Skip to content
Part 18 of 28 in the Series Mai Daki by Hafsat C. Sodangi

Komawar Zubairu Makaranta sai abubuwwa suka sake rincabewa. Ashe dama sun bari ne don sun gane yana kai kararsu wurin Babansu.

To yanzu ba ya nan sun ci gaba daga inda suka tsaya. Sai dai Ziradat ta riga ta tsorata saboda dukan da Baban ya yi mata a kaina.

Zainab ce take nuna mun salo iri-iri na rashin kunya da kuma nuna isa, amma na danne zuciyata ko kallon iya-shegenta bana yi.

A daidai nan ne kuma wani sabon laulayin ya kama ni, watanni uku bayan barin da nayi.

Amma a hakan na tsaya tsayin daka wajen ganin na gamsar da mijina duk wata lalura tashi.

Kullum nayi mishi maganar zuwa gida sai ya yi mirsisi ya hana ni, ya ce ba na yi mishi adalci da yana gari amma sai na tsallake hidimominshi na tafi gidanmu.

Na ce, To ai kai da rana kana kasuwa, da daddare ne ka ke dawowa gida ka bar ni mana naje da rana na dawo kafin lokacin dawowarka gida?

Sai ya ce, Wai a’a yafi son idan ya tuna ni a lokacin da yake kasuwa ya rinka tuna ni a cikin gidan shi ina harkokina.

Kallon Ahmad kawai nayi nayi murmushin takaici, amma a raina tunda ba ni da abin yi a kai, ba na musu dashi koda kuwa hukuncin da ya yanke bai yi mun dadi ba.

Hakanne yasa da yazo tafiya Kano gaida kanin Babanshi da ya yi rashin lafiya, tafiyar kwana daya sai na tuna mishi da zuwana gida.

Ya ce, Ba ki fa da lafiya Hauwa’u. Na dakatar da hada mishi kayan da nake yi, na ce “Haba yallabai, ba haka muka yi da kai ba fa.”

Ya ce, “Eh na sani, amma ai wannan karon tafiyar tawa ba mai jimawa ba ce, kwana daya zan yi.”

Na ce, To ni ai tawa tafiyar wuni ce. Shiru yayi sai da ya fita wurin Hajiya ya dawo sannan ya ce naje gidan yau Bala zai kai ni.”

Nayi tsalle don murna ya ce, “To kin gani ba. Nayi-nayi da ke ki rinka kula da irin wadannan abubuwan kin ki kanmar kin mance da abinda ya same ki wancan karon.”

Ahmad yana tafiya nayi shirina tsaf na rufe sashena na fito na shiga wurin Hajiya don nayi mata sallama.

Sannan na fito harabar gidan na samu Bala har ya yi warming din mota ni yake jira.

Sai kawai ga Zainab da Ziradat sun fito su ma za su je unguwa. Kai tsaye suka nufi motar za su shiga.

Bala ya ce, “A’a Zainab kada ki shiga motar nan, Hajiya zan kai unguwa a ciki.”

Tayi mishi wani wawan kallo. Akwai wata Hajiya ne a gidan nan baya ga wacce dama can na sani? Ina tsaye a gefe ina kallonsu ban tanka ba.

Ita dai Ziradat ta dan nutsu duk da dai nasan ba wani hankali ta kara ba.

Zainab ce da Bala direba suke ta jayayya ya shiga mota ya tuka ya ki, ita kuma ta fita a motar ta ki.

Ziradat fita kije ki kira mun Hajiya. Ba a wani jima ba sai ga

Hajiya ta iso wurin cikin hijabinta.

“Lafiya?” Ta kalli Bala direba. Nan da nan ya fara yi mata bayanin abinda ke faruwa.

Hajiya ta kalli Zainab ta ce, “To ke Zainaba ku shiga mana idan aka sauke ta a gidansu sai a kai ku taku unguwar ba shi kenan ba.”

Nan take ta fashe da kuka ita gaskiya ba za ta shiga mota da ni ba, bayan ba sonsu nake yi ba.

Na kalli Bala na ce, “Bala idan ka kai su ka dawo kayi mun magana.

Ya ce,”To Hajiya. Na dawo na shiga dakina na zauna. Ban san yadda zan yi da yarannan ba, abinda na sani shi ne bana kin su.

