Skip to content
Part 4 of 6 in the Series Malam Jatau by Haiman Raees

Fitowa ta 1

(Malam Jatau ya fito daga turu bayan ya shafe kusan sati uku a can. Gashi dai sauƙi ya samu domin yanzu ya bar batun bugun ruwa da dorinarsa, sai dai kuma ciwon mantuwa ya fara kama shi har ma baya gane mutane wani lokacin. Ya ma manta da an sa shi a turu har ya fito. Sakarci kuma sai abin da yai gaba. Gashi nan ya je siyayya wurin Sambo mai tireda)

Malam Jatau: Salamu Alekum. Malam Sambo yana ciki kuwa?

Sambo: (cike da mamaki) Alaikassalamu. A’a Malam Jatau kai ne, yau a gari in ji maƙi baƙo?

(ana iya jin muryoyin yara a kusa da su suna wasa)

Malam Jatau: (cike da rashin fahimta) ban gane ba, Sambo rashin cinikin tiredar ne ya sa har ka fara manta abubuwa ko kuwa bammi ka sha ne da safiyar nan?

Sambo: Hoi Jatau baki abin magana. Ai gani na yi rabonka da zuwa siyayya yau kusan mako biyu kenan. Kuma har na ji ma wai an saka a turu. Ina fata dai yanzu ka samu lafiya ko? Allah shi kiyaye gaba.

Malam Jatau: (muryarshi cike da rikici) Wato Sambo na dai ga alama gudumar da na yi maka a lokacin da muke neman auren Ta Mai-gari ce ke maka zafi har yanzu shi ya sa kake min ba’a ko? (ya ware hannayensa kamar ɗan dambe) To wallahi in ba ka iya bakinka ba yanzun nan sai in bazar da kai kuma na bazar da banza wallahi.

Sambo: (cike da mamaki) A’uzubillahi! Malam Jatau? Subuhanalillahi me kuma ya kawo wannan maganar Malam Jatau? Abinda ya faru shekara da shekaru ne kuma ya sa za ka taso da shi yanzu? Haba malam Jatau.

Malam Jatau: To ai gara in faɗa maka ne ɓaro-ɓaro. Shekaranjiya ina nan wurin fa na zo siyan sabulu, yau kuma ka zo kana ce min wai mako biyu kenan rabona da zuwa nan. To in ban zo wurinka siyayya ba sama zan je ko yaya? Kai dai da biyu an jefi biri da rani.

Sambo: (da jin haka sai ya fahimci halin da ake ciki, don haka sai ya wayance) Ni fa dama zolayarka nake yi. Amma tun da yau na ga ba ka jin yin rahar faɗi abinda zan ba ka.

Malam Jatau: (ya kaɗa kai) Kai dai faɗi gaskiyarka na ɗaure. Bani gishiri leda guda, sai ka bani wake mudu biyu, sai kuma wannan magin mai hoton zakara a jiki da manja gwangwani biyu.

Sambo: (cike da fara’a) A’aha ka ce yau ciniki ka zo min da shi raɓa-raɓa. Shi ya sa nake son zuwanka wallahi. Amma shi magi mai zakarar guda nawa zan ba ka?

Malam Jatau: (cikin isa da taƙama) guda biyu za ka bani. Kuma wacce nai maka guduma akanta ce ke da girki yau. Ita za ta dafa abincin.

Sambo: (ya yi dariya tare da kaɗa kai) Kai dai Jatau halinka sai kai wallahi (ya fara haɗa mishi kayan da ya ambata)

Malam Jatau: Oho dai, can ga su gada wai zomo ya ji kiɗan farauta.

Sambo: (ya yi dariya tare da miƙa mishi kayan da ya siya) To gashi. Sai kuma me za a kawo maka? Ko shikenan iya abinda kake so?

Malam Jatau: (Ya miƙa mishi kuɗin) Shikenan abinda nake so. In ka samu hali kuma anjima ina gayyatarka ƙofar gidana ka zo mu ci abincin dare. (Ya ajiye kayan a bakin tiredar) Saura canjina ko ba za a bani ba ne?

Sambo: (ya ƙuta) Kai Jatau abin naka fa ya fara yin yawa. Ga canjinka, Jeka na gode Allah ya saka da alheri. Ina da mai dafa min nima a gida.

Malam Jatau:. (ya karɓi canjin) Af toh! Ka ji haushi ne. Ai ka san dai wata miyar sai a maƙwafta ko?

Sambo: Na ji dai. Jeka. Inna ta gaida Aisha.

