Skip to content
Part 1 of 36 in the Series Mu'azzam by Fatima Dan Borno

Shimfiɗa

Kwance take a cinyar Gwaggo, tana lumshe idanu saboda tsifan da Gwaggon take yi mata. A duniyar Husna babu abinda take so sama da ace za a tsefe mata kai, musamman idan Gwaggo ce, dan tana yi tana yi mata susa.

A gefe guda Salma ce take karanta masu littafin Hausa, labarin littafin ya yi matuƙar tafiya da ita.

Duk da sanyin da ake dokawa, cikin ɗakin Gwaggo a wadace yake da ɗumi, kasancewar ɗakin baya rabo da garwashin wuta. Salma ta ɗago daga karatun da take yi ta ce,

“Gwaggo wai marubutan nan kullum matsalarsu akan namiji ɗan gata ne baya laifi?”

Gwaggo ta yi murmushi irin nasu na manya. Duk da damuwa ce dankare a fuskarta hakan bai sa ta iya bari sun fahimta ba.

“Marubuta suna rubuta hasashensu ne. A nufin su mazaje duk su zama na ƙwarai haka ma matan.”

Ta bata amsa ba tare da ta dubeta ba. Gaba ɗaya tunaninta ya tafi wani wurin. Idan bata yi ɓata a lissafinta ba, rabon da ta sanya ɗanta a idanunta yau wata huɗu kenan. Duk dauriya irin na Gwaggo wannan karon tana ji a zuciyarta ta gaza.

Husna ta gyara kwanciyarta tana sake naɗewa a jikin Gwaggon kamar mage. A lokaci guda kuma siririn hancinta sarkin jin ƙamshi, ya shaƙi wani ƙamshi mai sanyi wanda ya haddasa mata lumshe idanu, a lokaci guda kuma tunaninta ya fara sanar da ita ma malllakin ƙamshin, hakan yasa ta ɗan zaro idanu cike da tsoro.

Matansa biyu Anti Amina, da Anti Bilki suka fara shigowa, kowacce ta yi ado da kaya masu kyau da tsada. Da sauri Husna ta tashi zaune tana dubansu ɗaya bayan ɗaya. Gwaggo kuwa kamar an aiko mata da saƙon mutuwa, dole ta ɗan yi masu yaƙe tana duban bakin ƙofa.

Mu’azzam bai shigo ba, sai da suka ɓata lokacinsu kamar yadda suka saba, da shi da ta gaban goshin nasa, sannan ya shigo fuskar nan kamar anyi gobara.

 Kai tsaye kusa da Gwaggo ya zauna yana dubanta cike da so da ƙauna irin ta ɗa da uwa. Salima ta nemi wuri kusa da ‘yan uwanta ta zauna tana duban wayarta.

Gwaggo ta kauda kanta alamun tana fushi da ɗanta. Sassanyan murmushinsa ya jefeta da shi, a lokaci guda ya kai hannunsa kan rushin, sai da ya tabbatar ya yi ɗumi sannan ya janye hannun zuwa bisa ƙafafunta yana dannawa. Hakan yasa ta dawo da ganinta gareshi, duk suka yi wa juna murmushi.

Ita kanta tasan ba zata iya fushi da Mu’azzam ba, shi kaɗai take gani ta ji sanyi a ranta. Da ta ganshi sai hoton mahaifinsa ya faɗo mata a rai. Har gobe tana jin ciwo idan aka amci sunan masu garkuwa da mutane. Tana jin ko zata yafewa kowa ba zata taɓa yafe masu ba.

Gaba ɗaya matan suka haɗa baki wurin gaidata. Idanunta akan Mu’azzam ta amsa tana sake duban yadda duk ya rame. Babu wanda zai kalle shi yace wai shi ya tara waɗannan matan masu kama da giwaye.

Salma da Husna suka gaida su. Cikin isa da izza suke amsawa kamar waɗanda aka sanya su dole sai sun amsa.

Gwaggo ta dube su ta ce,

“Ku tashi kuje sasan Babban mutum, ku gyara masa. Zuwa babu sanarwa.”