Na zauna kato-kato ina jiran Bala yadawo da su Zainab mu tafi bai dawo gidan ba sai wajen karfe hudu da rabi.  Har sashena ya iso yayi sallama, na

ce “Kun dawo Bala? Ya ce, “Eh Hajiya kiyi hakuri zai fara yi mun bayani na ce a’a Bala babu komai je ka kawai.”

Ya tsaya zai ci gaba da ba ni hakuri, na ce ba fushi nayi ba Bala, amma kaga gidanmu zan je yanzu kuma yamma ta riga tayı, ya ce to Hajiya na gode.

Washegari ba ni da halin fita tunda Ahmad zai dawo gida a ranar, don haka tashi nayi don nayi mishi shiri.

Da aikin wurinshi na fara. Na wanke bayan-gida, nayi shara ko ina fes sannan na canza labilayen dakin gaba daya na zuba wasu na kira mai wanki na ba shi.

Na sake shimfida ko ina ya yi kal, sai kamshi kawai. Na dawo sashena na shirya mishi abinci na yi mishi fruit salad sannan na shiga bandaki nayi wanka nayi kintsi na sosai.

Nayi kwalliya mai kyau ta riga da siket, ina gamawa ko sai ga isowar motarshi cikin gidan.

Sai da ya shiga wurin Hajiya kamar yadda ka’idar shi yake, sannan ya shigo wurina da gudu na isa inda yake na rungume shi ina mishi oyoyo.

Yana dariya ya ce, Anya Hauwa’u ce kuwa ba canje aka yi mun ba da ba na nan?

Na ce, Canje kuma ‘Yallabai? Ya ce, Eh mana naga ne sai wani danyacewa ki ke yi kina dawowa ‘yar karamar yarinya.

Sashen shi muka shiga don ya yi wanka, yana ganin irin gyaran da na yi wa wurin ya ce,  “Wow! Ke da waye ku ka yi wannan aikin Hauwa’u?

Na ce, “Da waye ka ke tsammanin zan yi?” Ya dan yi shiru zuwa can ya dan kada kai ya ce, “Ke kadai ko?”

Na ce, Yauwa ashe ka gane kenan?

Ya ce, To Allah yayi miki albarka. Na wuce shi na shiga bandakin shi ina hada mishi ruwa da turarukan wanka.

Ya shiga ni kuma na fito na ciro mishi jallabiya ruwan kasa saboda sanin da nayi zai fita zuwa Masallaci idan anyi magriba.

Yana cin abinci ina zuba mishi yana ba ni labarin garinsu da mutanen garin.

Ya ce, “Sai kin haihu zamu je su ganki suga abin da muka samu. Ya ce kin ga ma na manta jiya da muka yi waya ban tambaye ki su Umma ba.

Na ce, Ai ma ban je ba. Ya kalle ni ya ce, Ba ki je ba kuma? Na ce, Eh. To saboda me? Nayi shiru ban ce mishi komai ba.

Ya ce, Ke dinnan fitanarki yawa ne da ita, da ban bar ki ba da har yanzu kina yi mun mitar na hana ki zuwa gida.

Ya fita sallar Magriba ya wuce wurin Hajiya, bai dawo ba sai da aka yi sallar Isha’i sannan ya shigo.

Tashi ki shirya muje gidan tare. Sannan ya wuce sashenshi. Ya dawo sanye da jamfa da wando na yadin material din maza yana rike da mukulln mota a hannunshi.

Ni ma yadin material na saka mai hadari ya kuma yi mun kyau sosai. Muka fito tare muka shiga wurin Hajiya don yi mata sallama.

Ta ce, lna zuwa haka a daren nan?

Ya ce, “Yar wata unguwa zata raka ni. Ta ce, To a dawo lafiya. Muka fito.

A wani babban shago ya tsaya ya yii siyayya mai yawa, sannan muka wuce gida.

Hira muke yi sosai da Umma shi kuwa yana wurin Babana ba mu dawo ba sai wajen karfe goma na dare.

Tashi nayi naga jini kadan-kadan yana fitar mun, sai dai ban kula na gani ba sai bayan da Ahmad ya tafi kasuwa.

Bana son daga mishi hankali, don haka nayi nufin bari sai ya dawo naayi mishi bayani.

