Skip to content
Part 13 of 36 in the Series Mu'azzam by Fatima Dan Borno

Banɗaki ya wuce ya sakarwa kansa ruwa cike da tashin hankali. Duk yadda ruwan ke sauka a jikinsa, hakan bai hana shi jin zafi ba. A yanzu kuma danasanin zuwansa garin yake yi. Sai ya gwammace da ya zauna da su Salima su yi ta haukansu fiye da ya zauna kusa da mahaifiyarsa. Ji yake ina ma bawa yana iya goge baya? Da ya zama mutum na farko da zai goge baƙar ƙaddararsa ta koma fara tas!

Jiki babu ƙwari ya fito ɗaure da tawul ya zauna shiru a gadonsa. A lokacin Husna ta shigo da ƙaton hijabinta tana ganinsa a haka ta fice da gudun tana haki. Gaba ɗaya miyan da ta riƙo ya ɓata mata gaban hijabi. Shi abin ma yaso ya bashi dariya.

Gwaggo ta dubeta ta ce,

“Ke lafiya lau kike kuwa?”

Asanyaye ta ce,

“Gwaggo miyar ce ta zube. Zan sauya hijabi ne insanya masa wata.”

Bata ce mata komai ba, ta ci-gaba da can carbinta.

Wannan karon a falo ta ajiye masa komai ta wuce abinta. Sai fitowa ya yi ya ga kayayyakin abincin. Cokali ɗaya ya kai baki, ya ji kamar maɗaci. Komai bayayi masa daɗi. A ɗan gaggauce ya fice ya wuce masallaci.

*****

Daga Islamiyya ta dawo, wanda babu wanda ya hanata zuwa, anan ta iske motoci biyu. Ko ba a  gaya mata ba tasan motar Kabiru ne da ta Mu’azzam. Bata san dalilin da yasa ta ƙarawa tafiyarta sauri ba. Sai dai da tasan abin da kunnuwanta za su jiyo mata kenan da babu ko shakka ba zata taɓa neman sani ba, bare har ta maƙale a bakin ƙofa.
“Amma yanzu tunda gamu munzo sai ki warware mana komai. Ni bana gari bansan da maganar fasa auren Kabiru da Husna ba.”

Cewar Bappa Sani. Gwaggo ta gyara zama tana dubansu idanunta jajir ta ce,

“Kana ji ko? Kabiru bashi da imani. Tun ranar da wannan abu ya faru na kula da take-takensa. Ƙaddara tana kan kowa. Yafi kowa sanin Husna marainiya ce, amma sai ya fara wulakanci saboda ƙaddara ta hau kanta anyi mata fyaɗe… Duk da Kabiru yasan ina da hawan jini, hakan bai hana shi wulakantani ba.”

Gwaggo ta ɗan dakata tana jin zuciyarta tana ƙuna. A sanyaye ta ci gaba da cewa,

“Tun Husna tana asibiti babu kunya ya kirawoni ya ce min, shi ba zai iya auren ragowar wani ba. Inyi haƙuri innemawa Husna wani mijin, ya yarda bayan ta yi aure zai jira har ta fito ya aureta a matsayin bazawara. Wai shi idan ya kwanta har ganinta yake yi a lokacin da wani ƙato yake keta haddin matar da zai aura. Ya ƙara da cewa ko ya aureta zarginta kawai zai dinga yi.”

Gwaggo Sahura da Bappa Sani suka sa Salati da ƙarfi. A lokacinne kuma ƙafafun Husna suka gagareta tsayuwa saboda rawa da suke yi. Tunda take jin munanan kalamai bata taɓa jin masu zafi da tsayawa a rai kamar na yau ɗinnan ba. Rintse idanunta ta yi hawaye wani na bin wani.

Muryar Gwaggo ta sake ji tana magana cikin damuwa,

“Da na fara roƙonsa sai ya kama ce min wai incire son zuciya idan ɗana ne zan yarda ya aureta? Maganganunsa sun yi min zafi, sai dai ban kai ga bashi amsa ba Babban mutum ya shigo ya ci kwalar rigarsa. Ganin abin zai jawo tashin hankali na shiga tsakaninsu. Anan wurin na dubi babban mutum a gaban Kabiru nace masa na bashi izinin ya auri Husna. Bai yi min musu ba ya amince, duk da dama bai taɓa yi min musun ba.”

