Skip to content
Part 3 of 6 in the Series Malam Jatau by Haiman Raees

Fitowa ta 1

(Malam Jatau ya je gona shi da yaransa Sabbinani, Talle da Ganjarma. Bayan rana ta take wurin Azuhur sai ya aiki Talle gida ya amso musu abinci saboda ba su da nisa da gari. Bayan ya dawo sun ci sun yi sallah sai suka ci gaba da aiki.

Fitowa ta 2

(Yamma ta yi, Malam Jatau ya ce wa ‘ya’yansa su yi gaba shi zai tsaya ya ƙarasa aikin da ya rage musu. Kafin ya gama hadari ya haɗu. Da kama hanya kafin ya iso gida an goce da ruwa, ya kuwa lakaɗa mishi ɗankaren duka, duk kayan jikin shi da sauran waɗanda ya ɗauko na aiki suka jiƙe sharkaf. Saboda haka ya dawo gida a rai a ɓace)

Fitowa ta 3

(Malam Jatau ya dawo gida rai a ɓace, gashi nan ya shiga cikin gidan da kaya bisa kansa duk a jiƙe)

Malam Jatau: (Ya shigo gida babu ko sallama. Ya watsar da kayan da ya ɗauko a ƙasa, sannan ya samu wuri ya kame ya zauna ruwan ya ci gaba da dukansa)

Delu: (dama ita ke da girki, don haka tana gindin murhun da ke wani ɗan ƙaramin ɗaki a tsakar gidan tana kwashe tuwo. Bayan ta gama sai ta ɗauka da nufin ta kai ɗaki, tana fitowa ta ci karo da Jatau zaune a ƙasa shirim ruwa na ta bashi kashi)

Delu: (cike da tashin hankali) Subuhanalillahi! Maigida lafiya? Ruwa fa ake yi kuma ka zauna yana ta dukanka. Lafiya dai ko?

Malam Jatau: (ya ƙuta tare da juya kanshi gefe ba tare da ya ce komai ba)

Delu: (ta fito cikin alamun tsoro ta dafa shi) Maigida? Lafiya kuwa? Magana fa nake yi ka yi banza da ni. (da dai ta ga gogan bai da alamar ba ta amsa, sai ta koma ɗakin girkin ta jawo buhun niƙan tuwon da ta gama amfani da shi domin ta rufe mishi kai ko ya samu sauƙin ruwan)

Malam Jatau: (da bai yi niyyar cewa komai ba, amma ganin ta jawo buhu za ta yafa mishi bisa kai sai ya fusata, ya miƙe tsaye ya hau ta da faɗa) Ke wace irin mahaukaciya ce da za ki yafa min buhu a kai sai ka ce wani ƙaramin yaro?

Delu: (Cikin takaici) Allah sarki ne! Da ma Hausawa kan ce abin arziƙi ba ya kyau da kare, ko ya yi ma sai an zage shi. Ni dai fito daga ruwan nan mu je ɗaki tukunna.

Malam Jatau: Wai ke ina ruwanki da ni ne ma wai? A kanki nake zaune ne ko me da har za ki wani yayibo buhu za ki rufe min kai? Af toh! Ni ne karen kenan ko me kike nufi?

Delu: Subuhanalillahi! Maigida ni na isa in kira ka da kare? Zance ne dai kawai irin na Hausawa. Na dai lura kamar fushi ka ke jin yi yau. Don Allah mu je ɗaki ka sake kayan jikinka. Ni ba rigima nake jin yi ba.

Malam Jatau: Au toh, magana za ki faɗa min kenan. Ruwa ya zane ni a banza ban ci ba ban sha ba shi ne ke kuma za ki zo ki faɗa min magana maras daɗi ko? Jai’irar mace kawai.

Delu: A’a fa mai gida banda zagi. Ko da yake an ce zomo ba ya faɗa da makashinsa sai maratayinsa, ban fa ga dalilin da zai sa ka zage ni akan ƙoƙarina ba.

Malam Jatau: Wannan mace kin cika ‘yar gwafar uba! Da fari kin ce min kare, yanzu kuma kin ce min zomo, anjima kuma ƙuda za ki kira ni ko? An zage ki ɗin, za ki rama ne?

Delu: Ni dai Maigida abin duk ba na faɗa ba ne. Ka ga ruwa sai bugu ba yake haka kawai, mu je ɗakin dai ka sake kayan. (ta ɗan tura shi gaba da nufin su je ɗaki)

Malam Jatau: Da yake ai ƙusa na kafa miki dole ki ce haka. Au dambe za ki yi da ni? Na ce dambe za ki yi da ni? (sai ya kai mata bugu)

Delu: (ganin bugun da ya kawo mata ya sa ta goce, ai kuwa sai santsi ya kwasheta ta faɗi ƙasa ta fasa baki kuma duk jikinta ya ɓaci da taɓo) Wayyo ni jikar Kallamu. Maigida dubi yadda ka ja min na fasa baki fa? Anya kuwa yau abin na lafiya ne? Ko dai ka haukace ne?

