Ta zauna tare da yin tagumi. Ta tuna tayi gwagwarmaya da wadanda suka fi Zayyad wayo da dukiya ta ci nasara bare kuma Zayyad. Dan haka wata dabarar ta sake dawo mata kai.
Zayyad kuwa bai wuce gidansu din ba kamar yadda yayi ninya, kai tsaye asibiti ya wuce.
Baisan dalili ba, zuciyarsa ta dinga ingiza shi ya je ya duba dattijiwan da Samha take jinya.
Kai tsaye wurinta ya nufa ya jawo kujera ya zauna yana dubanta,
“Sannu likita.”
Ta ce da shi tana numfarfashi.
“Mama jikinne?”
Ta girgiza kai ta ce,
“Dakta yunwa nake ji, gashi kudin asibitin ya kare sun ce sallamata zasu yi. Tun dazu Samha ta fita nemo mini abinci har yanzu ba ta dawo ba. Kila kuma ta tafi duba mahaifiyarta ne.”
‘Mahaifiiya! Samha!!’
Ya nanata a zuciyarsa. Maganar ta dake shi, ta kuma tsaya masa a rai. Bai ce komai ba ya mike. Nasis din da suke da duty ya kirawo. Ya rufesu da fada akan don meyasa zasu kyaleta har suna ikirarin sallamarta dan babu kudi?
Tunda suke da shi basu taba ganin ya yi fada haka ba. Mutumin da magana ma wahala take bashi. Duk suka yi ta bashi hakuri.
Kudi ya ciro ya aiki daya daga cikin nas din ta siyo mata abinci da ruwan gora.
Ya ce,
“Za ku iya tafiya.”
A hankali ya dawo zuciyarsa cike da tausayin Inna. Ya matso sosai ya kama hannunta,
“Inna ga dubu goma ki rike kina siyan abinci. Amma banaso ki gayawa jikarki cewa ni na kawo maki. Zaki iya cigaba da zama anan har ki sami lafiya. Ko harararki babu wanda zai sake yi maki.”
Inna ta saka kuka tana gode masa.
Yana ficewa Samha tana shigowa. Inna ta dubeta yadda duk ta fita hayyacinta,
“Samha ya aka yi?”
Samha ta yi kamar zata yi kuka,
“Bansamo komai ba. Ga Mama tana cikin wani hali. Idan Mama ta mutu bazan yafewa kaina ba.”
Ta ciji lebenta ba taso ta yi kuka. Inna ta yi sauri ta ciro kudaden da Dr. Sadik ya ba ta ta mika mata,
“Karbi wannan ki je ki siyo mata magungunan da abincin da zata ci. Nima dazu wani bawan Allah ya bani sadaka.”
Jikin Samha har kyarma yake yi, wajen karbe kudaden tana jujjuya su. Yanzu ba lokacin tambayoyi bane, dan haka ta dibi dubu biyu a ciki ta mayar mata da sauran. Ko Sallama ba ta tsaya yi mata ba, ta fice jikinta yana kyarma.
Magungunan dubu da dari biyar din ta siyo, sai kuma abinci na dari uku da hamsin, da ruwa.
Sai da ta juya hagu da dama, ta tabba tar da babu wanda ke kallonta, kafin ta shige dan lungun. Dogon tafiya ta yi, sannan ta shige wani kango.
“Mama! Mama!! Tashi ga abinci da maganin.”
Har kullum tausayin Samha yana takurawa zuciyar mahaifiyarta. Ta jima ba ta ga yarinya mai kwazo irinta ba. A kullum addu’a take yi Allah ya tsare mutuncinta.
Da kanta ta ba ta abincin, sannan ta ba ta maganin. Ta tallabota ta kaita bandaki, ta yi mata wanka, sannan ta dawo ta gyara makwancinta ta kunna mata turaren wutan da ta tsinto a bolan gidan Alhaji Aminu.
Mama ta dago ta dubeta,
“Allah yayi maki albarka. Allah ya baki masu yi maki.”
Samha ta goge kwallar idanunta sannan ta jinjina kai.
“Mama ki gaya mini su waye danginmu.”
Maman ta dan kauda kai tana jin damuwarta tana ninka ta farko,
“Idan danginmu suka san ina raye kashemu za su yi. Samha ina so ki mance Allah ya taba halittarmu da dangi. Ki kuma yi takatsantsar kada wani yasan muna rayuwa anan.”
Ba ta sake cewa komai ba, ta cigaba da yi mata firfita har ta yi barci.
Dr. Zayyad ne tsugunne agaban mahaifiyarsa.
“Umma ana bibiyan rayuwata.”
Ya furta kansa a qasa.