Nayi ta aikace-aikacena ba tare da wani abu a raina ba, tunanina dai bai wuce laulayi irin na ciki ba.

Sai da na gama ayyukana na shiga bayan gida da nufin yin wanka, sai

kawai na ganni kace-kace cikin jini. Sauri nayi na fito na dauki waya na sanarwa Ahmad cewa ina son Zuwa asibiti, ya ce lafiya? Na ce ch, ba na dai jin dadi ne kawai, ya ce to Allah ya sauwake.

Bala ya kai ni asibiti sai dai tun kafin nan a takure nake cikin sauri aka kai ni dakin Likita sai dai gwajin farko ya tabbatar mana cikin ya lalace, ya fita daga mahaifa dole a cire.

Duk da halin da nake ciki a haka na daure na kira Ahmad.

Cikin kankanin lokaci ya iso asibitin, sai dai duk da saurin da ya yi har an shigar da ni don wanke mun mahaifa.

Duk da kokarin da nayi tayi na hana kaina kuka kasa daurewa nayi da Ahmad ya iso kaina.

Wannan karon ma bari nayi na ciki wata hudu har da sati biyu, kamar dai wancan kenan.

Kwana nayi a asibitin kowa kuma yazo duba ni har daga gidanmu. Likita ya shigo saboda sallama ta da za a yi Ahmad yana yi mishi wasu yan tambayoyi.

Ya ce, To dai a fayil dinta na ga ta samu matsala makamanciyar wannan shima a watanni hudu, don haka tunda ga abinda ka fada zamu sake yi mata scarming don mu gani ko da matsala.

Likitan ya jawo wata ‘yar takarda yayi rubutu ya bamu. Ahmad ne da kanshi ya kai ni wurin scarning din muka dawo Likita ya duba ya ce, “Toa gaskiya ta samu matsala ne a mahaifa saboda jijigar farat-daya da mahaifarta tayi a wancan karon.

Saboda irin faduwar da tayi, hakan ne yasa mahaifarta ba za ta iya rikke wani ciki da zai yi fiye da watanni hudu a mahaifarta ba.

Saboda bakin mahaifarta da ya riga ya bude. Kuma shawarar da zan ba ku a yanzu shi ne, kafin a san matakin da za a dauka a kan matsalar, ta dan yi hutu.

Don kuwa idan tayi wani cikin ma a yanzu abinda zai faru kenan.

Dawowa gida muka yi jikinmu a sanyaye, ni kam Ciwo ne ya rufe ni jinya sosai Ahmad kwata-kwata ranar bai fita kasuwa ba.

Bai kuma fadawa kowa abinda Likita ya ce ba. Kwana biyu ko abincin da zan ci daga wurin Hajiya ake kawo mun.

Kullum kuma Ahmad zai ba ni hakuri saboda lurar da yayi na dan saka damuwa a raina. Duk kokarin da nayi kada ya fahimci wani abu kasawa nayi. Yau ma yana zama zai fara mun magana kuka na kama yi.

Sai da nayi ya ishe ni sannan na share hawayena, babu abinda ke tsaya mun a rai naji zuciyata ta baci irin na tuna ‘ya’ yan Ahmad ne suka yi mun wannan sanadin.

To tambayar ita ce, shin idan da ni ce nayi wa wani a cikin su haka anya zan zauna lafiya kuwa?

Amma gashi nan ni sun yi mun sun zauna lafiya, sun ma mancc in ban da shi Ahmad da yake ba ni hakuri.

Duk da warkewan da nayi a duk lokacin da na tuna ina jin wani iri na kuma kasa sakewa nayi harkokina kamar da.

Ko shi Ahmad din ya lura ya gane hakan, don yau ma muna zaune a falonshi muna kallon labarai ya Juyo yana kallona.

Hauwa’u magana nake so nayi miki. Na lura duk tsawon lokacin nan har yanzu ba ki saki jikinki ba.

Na kuma tambaycki shekaran iya ko wani abu na damunki ne kin ce a’a, lafiyarki kalau.

Ina so ki san wannan abun ba ke kadai ya samu ba har da ni, amma kuma kin takura ni na rasa walwalar da a da nake farin cikin samu.

Idan ni ne nayi miki wani abu ki gaya mun na gyara, idan kuma a kan matsalar nan ne ina so kiyi hakuri.

