Skip to content
Part 4 of 10 in the Series Ma'aurata by Aisha Abdullahi Yabo

Ɗakinsa ya shiga ya ajiye akan center table sannan ya cire kayan jikinsa ya faɗa toilet.

Tana ganin ya shiga ban d’aki ta yi murmushi tare da d’aukar abincin dama da shegeyar yunwa ta taso.

Zama tayi ta canye abincin tsaf ko kwara d’aya bata rage ba tana gamawa ta bud’e firij d’insa tasamu maltena d’aya ta kora sannan tabar d’akin ranta fes.

Yana gama shirinsa yaje zai karya yaga wayam ransa ya bala’in b’aci lallai yarinyar nan ta masifar raina shi. Dakinta ya nufa tana zaune tana chatin “Ruk’ayya awane dalilin zan ajiye abu ki d’auka?”

A yatsine ta kalle shi kafin tace, “Ban gane ba me na d’aukar ma?”

“Karki raina mun hankali abincin da na ajiye ad’aki ubanwa ya d’auka?”

“Au wai dama saboda abinci kake wannan hayagaga kamar kare.”

Cikin fito da idanu yace, “Ni kike kira da kare?”

“Ikon Allah nifa cewa fa nayi kamar kare, bakaji nace ma kare ba.”

“Yayi kyau Ruk’ayya kiyi duk abunda kikaga dama lokaci ne.”

Daga haka bai sake cewa da ita komai ba ya fita gidan gaba d’aya.

Ko a jikinta ta cigaba da chatting.

Fatima haka taje ta tsalkake jikinta zuciyarta na mata zafi ga zafin zazzab’i   darduma ta shimfid’a ta fuskanci gabas.

Habib ya fito wajan aiki ya tuna da tsohuwa Iya hakanan ya tsinci kansa da son zuwa gaisheta. Bayan yayi paking a k’ofar gidan yasamu wani yaro yace ya shiga yace ana sallama da Iya.

Bai jima ba sai gashi sun fito tare da yaron tana ganinsa ta washe baki “ah yaro d’an albarka ashe kaine shigo daga ciki.”

Bin bayanta yayi yana murmushi d’akinta ta kaishi ta shimfid’a masa darduma bayan ya zauna yace, “Iya ina wuni?” “Lafiya k’alau yaron kirki ashe zaka dawo?”

“Wallahi kuwa Allah ya nufa, yasu Baba?”

“Lafiya k’alau yana kasuwa bai dawo ba.”

Kwanun fura ta janyo ta ajiye gabansa “ga fura d’azun Maryam ta damamun ita”.

“Anya Iya na shanye maki fura.”

“Kai meye to a ciki ai rashin shan nata ba zai mun dad’i ba.”

Bud’e kwanun yayi yana “to Iya nagode dama kuwa fura mutuniya ta ce ina sonta sosai.”

Sosai yasha furar sun d’an tab’a fira kafin daga bisani yayi mata sallama tare da bata dubu biyu.

Da k’yar ta karb’a tana ta godiya har mota ta raka shi dai dai lokacin wata budurwa mai matsakaicin kyau ta fito acikin adaidaita.

“Yawwa kaga jikanyata nan Ku gaisa ke Maryama zo ku gaisa da yaron da nake baki labari.”

Cikin sakin fuska ta k’araso wajansu.

“Ina wuni” “lafiya k’alau shine ranar ki kasa tsohowar mutane tasha dukan ruwa?”

Murmushi tayi kafin tace, “Ta dai sa kanta ai ni ba yarinya bace da zata fita nemana ba.”

“Kaji ja’ira ko ni kawai nadamu da ita.”

Dariya yayi kafin yace “ah lallai naga alama Iya to nikam zan tafi sai wani lokacin kuma.”

“To muna godiya fa a gaida gida.” Cewar Maryama.

Yau kam anyi sa’a bai shigo buge ba sai dai fuskar nan ba annuri sai da yayi wanka sannan yazo danin dan cin abinci yaga wayam ba komai.

A fusace ya nufi d’akinta tana dunkk’ule kan gado cikin bargo yana zuwa yakai mata shuri k’iris ya rage ta kai k’asa Allah ya taimaketa ta rik’e kan gado.

“Ke dan uwarki mai d’an wake ina abinci na?”

Cikin muryar marar lafiya tace “kayi hak’uri wallahi banda lafiya shiyasa ban girka ba.”

“Lallai yarinyar kin raina ubanki to ba ciyo ba ko asibiti ce sai kin girka mun abinci kuma tuwon shinkafa miyar alayyahu nake so kuma karki kuskura ki b’ata mun lokaci”.

“To amma babu alayyahu da gushi”

kud’i ya jehu mata “ungo ‘yar matsiyata Allah bai had’amu da babu ba sai dai a gidan ubanki lagwani” ya fita d’akin yana tsaki.