“Ka hadu da Alhaji Bako ne?”
Dam! Kirjinsa ya buga. A hankali gargadin Alhaji Bako ya fara dawo masa kai,
‘Idan har ka bari iyayenka suka san wannan maganar, Wallahi sai na saka an kona iyayenka da ransu. Zan yi maka ta’asar da zaka sha mamakina.’
A karo na farko ya dago ya dan saci kallon mahaifiyarsa,
“Umma meyasa kika yi mini wannan tambayar? Ko dai akwai wani abu ne da kuke boye mini?”
Umman ta jinjina kai,
“Na tambayeka baka bani amsa ba. Ka hadu da Alhaji Bako ne?”
Bai iya karya ba, bai kuma taba yiwa iyayensa karya ba, baya jin barazanar Alhaji Bako zai saka shi ya fara.
“Eh na hadu da shi.”
A gigice Umma ta tashi zaune tana zare idanu.
“Innalillahi Wa inna ilaihiraji un. Me…Me ya ce maka?”
Izuwa yanzu kansa ya gama kullewa.
“Bamu yi wata magana ba.”
Firgicinta ya jawo yayi mata karya. Karyen da bai taba yi ba. Sai dai ba zai jure ganin mahaifiyarsa a cikin irin wannan razanin ba.
“Kayi hankali da Alhaji Bako.”
Abinda ta iya furtawa kenan. Akwai tarin tambayoyin da yake da bukatar amsarsu. Sai dai a lokacin da yake neman auren Sakina idanunsa sun rufe.
“Umma ku yafe mini kuskuren da nayi maku akan auren Sakina..”
Umma ta dan kauda kanta sannan ta ce,
“Zayyad kaje kayi takatsantsar. Komai ya faru da sanin Allah. Abinda yasa muka kyaleka ka auro Sakina, so muke ka bambance tasirin iyaye da kuma shawarar zuciya. A yanzu aikin gama ya gama. Ka dai yi takatsantsar.”
Ya jinjina kai. Ya tashi da nufin isowa dakin mahaifinsa.
“Kada kaje wurin Alhaji da zancen nan.”
Dakatawa yayi da takun tafiyar da ya fara. Ji yake ina ma shekarun baya zasu dawo? Da ya amince da shawarwarin iyayensa akansa.
Jinjina kai kawai yayi alamun ya gamsu.
“Ka hadu da Alhaji Bako ko?”
Kirjinsa ya buga da karfi! Sallama ce kadai ya yiwa mahaifinsa, sai amsar sallamar ta zamo tambaya, irin wacce mahaifiyarsa ta yi masa.
“Abba..”
Da sauri ya tari numfashinsa,
“Tambayarka nayi Zayyad! Ka hadu da Alhaji Bako?”
Ya hadiye yamu da kyar, sannan ya jinjina kai,
“Ban hanaka amsa duk wata kira da zai yi maka ba? Zayyad!”
Abba ya kira sunansa yana kokarin zura idanunsa a cikin nasa.
“Kana aikata kuskure da gangar! Banaso daga baya ka kira hakan a matsayin kaddararka. Inaso ka kira hakan a matsayin ganganci da rashin hankali. Mace shaidaniya ce, musamman idan ta zama mai son cimma wani buri. Zayyad! Zaka jawo gobarar da zata kona kowa, daga ciki har da ni mahaifinka. Tun farko na nesantaka da Alhaji Bako, amma ka dage sai ka hada jini da shi. Ka daura dammarar yin yakin da zai zama silar tonuwar asirinka damu gaba daya. Sirrin da yayi shekaru fiye da talatin a rufe, a yau rashin hankalinka yana neman ya bude shi.”
Mu je zuwa dai
Zayyad dai ya kasa tantance abinda mahaifinsa yake son sanar da shi. Ya kasa fahimtar wani irin sirri ne wannan? Me yake faruwa a tsakanin Alhaji Bako da mahaifinsa Alhaji Salisu?
Shiru ya yi, a wannan karon ba zai iya furta komai ba, ya yarda ya amince ya yi kuskure. Amma meyasa ba za a ajiye shi a gaya masa abinda ke faruwa ba?
“Abba a zatona a yanzu na yi girman da zan iya shanye kowane irin tashin hankali. Meyasa ake boye min abubuwa irin wadannan?”
Abba yayi taku biyu zuwa uku, ya karaso gabansa, sannan ya dafa kafadarsa,
“Banda wannan Zayyad! Wannan tashin hankalin yafi karfin kwanyar kanka. Kaje ka daura dammara tukuna, sannan ka tunkari abinda kake kira da tashin hankali.”
Zayyad ya mike ya juya da nufin ficewa. Ya zo wurinsu domin ya sami sassauci, amma hakan yana neman gagara.