Ina kokarin a wannan watan da zai kama idan zan yi tafiya mu tafi tare

saboda wannan matsalar, sai ki ga Likita a Dubai.”

Ban ce mishi komai ba, amma nayi kokari wajen ganin na rage takura ko don saboda Ahmad.

Sai dai har karshen wata yazo ya wuce Ahmad bai yi tafiyar ba, bai kuma ce mun komai ba.

Muna kwance a dakinshi da daddare a daren da ya dawo daga Legos dauko wasu kayan shi da suka shigo.

Nayi mishi maganar tafiyar da ya ce zamu yi don ganin Likita. Ya ce, “Kiyi hakuri Hauwa’u, ina nan ina wasu shirye-shirye ne kawai.”

Sai dai ba a wani jima ba ya shirya ya tafi Dubai ya dawo ba tare da ya ce mun komai ba.

Na shiga dakinshi na same shi zaune ya baje takardu, lissafi yake yi.

Na zauna a gefe ina jiranshi ya gama shiru bai gama ba har na gaji’ na mike na kwanta nayi barci.

Washegari tun da Asuba yayi shirin shi gaba daya alamar daga wurin

Hajiya zai wuce. Haka ina ji ina ganin babu yadda zan yi ya fita. Da daddare kuwa da ya dawo sai da na gama mishi komai sannan na kwashe kwanukan.

Wai kafin naje na dawo nayi mishi maganar da ke Cina a zuciyata nan ma dawowa nayi na samu wai Hajiya ta ira shi.

Zama nayi daram a kan kujera ina jiran shigowarshi, bai shigo ba sai

wajen karfe goma da kwata. Har yanzu ba ki yi bacci ba?” Na ce, “Eh kai nake jira.” Ya ce, “Akwai magana kenan? Na ce, “Eh.” Ya gyara ya kwanta ya ce, “To ki barta gobe kafin na fita kasuwa sai muyi.”

Na ce, Idan kuma a wurina tana da muhimmanci fa? Ya ce, “Komai muhimmancinta ki barta sai gobe, don a yanzu na gaji.”

Wani irin gululun bakin ciki ne ya tokare mun makogorona. Da kyar nake iya numfashi.

Tashi nayi na dawo dakina na hau gadona na kwanta. Sai dai ban iya yin barcin ba.

Ji nake yi kamar na koma na samu Ahmad muyi duk wacce zamu yi da shi daren nan amma ba zan iya ba.

Ko wani sauraron shi ban yi ba da safe haka nan shi ma bai bukaci ya ji maganar da nake son yi da shi ba.

Da dai ya gama shirinshi ne zai fita ya leko dakin. “Hauwa’u ina son burabusko da miyar bindi”.   Na ce, To babu tsakin shinkafa.” Ya ce, “Ki karba a wurin su Hajiya.” Ya tafi.

Babu abinda na tsana yanzu a rayuwata irin zuwa wajen su Hajiya. Tun da dai gaisheta ya zama mun dole, to kullum da safe ina zuwa amma baya ga haka bana komawa sai wata safiyar.

Sai da aka yi sallar Azahar sannan na dauki roba na shiga wurin Hajiyan na gaya mata ina son tsakin shinkafa.

Ta kalli Zainab ta ce, “Zainaba tashi ki debowa Mamanku tsakin shinkafa.”

Ta dago ido ta kalle ni, sannan ta ce, “Maman wasu dai Hajiya, ammna ban da mu.”

Ta ce, “To naji bana dai son rashin kunya, karbi ki debo mata. Kin dai kusa tafiya Makaranta a huta.”

Ta ce, “Ai idan na ganc tafiyata zai sa wasu murna ma sai na cc na fasa.”

Ta dawo da tsakin a hannunta ta dangwarar a kasa. Ban tsaya sauråronta ba, dauka nayi na yi tafiyata. Zainab a yanzu ta rubuta

jarrabawarta na gama makaranta secondary, Jami’a ake neman mata har ma an samu. Dawowa wajena nayi na shiga kokarin ganin na kammala cikin lokaci, kuma nayi sa’a yayi kyau ya yi dadi.

Ga kamshi ko ina a cikin gidan. Ina gamawa na shiga bandaki nayi wanka na fito kenan naj1 motsi a falona.