Haka ta fito jiki ba k’wari Allah ya kad’o almajiri gidan yana bara takira shi ta bashi aikin yayo mata cefane. 

Cikin d’an k’ank’anin lokaci ta gama masa abincin duk da tana aikin tana hutawa. Ko da tashiga d’akin sa yana waya sai da yagama sannan ta shaida masa tagama.

“OK kawo mun nan saura na ci na ji shi d’anye kici ubanki” (kai ina aka tab’a tuwon shinkafa danye in banda neman rigima).

Bayan ta kawo masa yace “ki k’aro plate.”

Zata bud’e k’ofa taji an turo k’ofar wata budurwa ce ta shigo d’akin shigarta kad’ai zata tabbatar ma ba musulma bace.

Wani kallon banza ta watsowa Fatima. Fatima bata ko san tana yi ba dan tana shigowa ta fita d’akin. Ko da ta dawo kawu plet tana zaune akansa suna shashanci ba kyan gani kallo d’aya tamasu ta kauda kanta. Abincin ta zuba masu sanan ta mik’e zata bar d’akin ya daka mata tsawa.

“Ke dan uwarki na sallame ki ne? tun da tsayen kike so yi tsaye agurin har sai na sallame ki.”

“Dan Allah kayi hak’uri wallahi jiri nakeji bazan iya jure tsayuwa ba.”

Bata ga tasuwar sa ba sai saukar mari taji “wato kin raina ni koh? to kinjawa kanki anan zaki ta tsayuwa har safe banza ‘yar matsiyata.”

Bayan ya zauna mary ta shafa sajen fuskarsa “baby kana burgeni da baka d’aukar raini shegiyar yarinyar nan da taga fuska ba k’aramin iskanci zata yi ba kasan talaka bai iya samun waje ba.”

“Ni nasan talaka ga naci ubanta fa maula yake zuwa gurin Dady.”

“Hhhhh kace sadakar yalla aka baka ita.”

“Kamar kin sani ba sisin kwabona aciki.”

Hawaye ne keta zarya a fuskarta komai takasa cewa dasu.

Suna gama cin abinci sukayi brush aka fad’a kan gado suka fara bad’ala da sauri ta kawar da kanta gefe. Jin anyi kiran sallah la’asar tayi hamdala aranta ta juya zata wuce yace “ke nace ki tafi ne?”

“Lokacin sallah naga yayi.”

“Dawo ki tsaya.”

“Kayi hak’uri ba biyayya ga abokin halitta akan  sab’awa ubangiji. Bazan zauna ina kallon abunda yake sab’on ubangiji ba na bar ibadana ba.” Tana gama fad’a tai wucewarta zai bita Mary tahana, “Please Baby shareta tana so kawai tahanamu farin cikinmu ne.”

Da wannan ya kyaleta amma ya k’udurta aransa sai ya koya mata hankali.

Ranar kam Habib tunanin Maryama bai barshi ya samu baccin kirki ba yana cikin wannan yanayin Ruk’ayya ta shigo d’akin cikin kayan bacci   “lafiya zaki shigo mun d’aki cikin darenan?”

Zama tayi kusa dashi tare da rik’o tana wasa da yatsun  sa tace  “wallahi Habib akwaika da abun dariya dan nazo d’akin  mijina sai ace me ya kawoni? to shikenan nazo gun mijina ko nayi laifi?”

“Uhm Aa idan anzo dan Allah ba” ya cire hannunta daga nashi ya kwanta tare da juya mata baya.

Shiru tayi tana tunanin yanda zatayi,  murmushi tayi  tuno mafitar da tayi, kwanciya tayi bayansa ta rungumeshi tun yana share abun da take masa hardai ya kasa yabiye mata  sai da  taga ta kamashi awuya sannan ta janye jikinta.

Cikin wani irin yanayi yace “miye haka Ruk’ayya?”

Cikin ko oho tace “me nayi idan kana buk’ata kabiya mun nawa buk’atan sai na biya ma taka.”

“Haba Ruk’ayya wannan abu da kike fa haramun ne meyasa zaki dinga tauye mun hakk’i?”

“Mtsw kai kana da matsala Habib kawai fa ihasani ne bana ce wai biyana zakayi ba”.

Cikin b’acin rai yace “naji dan Allah tashi  ki fice min d’aki.”

“Am… sauri katseta yayi “nace ki fitar mun d’aki ko ranki ya b’aci!”

Tashi tayi tabar d’akin tana masifa komawa yayi ya kwanta  kamar yayi kuka dole ne ma ya k’ara aure yagaji da halin Ruk’ayya.

Ku biyo ni a babi na biyar in shaa Allah.

Ta ku Aisha A. Yabo (Fulani)

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 2

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Ma’aurata 3Ma’aurata 5 >>

1 thought on “Ma’aurata 4”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×