“Kada ka sake tsayawa da Alhaji Bako.”
Abba yayi maganar cikin kakkausar murya. Bai juyo ba, sai cewa da yayi,
“Insha Allahu zan kiyaye.”
Yana ficewa ya nemi wani wuri ya yi parking motarsa ya hada kansa da sitiyari yana tunani.
‘Akwai wani muhimmin abu da yake faruwa a cikin gidanmu. Waye zai taimaka mini wajen zakulo matsalata? Waye zai ganar da ni abinda matata Sakina take shirin aikatawa akaina?’
“Dan Allah Alhaji ka taimaka mini da sadaka mahaifiyata ce ba ta da lafiya. Kuma yunwa nake ji.”
Ya dago da sauri. Ido hudu suka yi. Nan da nan wani tunani ya zo masa.
“Zo nan kada ki gudu.”
Ta dawo da baya tana kallonsa.
“Zaki iya taimaka mini?”
Ta sake ware manyan idanunta ta watsa masa, alamun ba ta fahimce shi ba.
“Ina so ki dawo gidana da aiki zan taimaka maki.”
Babu dogon tunani ta ruga da gudu ta bace daga wurin. Zayyad ya lumshe idanunsa da suke cike da tashin hankali. Ya tada motar ya koma gida.
“Masoyi ka dawo?”
Ta yi maganar tana cusa kanta a kirjinsa tana bin dukkan ilahirin jikinsa da sumba ta. Bai hanata ba, sai ma kwantar da ita da yayi yana shafa gadon bayanta.
“Ya kike?”
Ya yi maganar kamar bashi ya furta ta ba. Ta langwabe cike da kissa ta ce,
“Ba lafiya ba.”
Ta so ya tambayeta me ya faru, sai kawai ya jinjina kai ya saketa tare da zama a kujera yana rage kayan jikinsa.
Baisan meyasa Samha take yi masa yawo a kwakwalwa ba, baisan meyasa zuciyarsa take gaya masa ita ce mafitarsa ba.
Yana tunanin dole sai ya nemo wacce zata taimaka masa wajen gane hakikanin wacece Sakina.
“In kawo abinci?”
Bai ba ta amsa ba, domin ya lula duniyar tunani.
Mikewa yayi sannan ya dubeta,
“Zan shiga ciki. Akwai aikin da zanyi banason damuwa.”
Ta fahimci me yake nufi, dan haka tayi shiru tana dubansa.
Kyawun Zayyad ya wuce a tsaya kwatance. A kullum kyawunsa da tsarinsa sukan fizgota ta yadda zuciyarta take rawa akan kudurin mahaifinta.
Kafin tasan abin yi har ya shige ya rufe.
‘Ko dai ya gane ne?’
Ta tambayi zuciyarta.
“Me Abba ya gayawa Zayyad?”
Ta sake yin tambayar da babu amsa. Da sauri ta daga waya ta kira lambar Abbanta.
“Hello Abba me ka gayawa Zayyad?”
“Ko me na gaya masa ba matsalarki ba ce. Abinda na sakaki kawai ki yi.”
“Amma Abba ya kamata insan.”
“Rufe mini baki! Jayayya zaki yi da ni?”
Ta hadiye miyau da kyar,
“A’a. A huta lafiya.”
Ta ajiye wayar tana sauke numfashi.
A ranar Zayyad ya kasa runtsawa. Haka kuma tunanin ya tashi yayi Sallah ko kadan bai zo masa ba. Kila hakan ba zai rasa nasaba da abinda ke boye ba.
Washegari tun kafin Sakina ta tashi daga barcin asarar da take yi, ya fice. Bayan ya fito daga tiyata ne ya shigo domin ya tattauna da Inna. Sai dai abin mamaki babu ita babu dalilinta.
Dokto ya juyo a rikice yana duban nasis din,
“Ina wacce take gadon nan?”
Da sauri Nas Jamila ta ce,
“Jiya jikanta ta zo ta matsa sai an sallamesu. Ganin zata tara mana jama’a yasa dokto Saminu ya rubuta masu sallama.”
Zayyad da yaji damuwarsa ta ninku ya rike kansa yana jin tsantsar damuwa.
A daddafe ya duba sauran. Ko a ofishinsa ya kasa tsaye ya kasa zaune sai kaiwa yake yana komowa.
Da sauri ya dauki motarsa ya tafi nemanta a wuraren da yake yawan haduwa da ita. Sai dai ko mai kama da ita bai gani ba.
Ya dawo ya dauki file din tsohuwar, yabi adireshin da suka bayar. Anan ya gane adireshin ma na bogi ne. Ya rasa dalilin da yasa ya damu da lamarin yarinyar.
