Skip to content
Part 14 of 43 in the Series Kuskuren Waye? by Aisha Abdullahi Yabo

kasa tayi da idanunta ta na faɗin “kayi haƙuri ni ba hakan na ke nufi ba” komai bai ce da ita ba ya tashi ya fita ɗakin maganar ta susa masa rai. Miƙewa ta yi ta na safa da marwa da zancan zuci ‘tabbas dawowar Zarah garin nan da wata manufa a ka yi shi’ ta koma ta zauna gefen kujera ta yi tagumi “koma meye wallahi ba ta isa ta shi go gidan nan a matsayin matar Hafiz ba dan ya mata nisa domin ni kaɗai a ka yi shi” ta kwanta tare da jan bargo ta lulluɓe rabin jikinta sai juye ta ke karon farko tun bayan auren su da su ka raba shimfiɗa  ranar sai bacci ɓarawo ne ya yi awon gaba da ita.

*****
Da safe bayan sun gama karin kumallo Dady ya kalleta ya na faɗin “Mamana ki shirya Hafiz zai zo ya ɗauke ki ku tafi makaranta a yi duk abin da ya dace dan ki samu ki fara zuwa cikin lokaci.”

“Me yasa sai Hafiz ne zai kai ta aikin na sa kuma fa?” Momy ta yi tambayar ta na kallon shi. Tashi ya yi daga kan kujerar ya fara tafiya sannan da ga bisani ya ce. “kin ji me na ce ko Mamana?”

“Eh zan shirya kafin ya zo In Sha Allah” ta yi maganar jiki a sanyaye har ga Allah ba ta so fitar nan da Yaya Hafiz ba ba ta son duk wani abun da zai din ga haɗa su bare har abin da a koyaushe ta ke ƙoƙarin binnewa a zuciyarta ta gagara ci gaba da juriyar binne shi. Momy ta harareta tare da tashi tsaye tabi bayan Dady da ya nufi ɗakin shi. Khadija ta na kaɗa shayen da ta gama haɗawa ta kalleta ta na faɗin “wai ni kam na tambaye ki mana.”
“ina saurarenki.”

“Kaf ƙauyen ku kin rasa mashinshini ne da na ga Dady na ta ƙoƙarin sai ya cusa wa Yaya Hafiz ke ne?”

Murmushi kawai ta yi ta ci gaba da cin soyayyen dankali wanda a zahiri ba wai daɗin cin nasa ta ke ba kawai ta na cusa shi ne saboda ba ta so ta ba da wata ƙofar da zai sa Khadija ta fahimci ɓacin ranta a kan maganar da ta faɗa.

“ya ki ka yi shiru, babu kenan. Kin yi kwantai ne?” 
“Khadija kenan duk yadda ki ka ɗauka a je a hakan kawai” ta ci gaba da cusa abincin. Khadija ta kalleta har ranta ta ji haushi so ta yi ta biye mata ita kuma ta yi mata wankin babban bargo amma banza ko a fuska ba ta nuna ta ji haushi ba, ta yi maganar a ranta tare da ture shayen gefe ta tashi ta na tsaki tabar wajan. Zahra ta bi ta da idanu ta na mai gyaɗa kanta ita ma tashi ta yi ta koma ɗaki.

*****

Dady ya na saka babbar riga Momy da ta ke tsaye gefen sa ta ce.  “ka na fa ji ina magana ka yi mini banza kamar ina magana da icce.”

Ya ƙarasa sa ka rigar ya juyo ya na kallon ta “me ki ke so na ce ne Turai? Hafiz da Zhara duk abu ɗaya ne a wajena shi ɗin kuma na ga damar na sa ya kai  ta makaranta dan na isa da shi. To dan me za ki titsiye ni da tambayar dan me zan ce sai shi me ki ke so to na ce ma ki?”

“Ni gaskiya dai ka ne mi wanin dai ya kaita dan ban ga dalilin da zai sa ka ce sai shi ne zai kaita ba. Ni ba na buƙatar  wata a laƙa a tsakanin su.” wani kallo ya ke yi mata mai ciki da mamaki “ba kya buƙatar  wata alaƙa a tsakanin su ki ka ce?” ta na gyaɗa kai ta ce. “Eh hakan na ce.”

