Skip to content
Part 2 of 5 in the Series Matakan Nasarar Iyali by Hamza Dawaki

BUKATUN MA’AURATA

Gidan aure shi ne matattarar rikici, kuma gidan auren nan dai shi ne matattarar dukkan farin ciki! Yanayin da gidajen aure kan kasance a ciki sukan bambanta, daga gida zuwa wani. Amma za a iya cewa kusan kowane gida yana da irin wannan dabi’a, cewa shi ne wurin farin ciki ga ma’auratan, lokaci guda kuma shi ne dai idan ya cakude, to babu wani muhalli da ya kai shi rashin dadi!

Amma masana suna ganin akwai wasu muhimman matakai da suka kamata ma’aurata su bi domin kyautata nasu gidan, ya kasance farin cikin sa ya rinjayi bakin cikin. Ku zo mu bibiyi matakan tare da ku, daya bayan daya, kamar haka:

Karfafa gwiwa

Kowanne mutum, kuma ko ma me yake yi, sawa’un sana’a ce ko ma wasa ne yake yi, yana bukatar karfafa gwiwa daga mutanen da suke kewaye da shi. Musamman wadanda kuma yake da wata dangantaka da su. wannnan karfafar gwiwar kuma ta hada har tsakanin ma’aurata guda biyu. Amma, musamman namiji a nan, yana so ya samu ƙarfafar gwiwa daga gidansa a mataki na farko, kafin wasu daga waje su ƙarfafa masa gwiwa.

Akan ce: ‘Duk wani namiji da ka ga ya samu ɗaukaka, ya yi wani gagarumin abu na a zo a gani, to babu shakka akwai wata mace a gefensa da take ƙarfafa masa gwiwa.”

Wannan kuwa ko shakka babu. Sau da dama, namiji yakan ji ƙarfin aiki a jikinsa ne yayin da ya tuno yadda sakamakon aikin kan yi tasiri wurin biyan buƙatun iyali ko iyayensa. Kuma yana matuƙar tsanar aiki da gajiya da shi a lokacin da ya tuno irin rashin ɗa’a da halin ko-in- kula da waɗanda yake wahalar don su sukan nuna masa. 

Hakika mijinki yana bukatar ki yi masa abubuwa da dama na karfafa gwiwa wadanda a baya mahaifiyarsa ce take yi masa.

Karfafa gwiwar miji zai iya yiwuwa ta hanyoyi da dama. Musamman ta hanyoyin kalamai, wato fada masa da baki yadda abubuwan da yake yi a gidansa suke da muhimmanci. Ko yadda yake kyautata wa iyalinsa. Da makamantan wadanna. Haka kuma za a iya yi a aikace. Ta hanyar nunawa da jiki da fuska da alamtawa, ta yadda zai fahimci lallai ana so a tabbatar masa ne cewa tagomashin da yake yi yana samun karbuwa.

Kwantar da hankali

Matarka tana bukatar samun kwanciyar hankali cikakke daga wurin ka kafin ka kai ga samun duk wata karfafar gwiwa da abubuwan da su ka kamance ta daga gare ta. Ma’ana samar da kwanciyar hankali a cikin zuciyarta. Wato ta sami nutsuwa a ranta cewa kai din dai za ka tabbata nata, a yau da gobe. Ba wai a iya yau ba, kuma in rayuwa ta sauya kai ma ka sauya ta. Yawancin mata sukan yi addu’a akasin ta mazajensu a irin wadannan matakai. Wato yayin da shi yake addu’ar Allah Ya kawo budi da watada, ita ko tana can tana addu’ar Allah Ya bar su a wannan mataki har abada. Ba kuma komai ne yake sa wannan ba sai rashin samun kwanciyar hankali.

Samun kwanciyar hankali yana nufin ta ji kuma ta gamsu har ranta cewa duk ma irin sauyin da ka samu a rayuwa za ku kasance tare. Ba za ga kore ta ko sauya da wadda ta fi daidai da mutum mai cin duniya da tsinke irinka ba. Ba kuma za ka ajiye ta a a gefe kamar wata ratayayyiyar rigar ruwa ba, wadda sai damina-damina in ruwa ya tsananta za a tuno da ita.

Sau da yawa abubuwan da muke furtawa a gaban iyali su ne suke tasiri a zuciyarsu wurin kallon da suke yi mana. Akwai kalamai da dama da za ka furta matarka ta fahimci ai kana tare da ita duk canjin da za ka samu a rayuwa, domin za ta ji duk tsare tsaren sabuwar rayuwar da ita ake yin su. Sannan akwai wadanda za ka rika yi ta fahimci lallai ba da ita za ka yi sabuwar rayuwarka ba. Bayan kalamai ma akwai ayyuka ko motsi ko alamu da mata suke lissafin yaya rayuwarka za ta kasance game da zamantakewa da su.

To duk matar da ta fahimci tare kake son yin rayuwa da ita ko da an samu sauyi, to ita ce take samun kwanciyar hankali, kuma ita ce take iya sakin jiki ta karfafa maka gwiwa. Haka nan kuma duk matar da ta fahimci ba da ita kake shirin sabuwar rayuwarka ba, ba ta da wata kwanciyar hankali, kuma ba za ta iya sakin jiki da karfafa maka kwiwa ba.