Kudurtawa yayi aransa ba zai sake nemanta ba. Sai dai kuma me? Duk yadda yaso ya kyaleta abin ya faskara.
Haka zaman gidansa ya gagareshi.
A yau yana zaune a ofishinsa yana rubuce-rubuce. Lokaci zuwa lokaci gabansa yana faduwa, irin wanda bai taba jin irinsa ba.
Ya ji kwankwasa kofa.
“Come in pls.”
Ya furta yana rubuce-rubucensa ba tare da ya dago ba.
“Zayyad Zayyad!”
Da sauri ya dago, sai kuma ya mike tsaye suna kallon-kallo.
“Kayi mamakin ganina ko? Har ka isa ina kiranka baka daga mini kira? In wanke ‘yar in baka, bayan kowa ya hanaka aure, shi ne rashin kunyar zai koma kaina?”
Yanayin Zayyad ya fara canzawa, daga mai biyayya agareshi zuwa mai zafin zuciya. Dan haka ya rungume hannayensa a kirji yana dubansa ido cikin ido.
“Kada ka kureni Alhaji. Ina ganin girmarka ina ganin darajarka, amma kada ka bari..”
“Kai! Dakata! Har ka isa ina fada kana fada? To ko wanda yake tunkahon ubanka ne bai isa ina fada yana fada ba.”
Zayyad ya kafe shi da idanunsa babu ko kyaftawa. Haka zalika bai iya sake furta komai ba.
“Zaka saurareni ko zaka yi mini taurin kai?”
Zayyad ya kwashi keys dinsa da wasu files, har ta gota shi sannan ya dawo da baya,
“Zaka yi danasanin shiga gonata. Zan yi matukar baka mamaki Wallahi! Maganar tsoronka da ake ji, inaso ka cireni daga cikin masu tsoronka. Zan nuna maka ni dan zamani ne.”
Ya fice da sauri ya barshi a ofis din.
Alhaji Bako yayi murmushi yana karewa ofishin kallo. A lokacin yayi saurin cusa masa wani file ya fice da sassarfa.
Yana fita Samha tana cusa kanta ciki. Kasancewar babu sakatariyar. Kamar wacce aka hankada ta nufi wurin file din, ta dauke shi, ba tare da tasan dalilin daukewan ba. Tana dauka ta wuce abinta, ta nufi gida ta ajiye a gefen kan mahaifiyarta. Karshe ma ta dinga yi mata fifita da shi.
Dr. Zayyad ya jima yana kallon cctv dinsa ta cikin computer. Kansa ya daure matuka. ‘Alhaji Bako ya ajiye file, Samha ta shigo ta dauke.’
A lokaci guda ya sake saita idanunsa a cikin computer din yana sake zooming fuskar Samha.
‘Ko dai aljana ce? Ko bakinsu daya da Alhaji Bako? Me ya kawo Samha ofis dina bayan shafe wasu kwanaki da daina ganinta? Meyasa kai tsaye ta nufi file din da Alhaji Bako ya ajiye?’
Amsoshi ne da babu wanda zai iya bashi sai Samha.
‘A ina zan ganta?’
Ya mike tare da rufe computer dinsa ya fice da sauri. Neman duniyar nan yayi amma ya kasa ganin ko mai kama da Samha.
Yarinyar ta fara zame masa masifa kamar yadda ta taba gaya masa.
Dr. Zayyad ya zama abin tausayi, ya kasa samun natsuwa a tsakanin gidansa da kuma gidan iyayensa. A ofis kadai yake dan samun sassauci.
Yau ya fito da sassafe, kamar ance masa ya kalli gefen almajirai, anan ya ga Samha tana bin layin karbar sadaka. Da sauri ya nufi wani wuri yayi parking, sannan ya rufe fuskarsa, ya tafi dan nesa da wurin ta yadda yake iya hangenta ya tsaya.
Bayan ta karbi sadakar kosan, yana kallon yadda take waige-waige kamar wacce ba ta da gaskiya. Sannan ta nufi wani lungu da sauri.
Yaso ya biyota, sai dai yadda take waigowa ya tabba tar masa zata iya ganinsa, da zarar ya biyota.
Yayi ajiyar zuciya. Wani yaro ya kira sannan ya ce masa,
“Dan Allah ko kasan gidansu almjiran can Samha?”
Ya dan yi shiru, daga bisani ya ce,
“Babu wanda yasan daga inda take fitowa.”
Ya jinjina kai,
“Ok. Na gode.”
Bai bi bayanta ba, sai bayan da ya tashi daga wurin aiki, sannan ya nufi lungun da kafafunsa.