Malam Jatau: (ya kama hanyar tafiya, ya mance da siyayyar da ya yi) Ai dama ko ba ka faɗa ba tafiyar zan yi. (ya haura takalmansa ya wuce)

Sambo: (shi kaɗai) Kai wannan mutumi akwai rikici. Dama an ce cuta takan tadda hali, gashi yau na ƙara ganin zahiri. Allah dai ya ba ka lafiya Malam Jatau. (ya fara kakkaɓe ‘yan kayan shi da ƙura ta hau kansu, sai ga kayan da Jatau ya manta da su)

Sambo: Kai jama’a! Ashe ma ya manta da kayan da ya siya garin fitina. (sai ya kira ɗaya daga cikin yaran da ke wasa a kusa da wurin)

Sambo: Kai Ɗanliti, zo nan.

Ɗanliti: Na’am. To. Gani.

Sambo: (ya miƙa mishi ledar kayan da Jatau ya manta da ita) Amshi wannan, ka ga Malam Jatau yanzu ya bar nan, yi maza ka bishi ka kai masa wannan. In kuma ba ku haɗu ba ka wuce gidan shi ka ba iyalinshi.

Ɗanliti: To. (ya bi bayan Malam Jatau da kayan)

Fitowa ta 2

(yunwa ta ishi malam Jatau, gashi ya manta hanyar gida don haka sai ya miƙa ya yi ta tafiya ba tare da yasan inda ya nufa ba. Bayan ya wuni yana yawo sai gashi a majalisar su Ɗangwandi yana tafe yana kuka)

Ɗangwandi: (cike da mamaki) A’aha, kamar Malam Jatau nake gani tafe yana kuka.

Shekarau: Haba dai kai kuwa, wane irin kuka kuma sai ka ce ƙaramin yaro?

Ɗangwandi: Sa mai ganin dai. Babu shakka shi ne ke tafe. Bari kuma ya ƙaraso ka gani.

Shekarau: Ai kuwa in haka ne yau muna shirin ganin budiri.

Malam Jatau: (ya ƙaraso wurin yana kuka)

Ɗangwandi: Malam Jatau lafiya kuwa?

Malam Jatau: (yana ci gaba da kuka raɓe-raɓe) Ku taimaka min don Allah ku raba ni da ita. In kun raba ni da ita kuma ku kai ni gida.

Shekarau: To, me kake magana a kai ne? Mu fa ba mu gane ba.

Malam Jatau: Ita, tun da safe take bina ta kuma ƙi sakina.

Ɗangwandi: To ai mu ka ƙara jefa mu a duhu ne Malam Jatau. Shin akuya ce, ko macijiya ce ko kuma mecece ɗin da ta kama ka?

Shekarau: Yauwa, gara ka fito fili ka faɗa mana mu san ko menene. In za mu iya taimaka maka to, in kuwa ba mu iyawa sai mu kai ka ga sarki ya taimaka maka.

Malam Jatau: (Yana ci gaba da kuka) Ba yunwa bace take ta bina tun da safe ta dame ni da azaba, kuma ni gashi na mance hanyar gida.

(duk za su saki baki cike da mamaki)

Ɗangwandi: Babbar magana, yanzu yunwar ce ta saka kake kuka haka har da hawaye sharɓe-sharɓe?

Malam Jatau: (ya ɗaga kai sama alamar eh)

(duk sai suka fashe da dariya suna nuna shi da hannu. Shekarau kuwa har yana faɗuwa ƙasa tare da wuntsulawa saboda mugunta)

Ɗangwandi: (yana ci gaba da dariya) Kai amma duniya akwai ‘yan nema yasin. Yanzu kai ko kunyar faɗa mana wannan maganar ba ka ji ba?

Shekarau: Kasan me zai faru?

Ɗangwandi: A’a, sai ka faɗi.

Shekarau: Mu raka shi gida kawai in ya so sai mu barshi daga nan don kar ace mu muka yi mishi wani abin. Don ko da gani kai ma ka san abin ba na lafiya ba ne. Ko ya ka ce?

Ɗangwandi: Eh to, kaima kana da gaskiya. Amma ni da sai nake ganin me zai hana mu shiga gidana da shi ya fara cin abinci tukunna kafin mu raka shi ko kuwa?

Shekarau: (ya kaɗa kai) Hmm lallai Ɗangwandi na lura ba ka san halin mutanen zamani ba. Yanzu in ka ɗauke shi ka kai shi gidanka ya yi maka ta’adi wa za ka kama? In kuma wani abu ya same shi aka zo ana tambaya kai me za ka ce?

Ɗangwandi: Sai in faɗa musu gaskiya mana.