“Lallai notin kanki ya fara kwancewa. Kin kuma manta da dukan su su waye a junansu,  to bari na tuna ma ki  jinin da ya ke yawo a jikin Hafiz shi ne ya ke yawo a jikin Zhara domin tsantso ɗaya su ka fito.

Sannan ki kwantar da hankalin ki ko maza sun ƙare a duniyar nan Zhara ta yi wa Hafiz nisa ba za ta taɓa auren sa ba. In har wannan ne damuwar ki to kisa  ranki a inuwa.” Ya ɗauki holarsa ya bi ta gefenta ya nufi hanyar fita ɗakin ta bi shi da kallo har ya zura takalmi a kafafunsa ya fita.

“Hum! Wai Zhara ce ta fi ƙarfin sa faɗa dai ka ke wace ita sai dai ya fi ƙarfinta wallahi.” Ta fita ɗakin a zuciye.

Zhara ta kamalla shirinta ta na kwance ta na sauraren karatun alƙur’ani a wayarta ta na bin karatun Kande ta shigo ɗakin ta zauna gefen ta ta na faɗin “Maman masu gida wai ina za ku ta fi ne da Yallaɓai ƙarami” tsayar da karatun ta yi tare da tashi zaune cikin faɗuwar gaba ta ce. “har ya zo ne?”

“A’a bai zo ba ina gyara wa Hajiya farce ne na ji ta na waya da shi wai kar ya kuskura ya zo ɗaukar ki shi kaɗai ya zo da matarsa ku tafi tare dan ita ba ta son keɓancewar ku ku biyu dan ba ta san da wani munafuncin ki ka zo ba.”

Dariya kawai Zhara ta yi ta koma ta kwanta. “Makaranta zai kai ni shi ne ta ke wani tunanin daban wanda ba zai taɓa faruwa ba.”

“Me ta ke tunani kenan?”

“Manta da zancen nan kawai.” ta kunna karatun ta ta ci gaba da yi Kande ba ta sa ke cewa da ita komai ba ta fara linkin kayanta da ta wanke wanda su ke a jiye a kan kujera.

*****

Halima ta shigo falon bakin ta ɗauki da sallama Momy ta ragi sautin tv ta amsa mata cikin fara’a “maraba sannun ku da zuwa” ƙarasawa ta yi gaban Momy ta durƙusa har ƙasa “ina kwana.”

 “Lafiya lau Halima fatan kun tashi lafiya.”

“Lafiya lau”

“Madallah tashi ki zauna” zama ta yi a kan kujera ɗan nisa da Momy ta na faɗin “ina Khadija ko ba ta tashi bacci ba ne?”

“Khadija ai har ta fita makaranta tun ɗazun” Hafiz ya shigo zama ya yi kusa da Momy ya na faɗin “Allah dai yasa ta shirya?”

“Oho wa ya sanan mata” Kande ta fito za ta shiga kichen “yawwa Kande ji ki kira yarinyar can”
“To Hajiya” ta amsa tare da juyawa zuwa ɗakinta. Kallon Momy ya ke da mamaki ya ce. “me ta ke yi sashin mai aiki?”

“Saboda ita ma ba ta da banbanci da ‘yar aikin shi yasa a ka sauketa a can ɗin.”

“Haba Momy ita ma fa ‘yar gidan nan ce kamar Khadija. Sam hakan bai dace ba.”
“to ai sai ka zo ka dake ni ta yadda zan fi fahimtar bai dace ba ɗin!” shiru ya yi bai sake cewa komai ba duk sai ya ji ransa ya ɓace  sam ba ya jin daɗin wanan abin da Momy ta ke yi wa Zhara. Sai a lokacin Halima ta ɗan ji natsuwa ta saukar mata ko ba komai ta na da tabbacin Momy ba ta son Zhara dan haka ba za ta taɓa barin auren  su ya yu ba. Wannan tunanin da ta yi ya ƙara kwantar mata da hankali.