Don haka na fito falon bayan na sanya zulumbun hijabina don ganin

ko waye. Zainab ce rike da tircn abincin Babansu, gabaki dayan shi zata fita.

Sa hannu nayi na rike na ce “Yau kam a’a, abin ya ishe ni haka ba zai yiwu ba.

A duk ranar da ki ka ga kina da bukatar cin abincina to rinka gaya mun sai na rinka saka sanwa da ke. Ba haka kawai idan na gama girki ki saka hannu ki sunkuci na mijina kiyi gaba ki bar ni da dora sabo ba.”

Ta zuba mun ido tana kallona, nimna ita nake kallo, don na lura su gaba ki dayansu ba su san zuru ba.

Kuma a gaban kowa sai Zainab ta caccaba mun magana ba za a ce komai ba. Ba tun yau ba lokuta da dama sai na gama abinci sai tazo ta sunkuta gaba daya ta tafi da shi wurinsu ta ci iya cinta ta rabar da saura.

Wani lokacin ma ko rabi ba a ci sai ta bar shi haka ya lalace, sannan ba za ta dauko kwanukan ta dawo da shi ba sai dai ni nabi bayan su.

Sau daya Hajiya bata taba yin magana a kan hakan da take yi ba, duk da tasan abincin danta Zainab take dauka.

Kallon da take yi mun ne ya ishe ni nayi nufin karbe tiren, sai kawai yarinyar nan ta kabar da tiren gaba daya abubuwan ciki suka watse.

Abincin ya zube a kasa, sannan tayi murmushi ta raba ta gefena ta wuce. Zubawa abincin da ya tarwatse din ido nayi ba na ko kyaftawa.

Ban taba ganin danyen rashin mutunci irin wannan ba. Cikin dakina na koma na sanya doguwar riga na futo zuwa wurin Hajiya don na gaya mata abinda ke faruwa.

Na shigo na zauna a kasa zan fara magana sai ta ce “Dakata! Yau kuma abin naki har ya kai ma ki hana Zainaba abinci?

Ta dauko kuma kin biyo ta kin kifar. Me ki ke nufi da abinda ki ka yin? Kin taba siyo abinci kin shigo da shi gidan nan ne da ki ka samu damar hana wani?”

Na ce, “Hajiya..”.  “Bana son jin komai daga bakinki, nasha gaya miki ba sau daya ba ba sau biyu ba cewa duk abinda za ki yi a gidan nan to ya tsaya tsakaninki da wasu amma kada ki tsallako hurumina, don ba za ki ji da dadi ba.

Ya ya za ki hanata cin abincin da ubanta ya kawo ya ajiye takamar kina matarshi?” Tun ina daurewa bacin raina har ban san sanda na fara zazzago maganganu ba.

“Ai tun farko da nazo gidannan na fara kawo abinci sashen nan aka ce na daina don kuwa akwai mai girki. Me yasa tunda haka ne idan tana son abincina ba za ta fada mun tun da wuri ba sai na girka da ita, sai ta bari na gama tazo ta dauke gaba daya, haka ake yi?

Duk hakurin da nake yi da yarannnan bai isa ba kullum kokarinsu bai wuce na ganin sun kure ni ba.

Menene na yi musu?

Tunda na fara magana har na gama Hajiya bata sake cewa komai ba, sai kallona kawai da take yi.

Zuwa can ta ce, Lallai kin isa, ni ki ke gayawa irin wadannan maganganun? Dama ai biri ya yi

kama da mutum. Tun kwanakin baya na gane ya ba ki isasshen damar da ta wadace ki. To amma ba laifinki ba ne. Tashi ki ba ni wuri, bari yazo ya same ni mu san wacce muke ciki da nida shi.”

Mikewa nayi na dawo dakina na kara tsallake abincin a wurin na shiga uwar dakina na zauna.

Ni kaina na gane nayi kuskure amsawa Hajiya da nayi, to amma yaya zan yi da raina?

Rashin ‘yancin yayi yawa, ace wai har a kan budurwar yarinya mai shekara goma sha shidda kamar

Zainab za a zaunar da ni a titsiye ni wai nayi laifi! Kawai takamar ina auren ubanta bayan da za a bi Silsilar abin za a iya fahimtar ba ni ba ce mai laifin.

