Skip to content
Part 6 of 19 in the Series Miskilin Namiji by Fatima Dan Borno

A yau gidajen jaridu suka cika da labarin sace Hajiya Laure mahaifiyar Alhaji Bako.A daren jiya ne da misalin karfe goma sha biyun dare aka sace Hajiya Laure a gidanta. An tabba tar da ‘yan bindiga ne suka saceta.

Dr. Zayyad da ya gama karanta jaridar ya dubi Sakina da ke gefensa tana yanka masa tufa.

“Kika ce bakisan matar nan ba. Gashi naji ance mahaifiyar Alhaji ce. Kuma ni ankawo mini ita asibitina cikin halin yunwa ya gaskiyar abin yake?”

Yayi maganar yana rutsata da kallo. Sakina ta dago tare da leka jaridar cike da mamaki.

“Mahaifiyar Daddy? Gaskiya sai dai idan wata ‘yar uwarsa ce. Amma mahaifiyarsa ta rasu. Kasan shi bayason zumunci, babu mamaki ko kanwar mahaifiyarsa ce. Amma babu yadda za ayi mahaifiyarsa tana raye ace bamu sani ba.”

Bai ce komai ba, ya tashi da sauri. Yau yana bukatar tunkarar Alhaji Bala. Dan haka kai tsaye gidan gonarsa ya nufa.

A can kuwa ya same shi, da wasu murda-murdan mazaa masu gadinsa.

“HaHaHaHa!! Ya akayi kuma ka kawo kanka, kai da nake shirin sakawa a daukoka?”

Zayyad yana nan tsaye kamar bai taba dariya ba, kafin ya ce,

“Ya akayi kawoni ya zama abu mai wahala a wurinka? Kamata yayi daga maganarmu zuwa yanzu har burinka ya cika.”

Alhaji Bako ya cigaba da dariya,

“Naji labarin zaka yi aure, ina tayaka murna. Yaya kazo ne ka gaya mini ka amince da muradina a wurinka? Kada ka mance idan har ka cika mini burina, nayi maka alkawarin sanar da kai ko kai waye, nayi alkawarin warware maka dukkanin wani abu da kake bukatar karin bayani akansa. Aikin da na baka bai wuce mintuna biyar ka kammala shi ba. Me yake damunka ne? Meyasa arziki yana binka kai kuma kana guje masa?”

Zayyad ya harde hannayensa a kirji,

“Wani arziki nake nema a yanzu? Sai dai idan na haram! Kuma bana bukatarsu. Aikin da kake magana akai ko kasheni za ayi bazan taba yi ba. Ka daina farautar rayuwata, ka natsu ka kwantar da hankalinka, da zan tona maka asiri da tun ranar da na nadi muryarka kana wannan maganar da na tona maka. Mai iya kasheni sai ya zo da shiri. Yanzu dai ba wannan ya kawoni ba. Ashe mahaifiyarka tana raye.”

Ya watsa masa jaridar agabansa. Duk abubuwan da akeyi a garin ko kadan bai sani ba. Saboda gaba daya yau bai dauki waya ba, bai kuma bar wata hanya da zai iya samun labarin abinda ke faruwa ba. Su waye suka san mahaifiyarsa ce? Yaushe ma aka saceta?

Zayyad yayi murmushin mugunta. Domin kuwa shi ya saka aka yada jaridun nan a ko ina.

“Ya na ji kayi shiru? Kayi mamaki ko? Kana barci ana yi maka minshari ko? Haka duniyar take, cike take da abubuwan mamaki. Na kasa yarda wai mahaifiyarka ce wannan.”

Alhaji Bako ya mike hannunsa yana kyarma,

“Ka kiyayeni. Wadanda suka fika rashin kunya ma, sun kasa iyawa da ni bare kuma kai. Har ka isa ka hada baki da ‘yan jarida ku ba ta mini suna? Mahaifiyata ta dade da rasuwa kada ka sake dauko wata kace wai mahaifiyata ce.”

Zayyad yayi masa kallon takaici, kallon kayi asara. Duk da hakan wata zuciyar tana son gazgata abinda Alhaji Bako yake cewa. Abu daya yake bukata, shi ne D.N.A test dinnan ya fito. Shi kansa sai yake ganin yayi gaggawa da yawa. Zayyad yayi murmushi sannan ya ce,

“Sau tari abinda kake rainawa sai ya zame maka fitina a cikin rayuwarka.”

Ya juya tare da nufar motarsa. Ko waigowa bai yi ba ya shige motarsa.

Bayason ya kira masu test din, yana son suyi aikinsa yadda ya kamata.

“Hello sir.”

Dr. Zayyad ya dan rage gudun motarsa sannan ya amsa da,

“Ina saurarenka.”

“Sakamakon ya fito.”

