haka suka san ko wacece ita da matsayinta a rayuwarsa.

Me ya kamata a yi yanzu Habib?” Zinatu ta tambaya cikin rashin sanin madafar su.
Maimakon Habib ya bata amsa sai ya ɗauke idonsa daga kanta zuwa sashen da Cika Aiki yake, wata alama ce da ke tabbatar da ya samu amsar tambayoyinta.

Cika Aiki yana sanye da wata riga mai yankakken hannu da ta bayyana murɗaɗɗen hannunsa, idan ka dubi ƙwanjinsa kai tsaye zai tuna maka da ɗan wrestiling a filin daga, wandon da ke jikinsa three quater ne, a kwai aljihuna da yawa a jikin wandon sannan ga wata sarƙa da ke reto a jikinsa, kansa a kwai hula hana sallah. Baƙi ne sosai, yana da ƙasumba mai ban tsoro a kan mummunar fuskarsa.

Habib ya ajiye wayar Suraj a kan teburin robar da ke gaban su sannan ya gyara zaman hular zanna dake kansa.

“Nawa ne ma jimillar kuɗin aikinka?”
Cika Aiki ya gyara zama, “Ran ka ya daɗe maganar kuɗin aikin farko kawai muka yi naira dubu ɗari da hamsin, ka bada dubu dari ka ce zaka cika dubu hamsin sannan daga baya ka sa a ka cikawa tsohuwar nan aiki ba tare da mun yi ciniki ba ko?”

Habib ya ƙara gyara zama sosai sannan sai ya sunkuya ƙasa ya ɗauko wata baƙar leda daga cikin jakar da ya zo wajen da ita, ya ɗora a saman tebur ɗin haɗi da tura ta gaban Cika Aiki.

“Cika Aiki ya sa hannu ya ƙara janye kuɗin gabansa ya ɗauka yana jujjuya sannan ya tura su cikin aljihun wandonsa ya kuma kasa kunne don sauraren abin da Habib zai faɗa don ya fahimci inda karatun ya sa gaba.”

“Ina fatan kana aiki a wajen garin nan?” Habib ya buƙata yana dubansa, shi kansa ya faɗi haka ne don ya ji ta bakinsa, amma ya jima da sanin ko waye Cika Aiki.

“Ranka ya daɗe ai har ƙasa nake haurawa idan ta kama matuƙar za a yi min gwaggwaɓan biya, ya danganta da yanayin wahalar aiki.”

Habib ya kaɗan muskuta sannan ya ce, “Wannan kuɗin da na ba ka naira dubu ɗari da hamsin ne, idan ka hada da waɗancan na baya ya kama dubu ɗari biyu da hamsin kenan, gaba ɗaya aikin muna so ka yi mana shi a kan naira dubu ɗari uku da hamsin, ina nufin har wannan da za a gudanar daga yau zuwa gobe.”

“Cika Aiki ya lashi busassun leɓɓansa da suka dafe saboda shan sigari sannan lokaci guda ya juya rumfar hular da ke kansa zuwa baya ya ce, “Ranka ya daɗe ita ma waccan yarinyar za a gama da ita kenan?”

Kafin ya bashi amsa Zinatu da ke gefe tana duban duk abinda yake faruwa cike da gamsuwa ta ce, “Tambayarka ba ta buƙatar amsa Cika Aiki, zamu ba ka hotonta tare da adireshin gidan su a can Zaria, sannan tana karatu a jami’ar A.B.U duk a can Zaria, ba ta da gatan komai, mahaifinta tsohon kukun sojoji ne, ya rasu tun da jimawa, a yanzu tana zaune tare da mahaifiyarta da ke kasuwancin sayar da kayan adon mata da suka haɗa da sarƙoƙi, ‘yan kunne, da sauran su, don haka ne ma ba ta fiye zama a gida ba, Maryam ta fi zama ita kaɗai a gidan su wannan ma wata dama ce, ina ganin shima wannan aikin mai sauƙi ne kamar sauran.

“Kwarai kuwa nima haka na ke tunani.” Habib ya faɗa cike da ƙoƙarin gamsar da shi lokaci guda yana duban fuskarsa.”

“Babu damuwa Hajiya, ya za a yi wajen karɓar hoton ita yarinyar? don a yau nake son wucewa Zaria.”

“Kar ka damu, da zarar mun koma gida na ɗauko shi zan kira sai mu haɗu in baka.” In ji Habib.

Shikenan Ranka ya daɗe sai na ji ka.” Cewar Cika Aiki sa’ar da ya miƙe tsaye.

Zinatu ta bi shi da kallo, “Yauwa dama ina son sanar da kai wani abu, ina ganin ya kamata ka samu account domin tura maka ragowar kuɗaɗenka ba sai mun riƙa fama fa tsabar kuɗi a hannu ba, zamani ya sauya, yana da kyau kai ma ka sauya.”

Cika Aiki ya saki wani busashshen murmushi kana ya ce, “Ba damuwa Hajiya zan yi hakan ko don saboda tsaro.”

Yana rufe baki wayar Suraj da ke ajiye saman teburin ta fara ruri alamar kira ya shigo, lokaci guda dukkannin su suka kai idanu gare ta.

Maryam ce ta kira.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 1 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Kudi Ko Rai 7

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×