Fitowa ta 1
(Malam Jatau ya fito daga turu bayan ya shafe kusan sati uku a can. Gashi dai sauƙi ya samu domin yanzu ya bar batun bugun ruwa da dorinarsa, sai dai kuma ciwon mantuwa ya fara kama shi har ma baya gane mutane wani lokacin. Ya ma manta da an sa shi a turu har ya fito. Sakarci kuma sai abin da yai gaba. Gashi nan ya je siyayya wurin Sambo mai tireda)
Malam Jatau: Salamu Alekum. Malam Sambo yana ciki kuwa?
Sambo: (cike da mamaki) Alaikassalamu. A'a Malam Jatau kai ne, yau a gari in. . .
Malam Jatau fa abu ya ci tura.
Gaskiya malam Jatau abun sai a hankali.