To amma saboda daurin gindi da son kai sai ya zama komai suka yi daidai ne. A madadin abubuwa su yaru kullum kara cabewa suke yi? Kamar yadda ya saba dawowa haka ya dawo yau ma. Ko inda yake ban je ba ballantana na ba shi wani abu. Don kuwa babu, na kuma san an gaya mishi komai da ya faru.

Karfe tara har ta wuce ina zaune a kan sallayata da nayi sallar Isha’i a kai ban tashi ba. Jiran kawai abinda zai biyo baya nake yi. Bai shigo dakin ba sai wajen karfe goma na dare.

Yadda nayi zaton zai shigo ba haka ya shigo mun ba. Ya karewa abincin da har yanzu yake shimfide a kasan falon da food flask din da kuma fasassun plates din kallo.

Ya sunkuya ya kwashe plates din da kofunan da suka faffashe ya zubar a abin zuba shara na nan kicin. Sannan ya fito ya dawo da abin kwashe shara da tsintsiya yasa ya kwashe ya gyara wurin tsaf, sannan ya wanke hannunshi ya zo ya zauna a inda nake muna fuskantar juna.

“Ba kya jin maganata Hauwa’u, ko nayi miki magana ba kya ji. me ya hada ki da Zainab?” Nan take na fashe da kuka saboda karayar da nayi. Nayi kukana sai da na gaji nayi shiru, sannan nayi mishi bayanin komai.

Tun daga lokacin da Zainab ta tsiro da abubuwanta har zuwa yau abinda ya faru. Ya yi shiru zuwa can ya ce, “Me yasa ba ki taba gaya mun ba? Na kalle shi.

“Na gaya maka fa ka ce? Idan na gaya maka me za ka yi? Na taba gaya maka wani abu da aka yi mun ka dauki mataki? Sannan ko karata aka kawo wurinka ko ni ce da gaskiya ko ba ni ba ce ba ka taba saurarona ka ji ta bangarena ba.

Ni dai a kullum ni ce maras gaskiya, ‘ya’yanka kuma masu gaskiya. A ina ne aka ce a yi haka don daidaita zaman lafiya?

Ni kenan kullum ina da matsala da ‘ya’yan miji, to menenhe aibuna? Me nayi musu?”

“Za ki iya zama a Kano?”

Tambayar ta yi mun kwatsam! Na bar kukan da nake yi a take na kalle shi.

“Ina da gida a Kano, idan kin yarda za ki zauna a can sai na mayar da ke can tunda ina shirye-shiryen bude wata harkar a Kano kwanannan. Ina son zama da ke Hauwa’u. Ni kaina nasan ina da matsala a cikin gidan nan. Kiyi hakuri a yanzu ko meye Zainab zata yi miki ki daure ki jure saboda ni da ke mu samu biyan bukatarmu.”

Hankalina ya dan kwanta, ya ce “Ina neman alfarma idan ba zan takura miki ba?”Na ce, “Ta meye?” Ya ce, “Abinci nake so ki samar mun wanda zan ci, yunwa ta dame ni.”

Tashi nayi a daren nayi wa Ahmad dan girki mai sauri yaci sannan muka kwanta. Tun daga nan na samu sassaucin damuwa, sai dai Hajiya ta daina amsa gaisuwata, duk da haka kuma ban daina zuwa gaisheta ba.

Zan zauna na kai mintina goma bata saurare ni ba. Shi ma na lura yana da ‘yar matsala amma tunda dai bai bude bakinshi ya fada mun ba sai ban tambayar shi ba. Na dai tsaya tsayin daka wajen ganin bai kuntata da yawa ba, don nasan matsalar ba ta wuce ta Hajiya ba. Ba a fi wata daya zuwa kwanaki arba’in ba sai shirin Ahmad ya kammala na bude babbar harkarshi ta kasuwanci a Kano.

Har yaje ya yi sati daya a can don ya tabbatar komai ya daidaita, sannan ya dawo. Muna kwance a dakinshi yana bani labarin yadda abin yazo cikin gagarumar nasara, ni kuma dokina sai karuwa yake yi zai bar zama da su Hajiya da ‘yan fitinannun jikokinta, zan koma Kano tare da mijina.