Zhara shigowa ta yi falon ta na sanye da Hijab har ƙasa irin na zamanin nan da a ke ya yi. Ta na ƙyallo Halima ta je da sauri ta rungume ta “yaushe ki ka shigo?”

“Shigowar mu kenan. A she kin shigo gari sai jiya ai na ke jin labarin zuwan ki” ta yi maganar ta na ƙoƙarin janye ta da ga jikinta fuskarta kuma babu yabo babu fallasa. “ai kuwa dai na shigo, wayar ki ce ko an kira ba a samun ki. Su Mama duk su na gaishe ki.”

“Ina amsa wa” Zhara ta kai dubanta wajan da Hafiz ya ke zaune “Ina kwana Yaya Hafiz?”

“Lafiya lau Zhara fatan kin tashi lafiya?”

“Lafiya lau”

“Kin yi wuyar ga ni tun zuwan ki ba mu haɗu ba.” Murmushi kawai ta yi duk sai ta sha jinin jikinta ganin yadda Halima ta yi kinikinin da rai. Tashi ya yi tsaye “mu ta fi ko lokaci na tafiya ga shi ina so na shiga asibiti cikin lokaci.” tashi ta yi ta na faɗin “mun tafi Momy” harararta ta yi ta mayar da kallon ta kan Halima ta na faɗin “ki dai kula dan kin san yanzu babu aminci.”

“In sha Allah Momy” ta faɗa tare da miƙewa tsaye Hafiz tu ni ya fita.

*****

Zhara da ta ke zaune baya ta ce. “wai me ya samu wayar ki idan an kira ba ta shi ga?”

“A gida na barta sai bayan na zo ne na tuna da ita. Sai dai baby ya saya mini wata” ta yi maganar ta na kwanto da kanta  kafaɗar Hafiz. Kawar da kanta Zhara ta yi da ga kansu ta ɗauki wayarta ta kunna karatu tare da sa abin sautin a kunnenta. Da ga nan babu wanda ya sake cewa da wani uffan.

Bayan sun kammala da makaranta ya nufi hanyar gidan sa, kallon sa ta yi da Mamaki ta ce. “Baby ya na ga ka na yin hanyar gida?”

“Zan a jiye ku ne a gida na wuce asibiti.”

“Na ɗauka ai za ka fara a jiye wannan ɗin a gida” ya ɗan kalleta kafin ya mayar da dubansa ga hanya ya na faɗin “jira na a ke idan na tashi zan mayar da ita. Zhara zan a jiye ku gida idan na fito wajan aiki zan zo sai na mayar da ke kin ji ko” ba dan ranta ya so ba ta amsa da to. Halima ta yi kinikinin da rai ita fa sam ba ta wani son takura wallahi.

Ya na a jiye su ya juya da mota ya fita. Tun da su ka shi ga gidan ta yi shigewarta uwar ɗaki tabar Zhara falo. Mamakin sauyawar Halima ya cika wa Zhara zuciya ‘ikon Allah lallai mutum ka gan shi kawai wai Halima ce ta ke yin ko oho da ni kamar wacce ba ta taɓa ga ni ba’ ta yi maganar a zuciyarta ta na jinjina lamarin. Ta ga ji da zaman ta kwanta a kan kujera har bacci ya ɗauke ta.  Ana sallah azahar ya dawo gidan ya samu ta na bacci kallon ta ya ke a ransa ya na faɗin wannan ko matar liman albarka baccin ma da hijab a ke yinsa. “Zhara, Zhara” buɗe idanunta ta yi ta ɗora su a kansa “na’am Yaya” ta amsa masa cikin muryar bacci “kin kuwa yi sallah?”

Tashi ta yi ta na hamma ta ce. “A’a ai ban san lokacin sallah ya yi ba” tashi tsaye ta yi ta na gyara zaman hijab ɗin ta “ina banɗaki”

“Ki shi ga ɗakin Halima ki yi sallah a can idan kin idar sai mu tafi.”

