Skip to content
Part 12 of 36 in the Series Mu'azzam by Fatima Dan Borno

Husna ce duƙe a gaban Gwaggo ta zuba mata idanu tana son dole sai ta karanci a yanayin da take,

“Gwaggo tuntuni nake yawan ganinki cikin damuwa, a zatona saboda wannan abin da ya faru da ni ne, shiyasa naci alwashin zan kiyaye duk wani abu da zai sa ki ganni a cikin damuwa. Babban burinki a kullum ki aurar damu. Gwaggo yau burinki ya cika, me kuma kike nema?”

Gwaggon ta kasa magana sai kallon tausayi take yi mata, hakan yasa Husna sunkuyar da kanta ƙasa tana jin baƙin cikin abin da kullum idan ta tuna sai ta yi kuka. Ta kasa mance daren nan da ta kira da baƙar dare.

Sai yanzu ta tuna ashe fa tun ranar da ta haɗu da angon nata, ranar ɗaurin aurensu bata sake sanya shi a idanunta ba, bata sake jin ko waya ya yi ba.

“Gwaggo Kabiru bai sake waiwayoni ba. Allah dai yasa ba aure irin na Yaya Salma zan yi ba.”

Sai yanzu Gwaggo ta ɗago cikin mamaki da al’ajabi gami da firgici ta dubi Husna,

“Wani irin aure Salma ta yi? Gaya min.”

A lokaci guda ta fahimci ƙaton wautan da ta yi, don haka ta sunkuyar da kai ta ce,

“Ina nufin kishi da su Anti Bilki.”

Duk da hakan Gwaggo bata yarda ba, ta dubeta sosai ta ce,

“Husna gaya min gaskiya. Kun taɓa tattaunawa da Salma akan auren Babban mutum ne? Ta taɓa gaya maki baya sonta ne?”

Girgiza kai ta yi da sauri,

“Wallahi Gwaggo bata gaya min haka ba.”

Sassanyar ƙamshinsa ya yi masu sallama. Gaban Husna ya faɗi ras! Ta ɗago suka yi ido huɗu da shi, cikin shigarsa ta ambassador getzner. Launin kayan sun yi matuƙar dacewa da launin fatansa.

Ko ba a tambaya ba, kusa da Gwaggo yake shirin ƙarasowa. Hakan yasa Husna ta ɗan kauce masa gudun kada jikinsu ya haɗu.

Yana ƙarasowa ya durƙusa tare da ɗora hannayensa a jikinta yana sake dubanta a natse,

“Mahaifiya…”

Ya kirawo sunanta a hankali, wanda rabon da ya kirata da hakan har ya fara mancewa.

Duk da ya yi mata kyau sosai, hakan bai hanata hango ramar da ya yi ba. Cike da zumuɗin son jin lafiyar Salma Husna ta gaida shi. Yana amsawa ta ɗora da cewa,

“Uncle M.Y ina Yaya Salma? Don Allah ki kirawo min ita kaji?”

Yadda ta yi magana yasa shi zuba mata idanu, wanda shi kansa ba zai ce ga dalilin kallon da yake yi mata ba. Duk da yakan danganta hakan da tsananin tausayinta da yake ji.

“Salma tana nan lafiya.”

Ya bata amsa a takaice yana sake duban fuskar Gwaggo. Sai a sannan ta saki ajiyar zuciya ta ce,

“Yau kuma kai ne da zuwan bazata? Ke Husna kawo masa kujera sannan ki yi sauri ki damo fura.”

Husna ta tashi ta ɗauko kujera, ya karɓa ya zauna, sannan ta wuce ciki ta ɗauko furar ta dawo bakin ƙofa ta zauna tana damawa. Sannan kuma tana sauraren hirarsu, don ta sha jinin jikinta akwai matsala.
Sai da Gwaggo ta waiwayo ta dubeta tana mamakin yadda Husna take ƙaunar jin gulma. Shima ita yakai wa duba sannan ya yi murmushi.

“Gaya min abin da ke damunka.”

“Babu abin da ke damuna da ya wuce yanayin ayyukanmu. Ina ji kamar in ajiye aikin.”

Murmushi mai sauti Gwaggo ta yi, sannan ta ce,

“Da aikin nan kake taimakon na ƙasa da kai. Bana goyon bayan ka ajiye aikinka. Ina Salma tana lafiya ko?”

Sai da ya ɗan sosa kansa sannan ya ce,

“Eh tana lafiya. Sai dai ban sauketa a gidana ba, wani wurin na kaita kafin a gama gyaran ɓangarenta.”

Gwaggo ta jinjina kai. Tsalam suka ji muryar Husna ta ce,

“Kira min Yaya Salma ingaisheta.”

Babu musu ya jawo wayarsa ya latsa sannan ya miƙa mata. Sai da ta ajiye kwanon furar a gabansa sannan ta karɓa tana jin farin ciki yana ratsata.

A yadda ta ji muryar Salma babu wata alama ta damuwa ko ɓacin rai. Hakan ya sanyaya zuciyar Husna, har ma ta furta a bayyane,

“Alhmdllh Yaya kin ji daɗi abinki. Ni kuwa har yanzu babu idanun Kabiru. Ko haushi ya ji dan Uncle ya korani cikin gida?”

Salma ta girgiza kai kaman tana ganinta,

“A’a bana tunanin hakanne. Ai sati mai zuwa kema za a dawo da ke kusa da ni.”

