Skip to content
Part 21 of 28 in the Series Meenal by Fatima Dan Borno

Firgigit yayi a lokacin da Meenal take shigowa hannunta riƙe da abinda taje kawowa.

Bai ce komai ba ta miƙa masa Apple ɗin ya karɓa ya ci.

Meenal tana zaune tana saurarensa da abokin aikinsa yana gaya masa aiki ya yi kyau, mutumin ma yana ta tambayar ina Dr. Ahmad.

Murmushi kawai yayi ya ce “Meenal tashi ki je ki duba shi, a madadina.” Miƙewa tayi tana dariya tabi bayan Doctor Peter.

Da Sallama suka shigo farin bafullatanin me tsananin kwarjini ya yi saurin juyowa yana kallon Meenal. Ita kanta zuba masa idanu tayi tana jin wani abu yana huda ta.

Hannu ya miƙa mata, “Zo nan jikata.” Da yake da Hausa ya yi maganar shiyasa Dr. Peter bai gane abinda ya ce ba, amma kuma duk da haka sai da ya dube su da mamaki.Yana jinjina ƙarfin zumunci irin na Hausa Fulani.

Meenal ta ƙaraso ta ɗan kwanto masa ta rufe ido. Ita kaɗai tasan wani irin sanyi da ke shigarta. Shi kansa sai bubbuga bayanta yake yi. Dr. Peter ya katse masu shurun da yi masa bayanin ita ce matar Dr. Bakori. Ya ce “Masha Allah. Masha Allah.” Abinda kawai yake iya faɗi kenan. Daga bisani ya hau roƙon Dr. Peter ya barshi ya taka ya je gurin Dr. Bakori domin duba jikinsa. Wannan karon ba su yi dogon gardama ba kamar yadda suka saba da zarar ya roƙi zuwa ganin Ahmad.

Duk da haka mutumin bai saki Meenal ba suka ƙarasa gun Ahmad da ke kwance yana zancen zuci.

Ganin mutum riƙe da hannun Meenal kuma ko a jikinta ya cika da mamakin yaushe Meenal ta koyo halayyar yahudawa? Don haka ya sha mur kawai.

“Doctor ya ƙarfin jikin? Sunana Abubakar Munnir sarkin Gombe. Na ji daɗin yadda ka zama silar samun lafiyata bayan dogon ciwon da nayi har anfara kuka tsoho zai mutu. Yanzu Dr. Peter yake ce min wannan jikan tawa mai kama da jinina ita ce matarka.”

Kallo aka shiga yi a tsakanin Meenal da Ahmad. Bai san lokacin da ya tashi zaune ba. “Kana nufin kai ne Sarkin Gombe?”

Gyaɗa kansa yayi yana sake duban Meenal cike da dogon nazari. Ahmad ya yi ajiyar numfashi, “Alhamdulillahi.” Meenal ta kwantar da kanta a jikin dattijon nan hawaye na zuba a fuskarta. Mamaki yasa Sarkin Gombe buɗe baki da ninyar yin magana. Sai kuma ya yi shuru yana nazarin fuskokin su.

“Matarka jinina ce ko? Ta yaya hakan zai faru bayan Munnir kaɗai gareni kuma dukka ‘ya’yansa suna tare da mu. Ko a cikin dangina ne?”

Cike da jin zafi Ahmad ya ba shi amsar da bai san lokacin da ya fito ba, “Ɗanka Munnir da kake tunanin ya zama magajinka shine ya yi wa mahaifiyar Meenal ciki daga ƙarshe yake azabtar da mu. A dalilin haɗuwa da kai aka harbeni.”

Gaba ɗaya jin sarkin Gombe ya ɗauke ji yake ko dai mafarki yake yi ne? Zama ya yi yana duban Ahmad da alamun ƙarin bayani yake nema.

Sannu a hankali Ahmad ya warware masa komai. Tabbas da ba dan warkewa daga mummunar cutarsa ba, da babu abinda zai hana ciwonsa tashi. Hawaye suka gangaro bisa fuskarsa. Ahmad ya shiga ruɗani bai taɓa ganin babba namiji yana kuka ba, bare har a ce babban ma Sarki da kansa. Danasani ya kama Ahmad. A tunaninsa Sarkin halinsa guda da ɗansa, shiyasa ya gaya masa kai tsaye. Tsoron Ahmad kada aikin da ya sha wahala wajen yi ya lalace.