Kulawa da yarda

Matarka tana bukatar cikakkiyar kulawa, wadda kuma sai ka ba ta ita ne sannan za ka sami yarda daga gare ta.

Yayin da namiji ya nuna soyayyarsa da kulawa da kuma damuwa da dukkan wani abu da ya shafi abin da yake kaiwa da kawowa a zuciyar matarsa. Har kuma ta fahimci hakan har cikin zuciya, sai ta samu gamsuwa a ranta cewa lallai ana son ta. Nan take kuma za ta ji kanta cewa ita wata mace ce ta musamman a wurinka.  Idan kuwa har hakan ta faru, an biya mata daya daga cikin manyan bukatunta na soyayya kenan. Samun wannan biyan bukatar kuma, shi zai sa ta yarda da mijin. Yayin kuwa da ta yarda da shi, to za ta zamar da shi tamkar shi ne zuciyarta. Ta yadda babu wani sirri nata da za ta iya boye masa.

Yayin da duk kuwa ka ga mace ta saki jiki da namiji, tana bayyana masa dukkan sirrikanta, alama ce ta cewa ta gama yarda da shi. Yarda da shi kuwa yana faruwa ne yayin da ta sami tabbaci a ranta cewa lallai yana yin bakin kokarinsa wurin ganin ya kyautata tare da faranta mata.

Harwayau, yayin kuwa da duk mace ta nuna wa mijinta cewa lallai ta gamsu da irin kokarin da yake yi wurin ba ta kulawa, to shi kuma namiji ta gama burge shi kenan. Ta kuma biya shi daya daga cikin manyan bukatunsa na soyayya da zamantakewa, a matsayinsa na maigida. Don haka idan kuma har ya sami wannan, ya kuma gamsu cewa abin da take nufi gaskiya ne har ranta. To shi kuma a daidai wannan lokacin ne zai kara kaimi wurin ba ta wata kulawa ta musamman da ba ta taba zata ba.

Fahimta da karba

Yayin da mace take son mijinta ya nuna mata lallai ya fahimce ta a cikin dukkan abubuwan da ta zo masa da shi, dole ita kuma sai ta karbe shi a duk yadda yake. Ba kuma tare da yunkurin sai ta canza shi ba.

Yayin da duk namiji ya zauna ya saurari mace, cikakken saurare, ba tare da katse ta ko yanke mata hukunci a kan matsalar da take magana a kai ba. Bayan ta gama ya kuma nuna mata lallai ya fahimce ta, tare da nuna gamsuwarsa game da abin da take magana. Ko kuma ya nuna damuwarsa game da abin da duk ta nuna ya dame ta. To ita a wannan lokaci ya yi mata komai, kuma ya biya mata daya daga cikin manyan bukatunta na soyayya. Za kuma ta gamsu cewa lallai yana son ta. To ita kuma samun wannan yanayi daga wurin mijinta shi ne zai ba ta damar karbar sa a duk ma yadda yake.

Yayin da duk mace ta yarda da ra’ayin mjinta, ta ci gaba da son sa a yadda yake, ba tare da ta yi kokarin dole sai ta sauya shi ba, to daga nan shi kuma zai gamsu cewa lallai ya sami karbuwa a wurinta. Karba a nan wurin ba ta nufin dole mace ta yarda cewa lallai mijin nata ya kware a kan komai ba. Amma dai dole ta nuna masa cewa lallai ta yarda shi ma yana da cikakken hangen da zai iya tafiyar da ragamar gida da iyalinsa bisa kyakkyawan tsari, ba tare da nuna lallai sai ta sa shi a hanya sannan zai iya tafiyar da ragamar rayuwarsa da tasu ba. Ta nuna a aikace cewa lallai ta yarda da shi, kuma ta yarda shi kadai ya isa ya kai su ga gaci.

Yayin da kuwa duk namiji ya sami wannan yanayi a gidansa to babu abin da zai hana ya ba wa matarsa cikakken lokaci ya saurare ta sauraro mai kyau, ya kuma nuna mata lallai ya fahimce ta.

Girmamawa da yabawa

Mata suna bukatar wata girmamawa da kaddara darajarsu daga mazansu, yayin da mazan suke bukatar a yaba komai da su ka yi a matsayinsu na magidanta.

Yayin da maganganun miji da motsi da ayyukansa su ka bayyana lallai yana ganin daraja da kimar matarsa, sai ta rika ji a ranta cewa lallai ya girmama ta. Wannan ganin ana girmama ta din kuma shi zai sa ta yaba komai da ya zo daga gare shi.

Yabawa, tana daya daga cikin manyan bukatun da kowane namiji yake muradin samu a gidansa, sawa’un ya sani ko bai sani ba. Yayin da namiji ya sami yabawa daga iyalinsa, to ya samu dukkanin wata karfafar gwiwa ta yin kowane irin aiki don biya musu bukata kenan.

<< Matakan Nasarar Iyali 1Matakan Nasarar Iyali 3 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×