“Babu tausayi bare imani aka wuce da Meenal a sumen. Yaya Sani da ya sami kiran gaggawa yazo ya sami Nafisa a shimfide bata motsi. Duk yadda zan kwatanta maka irin tashin hankalin da muka shiga ba zaka fahimta ba, idan ba kana wurin ba. Meenal tana farfadowa aka rufeta da duka, bata iya cewa eh bare a’a sai dai aga tana duban hannayenta tana kukan fitar hankali.
Gidan da Meenal tayi rayuwa ita da mahaifiyarta, dama ina yawan kaita gidan, ina gaya mata ni da ita muka yi rayuwa a gidan, a lokacin da duniya ta juya mana. . .