Sarkin Gombe ya sake riƙe Meenal da ke kuka yana girgiza kai, “Da ba dan Meenal ba da na ƙaryata ka da na ce jinina ba zai taɓa rashin imanin nan ba.”

Shuru ɗakin ya ɗauka kamar ba za a sake tankawa ba. Ahmad ya rasa dukkan wani ƙarfin guiwa. Ba zai iya kallon idon tsohon ya cigaba da gaya masa munanan halayyar ɗansa ba.

Sarki Abubakar ya cigaba da magana cikin sarƙewa. “Munnir zai yi danasani, a lokacin da bai da amfani. Tunda yasa na zubar masa da hawaye insha Allahu sai ya zubar da hawayen nadama. Ban san da ke ba Meenal da na karɓe ki hannu bibbiyu. Da na fi alfahari da ke. Ki yafe min Meenal na haifo wanda ya cuzguna maki daga ke har mahaifiyarki.”

Da lafiyar Ahmad ƙalau da babu abinda zai hana shi bai fice daga ɗakin nan ba. Da gaske yake jin tausayin dattijon har cikin ransa.

Ahmad ya sake dubansa a karo na barkatai, “Rankashidaɗe ina ganin ba kuka ko baki ya kamata kayi ba. Ka bi komai a hankali.”

Miƙewa Sarki ya yi ya dubi Ahmad, “Ka bani number ɗinka da address ɗinka a cikin satin nan zan koma Najeriya, duk abinda ake ciki zan neme ka. Amma don Allah ka bani Meenal in tafi da ita cikin iyalaina.” Tun kafin Ahmad ya yi magana Meenal ta zare kanta daga gun Sarki ta koma kusa da Ahmad tana girgiza kai, “Kayi haƙuri Kaka mahaifiyata ce kaɗai zata iya dawowa ta raba ni da Yayana in haƙura saboda tafi kowa shan wahala a kaina. Idan aka raba ni da shi ko na sati guda ne Kaka zan iya mutuwa. Kayi haƙuri bana son haɗa idanu da mahaifina. Na tsane…”

“A’a Meenal na gaya maki bana son irin wannan kalaman. Har abada mahaifi mahaifi ne. Baki isa ki sauya masa suna ba.”

Sarki ya sake jinjina kaifin hankali irin na Ahmad. Ko da yake kallo ɗaya zaka yi masa ka fahimci yana da natsuwa da kamala. Sarki ya sake duban Ahmad, “Na gode ɗana. Ka gaya min abinda kake so inbaka. Kuɗin aikinka yayi kaɗan a cikin abinda zan iya baka.”

Ahmad ya lumshe ido yana jin kansa yana sarawa, “Kuɗin aikin ma na yafe. Babu aikin kuɗi a tsakanin mu. Meenal ta zama silar wannan aiki da nayi maka. Yau ga ‘yar da ake gudu tayi abinda babu wata jikarka da ta taɓa yi. Roƙona shi ne ka sada Meenal da danginta, itama ta zama ‘ya mai cikakken ikon zama a ƙarƙashin danginta. Rankashiɗaɗe ina son farin cikin Meenal. Ka taimake ni. Ita ce ta zauna da ni ina cikin halin da ban san kaina ba. Ita ce ta kula da ni a lokacin da aka fidda rai da sake rayuwata. Idan kayi min haka ka gama biyana kuɗin aikina.”

Sarki ya ɗinga duban Ahmad yana godewa Allah da jikarsa ta sami miji na gari. Zai tafi Gombe hankalinsa a kwance don yasan Ahmad ba zai taɓa barin ko sauro ya ciji Meenal ba.

Miƙewa ya yi bayan Ahmad ya zube masa dukka lambobinsa ya koma ɗakinsa yana jin tamkar ya ɗauke Meenal. Wani irin sonta ke mamaye dukkan jikinsa. Tun lokacin da ya ɗora idanunsa akanta yake ji a jikinsa, Tana da alaka da jininsa. Haka ya koma ɗakinsa cikin mutuwar jiki.

