Gabadaya dakin kowa ya dauke wuta. Sai aka hau kallon-kallo. Yadda Abba ya sunkuyar da kai kadai ya isa ya nuna maka maganar Alhaji Bala da gaske ne ba karya ba. Nura ya dubi mahaifinsa sosai, sannan ya matso daf da shi,
"Wai da gaske ne Abba?"
Gani suka yi ya goce da kuka. Lamarin da ya karasa sanyaya guiwowinsu kenan. Umma kuma ta dukar da kai tana jin kamar kasa ta tsage kawai ta shige.
Alhaji Bala ya fice cike da tashin hankali.
Samha ta taimakawa Zayyad ya yi wanka, sannu a hankali yake jin tashin hankalinsa yana. . .