Shekarau: To wa zai yarda da kai in ma ka faɗa?

Ɗangwandi: A’aha, ba ga ka ba. Ai kai ne shaida ta.

Shekarau: (ya dafe ƙirji) Ni? Wa ya aike ni balle ya ga na daɗe? Mutumin da bai jima da fitowa daga turu ba ai kasan ba a kira shi lafiyayye ba. Ka san kuwa an ce ba a shari’a da mahaukaci. Wallahi in kana ganewa tun wuri mu lallaɓa shi mu yi gaba tun kafin mu shiga uku. Don in wani ya zo wucewa yanzu ya ganshi zai iya cewa mu muka dake shi ko muka yi mishi wani abu kuma ba mu da halin fidda kanmu ga wannan rigimar.

Ɗangwandi: I, da gaskiyarka kuwa. Ko rannan ma kuwa na ji wani da irin hakan ta faru da shi, bai ji daɗi ba da aka je wurin Mai Gari da shi. Amma yanzu to, menene abin yi.

Shekarau: Ai kawai abin yi shi ne kamar yadda na faɗa, mu lallaɓa mu raka shi ƙofar gidansa, in ya so sai mu barshi ya shiga mu kuma mu kama kanmu.

(za su samu su lallaɓa Malam Jatau su nufi hanyar gidan shi tare)

Fitowa ta 3

(Malam Shekarau, Ɗangwandi da Malam Jatau sun iso ƙofar gidan Malam Jatau, sai suka iske wani maƙwafcin shi mai suna Sidi ya zari darnin Malam Jatau yana bugun ɗansa da yai mishi laifi)

Ɗangwandi: A’aha, Subuhanalillahi! Malam Sidi me ya yi zafi kuma haka kake ta jibgar yaro ƙarami irin wannan? Ai sai ka kassara shi.

Sidi: Ai gara na kassara shi ɗin kowa ya huta da ya jawo min abin kunya.

Shekarau: A’a Sidi, ai ba a yi haka ba. Me yaron ya yi ne ka far mishi da irin wannan bugu haka?

Sidi: Wai ace yaron nan, yaron nan har ya san a aike shi wai ya ce ba zai je ba?

Ɗangwandi: I, gaskiya dai kam bai kyauta ba. Amma kasan hannunka ai ba ya ruɓewa ka yanke ka yar. Haƙuri ake yi, yara sai da haƙuri da nasiha.

Malam Jatau: (ya rushe da kuka) Ni wallahi ba zan yarda ba sai an biya ni.

Ɗangwandi: A’aha, me kuma aka ɗaukar maka da kake cewa ba za ka yarda ba sai an biyaka?

Malam Jatau: (yana taɓara) ba kwa gani Sidi ya zarar min darni haka kawai yana bugun ɗansa da shi? Ni sai an biya ni darnina.

Shekarau: Tofa! Yau ake yinta fa. Wannan shi ne ana wata ga wata. Ana ƙoƙarin kashe wata wutar kai kuma yanzu darnin da aka zara ne kake so sai an biya ka?

Malam Jatau: Eh, ni sai an biya ni.

Shekarau: (ya dafa Ɗangwandi) Am, ina ganin lokaci ya yi da ya kamata ace mun bar wurin nan.

Ɗangwandi: Gaskiya dai na ga alama.

Sidi: (cike da rashin fahimta) Me ke faruwa ne Shekarau? Lafiyar Malam Jatau ƙalau kuwa yake cewa sai na biya shi darnin da na zarar masa?

Shekarau: Yanzun dai babu lokacin bayani, mu dai za mu wuce yanzu. Dama rakiya muka yi masa, kai yanzu sai ka tsaya ku daddale a tsakaninku. (ya dubi Ɗangwandi) ai sai mu tafi ko?

Sidi: Ina fa za a yi haka? Ai sai dai ku tsaya a ƙarƙare komai a gabanku.

Shekarau: To yanzu kai Ɗangwandi sai ka tsaya, amma ni na yi nan. (sai ya runtuma da gudu)

Ɗangwandi: A’a kai Shekarau ya za mu zo tare kuma ka tafi ka barni? (shima sai ya runtuma da gudu ya bi bayan shi)

Sidi: (Cikin mamaki da rashin fahimta) Wai me ke faruwa ne? Aradu nima ba a barni a nan ba. (sai ya sungumi yaron da yake bugu ɗazu shi ma ya arce a guje)

(a nan suka bar Malam Jatau yana kuka har yaran shi suka zo suka shigar da shi gida)

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Malam Jatau 3Malam Jatau 5 >>

2 thoughts on “Malam Jatau 4”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.