Ahmad ya kafe Meenal da idanu ya nuna mata hanya alamun ta wuce wajensa

Jikinta na rawa ta tashi tana goge hawayenta tayi hanyar fita. Zuciyarta bata bata ta tafin ba, don haka ta ɗan waiwayo tana son gazgata abinda ya ce. Lumshe idanu ya yi tare da gyaɗa kansa. Hakan ya bata ƙwarin guiwar ficewa. Shi kansa da yana da yadda zai yi ya bar Meenal da yau ya barta ta tafi ga Danginta. Sai dai yadda yake jin shaƙuwarta a ransa ba zai iya rabuwa da ita ba, ko da kuwa na kwana ɗaya ne.

Da ficewarta ya hangota rungume a ƙirjin wani Bature suna dariya, “Meenal ɗina tana da kawaici fiye da kowacce mace. Meenal ɗina tsoron mijinta take yi tana kunyarsa bare kuma akai ga bature. Zai fi kyau ace ana son wasa da hankalin Dr. Bakori ne wajen cusa masa tsanar Meenal.

“Idan namiji yana kama Meenal ba zan taɓa yarda ba. Saboda nasan wacece ita.” Dariyarsu yake ji wanda kai tsaye hakan ke nuna masa suna cikin nishaɗi. Daga kwancen ya kafe su da idanu har idanunsa yakai kan ɗan zoben da ya siya mata a Abuja ranar da suka je siyayya take bashi labarin Bafullatani ya ɓatar mata da zobe.

Haka idanunsa suka sauka akan ɗan tabon da ke hannun Meenal ga shi nan a jikin wannan Meenal ɗin. Lumshe idanu ya yi kansa yana wani irin sarawa da ƙarfi. Ya sake Rufe idanunsa, baya son yana kallonsu. Sai dai kuma kamar akansa take kwasar dariya, muryarta tana yi masa amo. “Meke faruwa ne? Bari Meenal ta shigo inji wacece wannan Meenal ɗin? Ko dai dama ‘yan biyu ne.

_Na sadaukar da shafin nan a gareku masoya littafin Meenal, musamman masu Comment na cikin dandalin Bakandamiya. Ku zo mu hadu mu yi comment mu yi hira a karkashin comment din labarin nan mai rikitarwa. Ku zo mu yi zumunci. Ina kaunarku fisabilillah. Ku danna mana like insha Allahu tare zamu karanta littafin nan har karshe ina jin ra’ayoyinku.

“Meenal wacece take kama da ke? Ina yawan ganin mai kama da ke.” Dariya tayi ta mayar da zancensa kawai kamar tatsuniya. Hancinsa ta ja tana ‘yar dariyarta, “Husband nayi hira da Kakana cikin so da ƙauna. Kakana har yana bani labarin matarsa Hajiya Fulani me tsananin riƙo da Addini. Ya bani labarin Masarautarmu.”

Yadda yaga tana cikin nishaɗi yasa ya kai hannu fuskarta yana shafarta. “Meenal kina kina cikin farin ciki?”

“Yes Ɗan bafillatani na ina cikin farin ciki fiye da kullum. Kai fa?” Ta yi maganar cikin shagwaɓa. “Ina cikin farin ciki tunda Ahnal tana cikinsa.”

“Husby rufe idonka inyi maka wani abu.”

Idanunsa fes akanta bashi da alamun rufewan, “Naƙi wayon ba zan rufe ba.” Matso da fuskarta tayi saitin nasa fuskar ta hure masa idanun. A take suka rufe ruf! Murmushi tayi sannan ta ɗora bakinta a goshinsa ta bashi sumba… Shi dai komai nasa daban ne. Bai hanata ba, haka bai mayar mata da martani ba kamar yadda ya saba. Hakan yasa ta zare kanta tana dubansa cike da mamaki.

Cikin dabara ya ware idanunsa ya ce, “Ni kaɗai nasan me nake ji akan ki. Ni yarinyar nan ma kamar so kike inyi maki wani abu ko? Zo nan ki kwanta kusa da ni.”

Tashi tayi ta koma ɗan nesa da shi tana ta kwasar dariya. Ajiyar zuciya ya ƙwace masa, “Wacece ta biyun Meenal? Meyasa take son hargitsani?”

