Husna ce duƙe a gaban Gwaggo ta zuba mata idanu tana son dole sai ta karanci a yanayin da take,
"Gwaggo tuntuni nake yawan ganinki cikin damuwa, a zatona saboda wannan abin da ya faru da ni ne, shiyasa naci alwashin zan kiyaye duk wani abu da zai sa ki ganni a cikin damuwa. Babban burinki a kullum ki aurar damu. Gwaggo yau burinki ya cika, me kuma kike nema?"
Gwaggon ta kasa magana sai kallon tausayi take yi mata, hakan yasa Husna sunkuyar da kanta ƙasa tana jin baƙin cikin abin da kullum idan ta tuna sai. . .