Dole ya natsu sosai yadda gabansa yake faduwa, sannan ya ce,

“Mahaifiyarsa ce?”

Dr Salim ya kara kallon takardun sannan ya ce,

“Gwajin nan ya nuna mana mahaifiyarsa ce.”

Wani irin birki Zayyad ya taka. Wanda saura kiris ya bugawa wata mota.

“What! Kana nufin gwajin yayi daidai da Alhaji Bako?”

Ya jinjina kai kamar yana ganinsa,

“Tabbas! Idan ka zo ofis zaka gani da idanunka.”

“Ok. Gani nan zuwa yanzu insha Allahu.”

Alhaji Bako kuwa tun bayan tafiyar Zayyad yake kaiwa da komowa. Kai tsaye ya daga waya ya kira mahaifin Zayyad,

“Hello Salisu. Dakata! Ni nayi maka rana, shine kakeso kayi mini dare ko? Wallahi! Wallahi!! Idan yaron nan ya cigaba da zuwa yana yi mini rashin kunya, zan fasa baragurbin kwan kowa ma ya ji warin. Kasan sai kafi kowa cutuwa ko?”

Abban Zayyad ya danyi shiru, daga bisani ya ce,

“Yanzu me kuma ya faru? Ni fa bansan abinda kake nufi da ni ba, Bako. Ya kamata wannan gabar ta tsaya hakannan, ka fada mini ranar da zanzo mu zauna mu tattauna.”

“Ban sani ba!”

Alhaji Bako ya dakatar da shi a fusace.

Ya cigaba da cewa,

“Gaba da ni da kai yanzu aka fara. Kai ka siya da kudinka, kai ka zabi wannan hanyar kuma akanta zamu cigaba da tafiya. Danka yaje ya binciko mahaifiyata, sannan yasaka duniya ta dauka akan an saceta. Ka kirashi ka gaya masa ya fita sabgata idan kuma ba haka ba, mintuna goma sunyi mini yawa in shafe labarinsa. Ka sanni kasan halina.”

Kit! Ya kashe wayar yana huci.

Abba ya yi shiru, daga bisani ya shiga neman Zayyad a waya. Yana dauka ya rufe shi da fada,

“Idan na isa da kai, ka cire bakinka akan sha’anin Alhaji Bako. Kana bani matsala Zayyad! Akan me ina ganinka a matsayin mai yi mini biyayya zaka canza ka jawowa kanka damuwa? Na gaya maka ka fita a sabgar Alhaji Bako.”

Zayyad ya jinjina kai,

“Insha Allahu zan kiyaye. Allah ya huci zuciyarka.”

Suna ajiye wayar ya kirawo dan jaridan da ya bashi aikin,

“Ku sake dagewa da maganar ba tan mahaifiyar Alhaji Bako. Ku matsa akan har yanzu bai ce komai ba, akan ba tanta. Sannan ku rubuta wadanda suka yi garkuwan sun kira makotanta a waya, sun tabba tar da miliyan dari suke bukatar kudin fansa, amma Alhaji Bako bai bayar da fuskar da za a fuskance shi da maganar ba.”

Duk da dan jaridar ya jinjina maganganun, sai dai babu abinda Zayyad zai saka shi wanda ba zai iya yi ba.

Kwanaki biyu rak! Zayyad ya kunna masa wuta, irin wanda bai taba tunanin akwai mahalukin da zai iya yi masa hakan ba. Gaba daya ya yama haukacewa.

Sakina ta kirashi cikin tashin hankali ta ce,

“Abba da gaske mahaifiyarka tana raye?”

Ya hauta da masifar cewa da tana raye ai da za su sani.

Zayyad yana ta murmushi. Ana cikin tashin hankalin nan ne, Aka tsinci labarin daura auren Zayyad da Samha. Tun lokacin da yakaita wurin Rahama, ko sau daya bai taba zuwa wurinta ba. Idan yayi yunkurin yin hakan, sai wani tunani ya hana shi.

Samha tasha kyau har ta gaji. Tunda aka daura auren ta tubure masu da kuka tana rokar akaita wurin mahaifiyarta ta ganta. Rahama dai da ta ji bazata iya lallashin ba, ta kira Zayyad da yake shirin shiga tiyata.

“Rahama zan shiga tiyata idan na fito zan kira.”

Daga nan ya katse kiran. Ta juyo tana duban Samha. Ta ba ta tausayi sosai,

“Kiyi hakuri tunda anjima za akaiki gidansa kuna tare sai ki gaya masa bukatarki. Idan kina kukan nan zaki ba ta kwalliyarki ne. Tuni ta cizge duk wata kwalliya tana cigaba da kukanta.

Da Rahama da kanwar mamanta suka dauketa sai gidan Zayyad.