Cikin ikon Allah Dr. Bakori ya miƙe sarai haka ya ci nasarar yi wa Meenal ɗinsa aiki, zaman jiran farfaɗowarta kawai yake yi. Dr. Peter ya shigo yana dubansa, “Har yanzu bata farka ba?” Ya tambaye shi da alamun tsoro a fuskarsa.

Hakan yasa jikin Ahmad sake mutuwa. Da kai kawai ya amsa masa domin zuciyarsa duk babu daɗi. Dukkan su suka yi jigum jigum.

“Yaya…” Daga Ahmad har Dr. Peter aka hau rige-rige. Ahmad ya kamo hannayenta yana gyara mata gashin da suka fito daga cikin hulan kanta saboda yawa. “Meenal kin farka? Sorry zaki ji sauƙi kin ji?” Canza fuska tayi alamun zata yi kuka, ya ɗinga girgiza mata kai, ya ɗora yatsunsa a bisa laɓɓanta, “Idan kika yi kuka zaki sha duka. Oya mayar da fuskar nan kalar fara’a yanzun nan.”

Yadda yayi maganar cikin ɗaure fuska yasa ta kama dariya irin ta marasa lafiya. Ajiyar zuciya ya yi yana yiwa Allah godiya. Peter ya dafa kafaɗarsa a lokacin da suka miƙe domin ficewa daga ɗakin Meenal. “Wato ban taɓa tunanin malam Bahaushe yana soyayya da matarsa ba. Na fi ganin irin haka a wuraren mu, namiji kamar ya kwanta a ƙasa saboda mace. Sai gashi naga naku soyayyar ba irin namu bane. Naku ya fi burgeni.”

Ahmad bai ce masa komai ba sai ‘yar murmushi. Sau tari Peter baya son yin hira da Ahmad saboda sai ya gama jawabi sai ya yi zaton zai bashi amsa sai kawai yaga ba haka ba.

Har waje suka je tare ya kwaso abinda zai kwasa. “Dr. Dubi abin mamaki matarka da yanzu ta farfaɗo kuma sai gata a waje sai sauri take yi.” Ahmad ya zubar da duk abinda ke hannunsa ya bi bayanta. Peter ya durƙusa yana kwashewa.

Sun yi tafiya mai ɗan nisa a tsakanin su tana ta sauri. Yasa hannu ya juyo da ita. Abin mamaki da tsoro ba Meenal ba ce haka wannan bata da kama da Meenal. Murmushi tayi masa kawai tana dubansa. Haƙuri ya bata ya juya kawai ba tare da ya sake ko da waiwayota ba.

Ɗakin Meenal ya koma ya sameta tana nan a kwance. Cikin ‘yar shagwaɓa ta ce “Yaya zanyi fitsari.” Damuwar da ke ɗauke da fuskarsa ya yi ƙoƙarin ganin ya kauda. “Zo kiyi a jikina.” Dariya kawai tayi masa. Ɗaukarta ya yi cak! Ya kai banɗakin. Ƙiri ƙiri ta ƙi yin fitsarin wai sai ya fita. Ganin suna ta jayayya yasa ya fice. Sai da ta fara yin fitsarin kawai taga mutum ya shigo. Rintse ido tayi tana cewa, “Ayya babu kyau fa. Haramun ne.”

Girgiza kai ya yi, “Ba haramun bane lada ne.” Tana gamawa ya ce zai yi mata tsarki saboda hannunta. Amma fir ta ƙi amincewa.

Cikin nasara Ahmad ya koma gida Abuja. A hotel ya sauka suka yi kwana biyu sannan suka dawo wannan rugar

Duk abubuwan da Ahmad ya bari ayi ankammala komai tsaf. Hatta Kujeru da gadon da ya ce yana so haka aka sa masa. Unguwa ya koma kamar akwai mutane masu yawa a ciki. Wanda gaba daya fulani ne suka kewaye su. Masallacin ma yayi kyau sosai, haka gidan Lado da ya ce a mayar masa ginin zamani shima yanzu yafi kowa girman kai a unguwar. Jin kansa yake tamkar wani sarki.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Meenal 20Meenal 22 >>

1 thought on “Meenal 21”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×