Ina ta ayyano irin tattalinshi da zaan kara yi da irin abubuwan da zan yi na ci gaba don kaina. Don kuwa nima yanayin kasuwancin Ahmad yana ba ni sha’awa, har nima na kan yi tunanin a matsayina na mace idan zan gwada babu mamaki nayi nasara.

Na ce, Kaga idan muka koma ni ma sai na gwada kasuwancin mata na cikin gida. Kallona ya yi cikin mamaki. “Kasuwanci kuma Hauwa’u? Na ce, “Eh mana, na zannuwa da gwala-gwalai irin naku ba.”

Shiru yayi yana kallona, ya ce “Ashe kina sha’awar kasuwanci?” Na ce, “Eh, zama da kai ne yasa

hakan, da can ba na yi.” Ya ce, To bari kayan da nayi oda wannan watan su zo sai na diban miki a ciki ki gwada muga irin taki nasarar. Kin san mata da yawa suna karban kaya a hannuna kuma suna samun

riba ba kadan ba. Amma abin da na lura da shi shi ne, ai wacce ta iya rikici saboda siyan kayan gida yawanci bashi ne. Ke kuma ban ga wannan a tare da ke ba.”

Ba mu yi bacci ba sai karfe daya saboda ‘yan hirarrakin da muke yi. Washegari bai kintsa da wuri ba saboda bakin da yayi abokan kasuwancinsa. Sai kusan sha daya na rana. Ya shigo dakina rike da mukullin motarshi yana ba ni sakon da zan bai wa Bala direba idan yazo, saboda haihuwar da matarshi tayi.

Sannan ya shiga wurin Hajiya. Kwanciya nayi don na dan yi barci kafin Azahar tayi. Sai dai ban ko yi nisa ba naji sallamar Larai.

Daga cikin dakin na daga murya ina tambayarta ko lafiya? Ta ce, Lafiya kalau Hajiye ce take kiranki.

Gabana ne ya fadi, to menene kuma? Ba dai naje na gaisheta ba. Nayi sallama a kofar dakin na shiga.

Har yanzu Ahmad yana nan bai fita ba, yana zaune can gefe a asa,  kanshi kamar zai dunguri kasa saboda

irin sunkuyon da ya yi. Jikina a sanyaye na zauna a gefe nesa da inda yake.

“Ina ce dai ita ce wannan?” Hajiya ta fara magana. “Yarinyar da ko darajar sauran matanka bata kai ba. A kanta ne kuma nake baka umurni ka ke kin bi.

Abinda ban taba zaton zaka iya yi ba shi ne take umurnina. Na kyale ku na zuba muku ido amma gaba dayanku ba ku fahimci hakan ba. Nan wurin nan kazo mun da maganar za ka kaita Hajji a bana na ce a’a banyarda ba, don ina ta binka ka biya wa Lado dan kanina har yanzu ba ka biya ba kana daga tafiyar.

Sai ka dawo min da maganaar zuwan ku Dubai wanda wannan ma duk wani salo ne na kin bin umurnin da na bayar din. Ka dai nuna mun a yanzu kai ma ka girma. Ba a wani dauki lokaci mai tsawo ba yarinyar nan ta zo har dakin nan ta zage ni.

Na gaya maka ban ji ka dauki matakin komai a kai ba. A jiya kuma abinda ka zo da shi shi ne za ka dauke  ta ku koma Kano da zama ko Amadu?

To bari ka ji wata magana, idan ba mantawa nay1 ba, ko a ranar da na haife ka, nayi nakudar ka ne ni kadai a dakina na haife ka na yanke maka cibi da kaina. Sannan ne nayi maka wanka kafin wasu ma daga gidan suka san na haihu, kenan ka gani babu wanda ya taya ni.

Don haka ba zan haifi da nayi tarbiyyarshi da irin abubuwan dadi da wahala da dawainiyar da nasha wata tazo ta kwace mun shi rana tsaka ina kallo ba, babu ita.

Zagina da tayi ba ka ce komai ba saboda ka daina gudun bacin raina sai nata, to na yafe maka amma ko don na yi wa tufka hanci ya zama hakan bai sake faruwa ba. Ga takarda da biro nan na baka rubuta takardar sakin aurenta yanzunnan ka bata, auren nata ya ishe ni haka.”

<< Mai Daki 17Mai Daki 19 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×