Gaba daya Sakina ba tasan wainar da ake toyawa ba, tana can cikin tashin hankalin yadda sunan mahaifinta yake kokarin baci, akan abinda take tunanin sharri ne kawai.

Yau fushinta ya fito fili, jiran Zayyad kawai take yi, ayi duk wacce za ayi. Gwara ayita ta kare wulakancin da yake yiwa mahaifinta abin ya wuce hankali.

Tana nan tana girgiza kafafu taji Sallama. suka shigo tana dubansu cike da mamakin yarinyar da aka lullube da lafiya.

“Bayin Allah ban gane ku ba.”

Anti Rahama ta dinga kallonta tana mamakin tayaya za ace bai gaya mata ba?

“Mun kawowa Zayyad amaryarsa ce.”

Anti Rahama mai karfin hali ta furta. Ba tasan lokacin da ta liliyo wata ashar ta narka masu ba.

“Har kun isa? Wallahi ba nan gidan bane, domin ni kadai ce amarya kuma uwargida dan haka ku je can ku nemi gidan da za a kawo amarya ba nan gidan ba.”

Daga bakin kofa suka ji tsayayyar muryarsa yana cewa,

“Nan gidanne. Dazu ayyuka sunyi mini yawa na mance ban gaya maki.”

Sakina ta dago ta kafeshi da idanu. Bakinta yana rawa hawaye suka shiga aikinsu,

“Dokto nasan wasa kake yi mini. Dan Allah ka daina yi min irin wannan wasan zuciyata zata iya bugawa.”

Ya dubi su Rahama ya ce,

“Rahama ku hau sama bangarenta yana can. Duk da haka ku hau zan zo innuna maku inda bangarenta yake.”

Sakina tayi mutuwar tsaye. Takasa kwakkwarar motsi har sai da ta ji alamun haurawansu sama. Tunda take jin labarin wulakanci ba ta taba jin labari irin nata ba. Ta kasa yin kukan domin kuwa hawayen sun qi fitowa. Sai wani irin suya da zuciyarta takeyi kamar zata fito kirji.

“Ni Zayyad zai ciwa fuska?” Ta nemi wuri ta zauna tana zare idanu. Kamshin turaren wuta ta ji, ya cika kofofin hancinta, hakan ya sake tabba tar mata da tabbas Zayyad aure ya kara. Da sauri ta lalubi lambar mahaifiyarsa, wanda ba zata iya tuna ranar da ta kirata a waya ba. “Assalamu alaikum.”

Umma ta kwarara sallama. Sakina ba ta tsaya wata gaisuwa ba ta ce,

“Umma wai kuna sane da Dokto ya yi auren sirri? Yayi aure ba tare da sanin kowa ba Umma. Umma Dokto yana so ya kasheni ne kawai.”

Umma ta dan yi shiru. Abin ya ba ta mamaki jin cewar Zayyad bai sanar da matarsa ba maganar karin auren. Ta zaci tasani ne, shiyasa ta hana ‘yan uwansa zuwa gidan dan tana gudun aje a sami matsala.

“Hello Umma kina jina?”

Ta katse mata tunaninta jikinta babu inda baya kyarma.

“Ina jinki Sakina. Wallahi bansan bai gaya maki zancen karin aurensa ba, da bazan kyale shi ba. Amma… Dogon tsaki ta jawa Umma wanda ya wuce mata har tsakiyan kanta. Dif ta kashe wayarta tana cewa,

“Munafuka kawai. Aikin banza aikin wofi. Tunda kun saka shi ya kara aure menene na raina mini hankali.”

Ta mike tsaye tana huci.

“Tabbas yarinyar da tayi gangancin shigowa gidan nan ita tafi kowa bani tausayi Walh. Nayi alkawarin sai ta gwammace ta zauna a cikin kabari da ta zauna a cikin gidana.”

Dakinta ta shige ta datse kofa. Ta fara kuka, amma hawayen ya qi ya ba ta hadin kai ya zubo. Da sauri ta lalubi lambar mahaifinta,

“Hello Abba. Wai kaji…”

Ya yi saurin dakatar da ita,

“Nasani mana. Dokto yayi aure ko? To menene abin mamaki? Menene abin tashin hankali? Tashin hankalin da ya sakaki bai kai kwatan kwatan tashin hankalin da ya jefani a kwanaki biyu ba. Ya jawo mutanen duniya suna tsine mini akan matar da yakirawo da mahaifiyata. Duk kayayyakin da kamfanina suke kawowa kaso tamanin sun daina siyan kayayyakina, a cewarsu ni azzalumi ne. Ya jawo mini dumbin asara. Shiyasa na gaya maki kasancewar Zayyad a raye, tamkar barazana ce a cikin rayuwata. Ni da nake da burin zama mai kudi na biyu ko na daya a africa, yau gashi Rai daya tak! Yana neman ya mayar da ni, kashin baya. Kasuwancin da nake tattalinsa ya jawo mini muguwar asara. Dan haka idan baki kashe shi ba, shi zai kasheki. Dan ni tuni na samo hanyar maganinsa.”