Malam Jatau: (Ya ƙara kai mata bugu) ‘Yar nema. Wato ni ne mahaukacin ko? Ai maganinki kenan. Alhakina ne ya kama ki. (ya sake kai mata wani bugun)

Delu: ‘Wayyo jama’a ku taimake ni zai kashe ni. (daga nan ta tashi ta nufi ɗakin Ta Mai-gari a guje)

Malam Jatau: (Shi kuwa komawa ya yi ya zauna abinshi har aka ɗauke ruwan tukunna ya tashi ya shiga ɗaki.

Bayan an ɗan jima Ta Mai-gari ta rako Delu ɗakinta aka sulhunta su.

Fitowa ta 4

(Da gari ya waye, dama ranar kasuwar garin ke ci. Saboda haka sai Malam Jatau ya je kasuwa ya siyo wata zabgegiyar dorina mai baki iyu ya siya man shanu ya shafe ta da shi ya adana abinsa)

Fitowa ta 5

(Bayan an kwana biyu, rannan sai hadari ya haɗu, ba a jima ba sai kuwa aka tsuge da ruwa kamar da bakin ƙwarya. A wannan lokaci kuwa Malam Jatau na zaune a turakarsa, da dai ya ga ruwan nan ya sauko sai ya nannaɗe ƙafar wando ya suri dorinarsa ya yi waje)

Malam Jatau: (ya fito tsakar gida yana kai wa ruwa duka da dorinarsa) Karɓi! Amshi! Ungo nan! Haka kawai ka kama ɗan talikin da bai ji ba bai gani ba ka daka son ranka ka ce ba zai rama ba? Ai kaima ka san ana zaman ƙarya wai baƙauye da ya je birni ya tambayi masussuka aka ce babu. Lallai yau sai na rama dukan da ka min waccan ranar (sai ya ci gaba da kai wa ruwa duka)

Abu: (tana ɗaki zaune ita da ‘yarta ta fari wadda ake kira Lantai suna saƙa) Ke ‘yan nan ɗauki bokitin can ki tarba min ruwa ko ma samu na sha. Na ga na randar nan kamar ya kusa ƙarewa.

Lantai: To Mama. (ta miƙe ta ɗauko bokitin za ta tari ruwa da shi)

Abu: Saura kuma kar ki ɗauraye bokitin, ki tara min ruwa da shi hakanan ki ga yadda za mu ƙare ni da ke. Gama na ga alama ba ki da hankali.

Lantai: (ta ɗauraye bokitin ta tara ruwan kenan sai ta hango Jatau yana ta kai wa ruwa duka) Mama, zo ki ga abinda Baba yake yi.

Abu: Wannan yarinya akwai ‘yar nema, me zan zo in gani da ban taɓa gani ba?

Lantai: Ke dai ki zo ki gani Mama. Wani irin wasa ne Baba ke yi da bulala. Amma bana ganin sauran abokan wasan nashi.

Abu: Ke dalla can raba ni da surutan banza irin naki. Baban naki ne zai fito yin wani wasa ana tsuga uban ruwa irin wannan. Sai ka ce wanda aljanu suka shafa.

Lantai: Wayyo Mama! Aljanu dai?

Abu: Hoi! Wannan akwai ja’ira. Hausa fa nake miki.

Lantai: To mama, bari in je mu yi wasan tare (kafin uwar ta ce wani abu har ta yi waje, duk kiran da take mata a banza ba ta ko waiga ba)

Malam Jatau: (yana ta ci gaba da kai wa ruwa bugu, bai lura da Lantai ta zo wurin shi ba har sai da bakin dorinar ya sameta a hannu tukunna ta fara kuka) Wato bayan ka dake ni rannan shi ne kuma har da ɗiyata za ka haɗa? (shi a tunanin shi ruwan ne ya sa yarinyar kuka, don haka sai ya ƙara zage damtse wajen kai wa ruwan duka)

Da haka fa iyalanshi suka dinga fitowa ɗaya bayan ɗaya suna bashi baki amma ya ƙi saurarar kowa daga cikinsu. Duk wanda ya nufe shi in ya tsula mai dorina sau ɗaya ba ya ƙara komawa. A haka dai har sai da maƙwafta suka taru tukunna da ƙyar aka samu aka kama shi aka ɗaure, shi kuwa sai cewa yake ‘Ku barni in rama dukan da ruwan nan ya yi wa ɗiyata.’ Da dai aka ga abin ba na lafiya ba ne sai aka saka shi a turu.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 6

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Malam Jatau 2Malam Jatau 4 >>

1 thought on “Malam Jatau 3”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.