Tana maganar tana kauda kai, sakamakon hawaye da suka cika mata idanu. Jikin Mu’azzam ya gama yin la’asar, ya fi kowa fahimtar mahaifiyarsa don haka ya fahimci kuka take son yi.

Duban matansa ya yi a natse sannan ya dawo da dubansa ga Salma wacce ita ce bata ƙarasa fita ba,

“Ku je mota ku kwaso kayayyakinmu.”

Ya dawo da dubansa ga Gwaggo, ba tare da ya damu da amsawar da Salma ta yi ba.

“Gwaggo ki kwantar da hankalinki. Na sami hutu don haka anan zamu yi maki hutun mako biyu insha Allahu, sai kin gaji da ganina.”

Gwaggo ta ji maganar tasa a bazata, don haka ta dubi fuskokin matansa a karo na farko tun zuwansu, ta ga kowacce fuskarta babu fara’a, don haka ta gazgata zancensa.

Anti Amina ta fara tashi ta fice fuskar nan kamar gobara, sai Anti Bilki ta bi bayanta. Ya so ƙwarai Salima ta tashi ta basu wuri, amma sai ya ga tana sake danna wayarta ba tare da ta ɗago ba. Ba zai iya ce mata ta tashi ba, dole ya dawo da kallonsa agun Gwaggo da take faman ƙare masa kallo cike da tausayawa.

“Babban Mutum ka rame da yawa. Ko aikin naku ne?”

Ta tambaye shi, tare da kai hannu ta shafi wuyansa, tana jin tarin damuwa yana sake lulluɓeta.

Sai da ya kama hannayen ya riƙe su tsam a cikin nasa, yana jin ya yi kewar irin wannan kulawar da mahaifiyarsa kaɗai take bashi, ya ƙurawa yatsunta idanu. Daga yatsun ƙafafunta har na hannayenta duk irin nasa ne, sau tari idan yana jin damuwar rashinta kusa, yakan kafe yatsun hannunsa da idanu, a lokaci guda kuma sai ya kai hannun fuskarsa yana shafa, alamun lallashi irin wanda Gwaggo take yi masa, da zarar ta ganshi cikin damuwa.

“Gwaggo babu abinda yake damuna. Na yi matuƙar kewarki ta yadda bakina ba zai iya kwatanta maki ba. Gwaggo ki yafe min rashin zuwana akan lokaci.”

Gwaggon ta ji sanyi sosai a zuciyarta, don haka ta yi dariya. Wannan karon dariyar tun daga zuciyarta ta fito.

“Babu komai. Yanzu dai bari Husna ta zo ta dama maka fura kafin a ɗora abincin.”

Yana murmushi ya dubi Salima ya ce,

“Ki tashi ki je ki huta, ina ganin sun kammala gyara  ɗakinki.”

Bata so haka ba, taso ta zauna ta ji me Gwaggo take son cewa akansu. Dole ta miƙe ta fice kawai. A lokacin Mu’azzam ya gyara zamansa sosai ta yadda suke fuskantar juna da Gwaggo. Ya dubi fuskarta yadda ta sauya a lokaci guda, daga barin dariyar zuwa ɓacin rai.

“Yanzu Babban Mutum waɗannan tuma-tuman matan ka ajiye a gidanka? Mata har uku amma babu amfani? Naci burin inga ‘ya’yanka a duniya. Ita Salman da ta zama jakarka itama baka ga irin kallon da take yi min ba? Babu wanda zai kalleka ya dubi matanka yace wai matanka ne. Sun saki jiki suna cin daɗi sun narka uban ƙiba.”

Mu’azzam ya sani sarai, dukka matansa babu wanda Gwaggo take jituwa da ita. Gara ma amarya Amina, a waya sukan ɗan yi magana, amma idan aka ce za azo wurin Gwaggo ta fi kowa jin haushi dan ta tsani zama a ƙauye sosai, duk kuwa da yadda gidansu Mu’azzam ya fita daban a cikin ƙauyen.

Muje zuwa. Yanzu aka fara.

Fatima Ɗan Borno

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 2.6 / 5. Rating: 34

As you found it interesting...

Follow us to see more!

Mu’azzam 2 >>

7 thoughts on “Mu’azzam 1”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×