Husna ta ji daɗi a yadda ta ji Salma tana cikin ƙoshin lafiya. Tana kashe wayar ta sake duba gaba da bayan wayar ta yi mata kyau sosai. A lokacin saƙo ya shigo ciki, fes ta fara karantawa,
‘Yanzu yaji kayi mana a gidan? Wallahi idan baka dawo ba zan bar maka gidanka.’

Da sauri ta kai masa wayar tana kallonsa. Shima ita ya kalla gabansa yana faɗiwa. Bai duba wayar ba ya mayar da ita aljihu.

Jujjuya maganar take yi, wai namiji da yaji… Bata taɓa ji ba, ta fi dai sanin mace ke yin yaji ba namiji ba. Ta taɓe baki tana cewa,

‘Oho dai! Indai Yayata tana cikin ƙoshin lafiya kun daɗe baku tafi ba. Mugaye kawai.’

Sai da ya tabbatar ta shige sannan ya dubi Gwaggo da kulawa,

“Gwaggo Kabiru bai sake waiwayoku ba? Kafin inzo nan sai da naje gidansu. Antabbatar min tun ranar bikin babu wanda ya sake sanya shi a ido. Nasan dole Husna zata dinga damunki da tambayoyi ko da kuwa bata sonsa dole zata so taga mijinta kusa. Ko kuwa bata yi maki wata magana ba?”

Gwaggo ta gyara ɗaurin ɗankwalinta da ke ƙoƙarin karkacewa ta ce,

“Yanzu kafin ka shigo ta tambayeni ina Kabiru. Ka bar maganar nan kawai Babban mutum anjima zamu tattauna akai. Ina sauran iyalanka suna nan cikin koshin lafiya ko?”

Girgiza kai ya yi,

“Gwaggo ji nake kamar duk inrabu da su inhuta. Na gaji da hayaniyarsu. Tunda akace anyi auren nan zaman lafiya ya kau a cikin gidana.”
“Uhum! Icce tun yana ɗanye ake tanƙwara shi. Ka riga kayi kuskure. Tun farko ka sakarwa matanka abubuwan da bai kamata ka sakar masu ba. A yanzu kuwa dole kayi haƙuri da komai da ke faruwa.”

Jinjina kansa ya yi, yana jin gaskiya Gwaggo ta faɗa. A natse ya yi mata tambayar da shi kansa baisan lokacin da maganar ta fito ba.

“Gwaggo wani laifi zaki kamani da shi ki kasa yafe min?”

Murmushi ta sakar masa,

“Bana jin zaka iya aikata irin laifin da ko mahaifina yake aikata shi ba zan iya sake kiransa da uba ba. Ka ga zina? Ka ga shaye-shaye? Ka ga ɓarawo? Manyan laifukan nan guda uku su zaka yi min inkasa kallon ko da gawanka ne. Na jima ina yi maka addu’a kuma Allah ya karɓi addu’ata tunda ya yo ka a cikin masu mutunci da ƙima.  Ko da yake duk da addu’ata ya taimaka maka. Bana barci ba tare da na yi maka addu’a ba. Ƙila sakacin iyaye ke sanya ‘ya’yansu lalacewa. Bana fatan Allah ya tsaidani ya tambayeni yadda na kiwata amanar da ya bani inkasa bayar da amsa.”

Gwaggo kaɗai ke jawabi, amma shi kansa baisan a duniyar da yake ba, gumi kawai yake haɗawa duk da garin babu zafi. Tunda yake bai taɓa jinsa ya jiƙe sharkaf ba, kamar yau ɗinnan. Da za ace ya tashi ya shiga ciki ya tabbata da ko motsa yatsun hannunsa ba zai iya yi ba.

Gwaggo tana ta surutai daga ƙarshe ta ce,

“Insha Allah yadda ka faranta min, ka tayani tarbiyyar kanka haka zaka sami ‘ya’ya da za su yi maka haka.”

A zuciyarsa ya dinga maimaita ‘Ba Ameen ba Gwaggo ba Ameen ba.’

Kwata-kwata bata kula da halin da yake ciki ba, ta tashi tana cewa,

“Kaje ka huta, yanzu za ayi maka tuwo Husna zata kawo maka.”

‘Husna!’ ya maimaita sunanta a zuciyarsa da ƙarfi. Me zai sa Husna ta kai masa tuwo? Idan akwai abin da ya tsana a duniya bai wuce ganin Husna a gabansa ba. A yanzu baya son yarinyar tana kusanto inda yake bare har wata magana ta haɗa su.

Ya kai minti talatin yana zaune a wurin, jikinsa babu inda baya rawa… Ji yake kamar Gwaggo ta sakar masa magana ne, ji yake kamar asirinsa yana gab da tonuwa ne. Indai hakane da ya ga ranar da mahaifiyarsa zata tsine masa ta juya masa baya, gara ya guji kowa ya nesanta kansa da masu tsafta. Domin ya sani lokaci ya ƙure masa.

Sannu a hankali ya fara dawowa cikin hayyacinsa, sannan ya dafa bango ya shige ɓangarensa.

Abin mamaki Husna ta share masa wurin ta kunna turare. Yarinyar kamar aljana babu wanda ya ga wucewarta.

<< Mu’azzam 11Mu’azzam 13 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×