Dif ya kashe wayar. Ta saka kururuwa tana kuka tana bige-bige kamar mahaukaciya. Kiran mahaifiyarta ne yake shigowa babu kakkautawa. Tana kallo ta qi daga wayar dan tasan nasiha zata yi mata, ita kuwa a yanzu mai zigata ta hau sama ta kashe yarinyar nan kawai take nema.

A ranar wuni tayi ba ta ci ba, ba ta sha ba. Ta zama kamar mahaukaciya sabuwar kamu. Shi kansa bai sake bin ta kanta ba. Bayan su Anti Rahama sun tafi Samha ita kadai ta rage a sashenta. Sai zazzare idanu take yi kamar tsohuwar mayya. Ga yunwa da take ji.

Tun tana jin tsoro har ta dan saki jikinta. Kewar mahaifiyarta kawai take yi, taso suna tare a cikin daular nan.

Sakina ta kasa hakuri, bayan ta tabba tar Zayyad baya gidan, ta fito tana zare idanu. Kai tsaye saman ta haura tana huci kamar zaki.

“Ina kike! Ina kike nace?”

Ga mamakinta sai ganin Samha tayi tamkar wacce ba ta taba dariya ba ta harde hannayenta a kirji tana watsa mata kallon rainin wayo,

“Gani nan lafiya kike yi mini irin kiran nan kamar nayi maki sata?”

Sakina ta janye mamakinta ta ce,

“Ina fatan kin shirya zaman kabari? Domin gidana tamkar cikin kabari ne.”

Samha tayi dariya sosai sannan ta janye dariyar ta ce,

“Harda likafani na shigo karshen shiri kenan. Sai kuma mene?”

Baki bude Sakina ke kallonta. Kafin ta sake sanin abin cewa Samha ta shige ciki ta datse kofar tana jan tsaki.

Guiwowin Sakina suka saki, ta tabba tar Zayyad ya auro wutan da zata konasu su dukka. A karo na farko gabanta ya fadi da karfi. Kyawun Samha yafi komai jan hankalinta. Yarinyar ba ta da makusa, sai dai kalamanta sun girmi shekarunta.

Haka ta cigaba da zage-zage tana tsine mata. Amma Samha ko kadan ba ta fito ba. Dole ta gaji ta sakko tana tsoron Zayyad yazo ya sameta. A falo ta zauna tana huci. Daurin kirji ne kawai a jikinta. Idanun nan sunyi jazir saboda azaban kuka. Wanda a farko ta nemi hawayen ta rasa, sai daga baya.

Da Sallama ya shigo hannunsa dauke da ledoji. Ganin Sakina ya fahimci yau akwai tashin hankali. Sai dai ya shirya mata.

Ajiye mata ledar yayi,sannan ya haura sama. Kwankwasa mata kofar yayi a hankali. Hakan yasa ta bude. Duk suka dubi juna. Duk da hijabine a jikinta, kyawunta ba karamin mamaki ya bashi ba. Sai yake ganin tamkar an sauya masa ita ne. Dama dazu tana cikin lullubi bai samu ya kalleta ba. Ita ta fara kauce masa. Ya shiga ciki ya ajiye mata ledar.

“Na barki da yunwa ko?”

Yayi maganar yana tsareta da manyan idanunsa. Ganin ba zata yi magana ba, ya saka shi jawota jikinsa ya cusa hannu cikin rigarta yana shafa shafaffen cikinta.

“Yunwa kike ji Samha.”

Ji tayi babu wanda ya iya kiran sunan kamarsa. Sai dai yadda yake shafe mata ciki ya sakata fara mutsu-mutsu jikinta yana rawa. Ya kula da hakan dan haka shima yayi saurin sakinta yana jin wani abu yana yawo a jikinsa.

“Ki ci kisha dukkan lemukan da kike so. Sai kiyi wanka ki kwanta. Zan barki ki huta.”

Ta gyada kai tana kallonsa ya fice. Kamar ta ce masa bazata iya kwana ita kadai ba. Sai kuma ta daure, domin shi kansa tsoro yake ba ta, tana jin shakkar yace zai yi mata wani abu, bayan a cikin yarjejeniyarsu babu maganar wani abu da zai ratsa a tsakaninsu.

Sakina tana nan a falon kamar sabuwar kamu. Ya ji tausayinta sosai. Ya dubeta,

“Ki tashi mu je mu kwanta.”

Ta dago a razane tana kallonsa. Ta ci burin sai cikin dare zata kona shi, shi da amaryarsa. Sai kuma ga maganar da ba ta taba zato ba.

<< Miskilin Namiji 5Miskilin Namiji 7 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×