Ya wuce zuwa ɗakin shi ta shi ga ɗakin da ta ga Halima ta shi ga ta samu ta na kwance a kan gado ta na dannar waya. “ina ne banɗaki zan yi alwala ne” Halima ta ɗago ta kalleta fuska babu annuri ta nuna mata da hannu ta.

Bayan ta yi alwala ya dawo falo ta cire kallabin kanta ta shimfiɗa ta fara sallah Hafiz ya fito kallon ta ya yi kawai ya shiga ɗakin Halima ta na ganinsa ta ta ta sauko da ga kan gadon ta rungume shi “har ka dawo” janye ta ya yi da ga jikin sa “ina dardumomin gidan nan ne da Zhara ta ke yin sallah a kan kallabin ta?” 

“Ganin damarta ne tun da ba ta tambaya na hana ta ba” gyaɗa kansa kawai ya yi kafin daga bisani ya ce. “mu je ki ba ni abinci ina so na je na a jiye ta na koma asibiti dan ina da aiki.”

“Ka yi haƙuri ban san za ka dawo da wuri ba shi yasa ban girka komai ba. Amma bari na yi sauri ko taliya na dafa maka” kallon ta ya ke da matuƙar mamaki ya ce “kenan babu abin da ki ka ba Zhara ta ci?” komai ba ta ce da shi ba ta bi ta gefen sa za ta wuce ya janyo ta ta yi baya kamar za ta faɗi ta samu ta tsayu.

“Tambayar ki na ke me ki ka ba ta ta ci?”

“Ita ƙaramar yarinya ce da har sai na ba ta abincin da za ta ci ko kuma ‘yar aikin ta ce ni” ta yi maganar ranta a ɓaci. Kallon mamaki ya ke mata “me ya ke damun ki shin kin manta wace ce Zhara a wajan ki ne? Ko da ita ɗin ba ƙanwata ba ce ai ƙawar ki ce da ki ke faɗar amintar ku ta kai matakin da za ku kira juna da shaƙiƙai, amma gaba ɗaya kin sauya me yasa?” shiru ta yi tana turo baki. Gyaɗa kansa ya yi “hum ba ki da abin faɗa kenan. To bari ki ji wallahi ba zan ɗauki wannan shashancin ba, ba kuma zan lamunta da wulaƙanta mini ‘yar’uwa ba!” ya na gama faɗa ya fita ɗakin rai a ɓace. Tsaki ta yi tare da bin bayansa.

Ya samu ta idar da sallah “mu tafi ko?” ta na tashi tsaye Halima ta fito ta na faɗin “bari na ɗauko mayafina na rak… Kallon da ya watsa mata ne yasa ta kasa ƙarasa maganar ya yi gaba Zhara ta juyo ta na kallon ta ta ce. “sai anjima.”

“Na sa ni duk da da sahalewar ki aurena da Baby ya tabbata hakan ba ya na nufin kin daina son sa ba ne dan na fi kowa sanin irin son da ki ke masa wan da shi kansa bai sani ba. Wannan yasa na ga ya kamata na ba ki shawara kar ki taɓa sa wa a ran ki cewar za ki aure shi domin ina da tabbacin ko auren ki ya yi sai dai umurnin Dadyn sa kawai zai bi dan babu yadda zai yi, amma koyaushe ya na faɗa bai taɓa sonki ba ba kuma zai taɓa ba har abada.”

Idanunta su ka ciko da hawaye wai Halima ce ta ke yi mata hakan wanda ko a mafarki ba ta taɓa tunanin faruwar hakan ba bare kuma a zahiri. Ajiyar Zuciya ta yi tare da juya wa za ta fita “shawara ce fa na ba ki ki daina ba kan ki wahala da son maso wani da Hausawa suka ce ƙoshin wahala” juyowa ta yi ta kafeta da idanu.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 3 / 5. Rating: 4

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Kuskuren Waye? 13Kuskuren Waye? 15 >>

1 thought on “Kuskuren Waye 14”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×