Ɗakin ya ɗauki shiru. Zuwa can Gwaggo ta share hawayenta ta ci gaba da cewa,

“Duk abin da Allah ya rubuto sai ya faru. Muka lallaɓa Kabiru akan ya ci gaba da neman auren Husna kada ta gane ta shiga wani hali, haka kuwa akayi ya dinga zuwa a matsayin masoyinta na tun yarinta. A zatona ya sanar da ku komai, don haka na sami Salma na gaya mata duk yadda ake ciki ta nuna min dama akwai Sahibi da yake sonta, don haka akayi masa magana kuma cikin ikon Allah ya turo iyayensa. Don haka a wannan rana Babban mutum ya zama mijin Husna, Sahabi kuma ya auri Salma. Gudun Husna ta gane komai nasa Babban mutum yakai Salma ɗakin mijinta. Har yanzu da nake wannan maganar Husna bata san cewa Kabiru ya gujeta ya ƙyamaceta a lokacin da take da buƙatarsa ba. Sai yanzu kuma zaku taso shi a gaba? Ai aikin gama ya gama.”

Da ace zata iya kashe kanta, da babu ko shakka sai ta kashe kanta a yau kuma a yanzu. Duk da karkarwar da jikinta ke yi mata, hakan bai hanata tashi da ƙyar ta buɗe labule tana dubansu ba. Duk jarumta irin na Mu’azzam sai da ya ji zuciyarsa tana rawa.

“Gwaggo dama Kabiru guje min ya yi? Don Allah Gwaggo na taɓa yin wani abu da ya saɓawa tarbiyyar da kika bani? Yanzu Uncle Shi ne mijina? Me ya sa baku gaya min ba? Me ya sa zaki kaini gidan da ko Yayata ya fi ƙarfinta bare kuma ni? Yanzu… Yanzu… Saboda ƙaddarata ake gudu…”

Ta kasa ƙarasawa sakamakon wani jiri da ya ɗebeta. Zata faɗi ƙasa Mu’azzam ya yi saurin tarota. Kabiru ya miƙe da nufin riƙeta Mu’azzam ya nuna shi da yatsa,

“Kada ka kuskura ka taɓa ta, dan zan iya sauya maka kamanni. ‘Yan uwana suna cikin farin ciki ka shigo ciki ka tarwatsa masu. Da ace baka zo ka ce a cireta a makaranta ayi mata aure ba, bana jin Gwaggo zata yi tunanin aurar da ita, bare har ka ɗauketa a motarka Ka biyo hanya mai hatsari a cikin dare ka kaita zuwa ga ƙaddararta ba. Na fi jin zafinka Kabiru akan kowa.”

Gwaggo dai sai ƙoƙari take tana shafawa Husna ruwa har zuwa ajiyar zuciyar da ta yi.

Kabiru da Gwaggo Sahura, da Bappa Sani suka miƙe kowannansu guiwarsa a sake.

A ranar har zuwa dare ankasa gane kan Husna, taƙi cin abinci sai kuka kawai take yi. Sai yanzu take jin ta tabbata mareniya, sai yanzu take jin babu wani namiji da zai sake ganin martabarta. Da ta tuno da su Bilki da irin rayuwarsu sai ta sake fasa kuka.

Shi kuwa ji yake gara ya sake tattarawa ya koma inda ya fito tun kafin zuciyarsa ta buga. Yana cikin haɗa tarkacensa Gwaggo ta shigo kai tsaye, saɓanin da da idan zata yi magana da shi sai dai ta aika.

“Babban mutum ka ɗauki Husna ka tafi da ita. Idan tana ganina anan ba zata haƙura ta karɓeka a matsayin miji ba, amma idan acan take tasan bata da kowa sai kai.”

Dakatawa ya yi da abin da yake yi, ya dinga kallon Gwaggo kamar ya ce mata ta yi hakuri yau zai yi mata musu. Sai dai har abada Gwaggo ta wuce hakan a wurinsa don haka ya ce,

“Duk yadda kika ce haka za ayi Gwaggo.”

Ta fahimci sarai baya son hakan, amma sai ta kauda kanta ta koma ta sami Husna.

“Tashi ki sauya kaya ki wuce ki bi mijinki. Kuma kada ki kuskura ki ce zaki yi min musu.”

Abin da Gwaggo bata sani ba, tuni Husna ta amincewa kanta a yanzu rayuwar maraici zata yi. A hankali ta sauya kaya ta ɗauki hijabi tasa, ta ɗauki Alqur’aninta da Gwaggo ta bata, ta rungume tsam a jikinta.

Jikin Gwaggo ya ƙarasa mutuwa, sai dai babu yadda zata yi dole ta hakanne kaɗai zata iya gyara komai.

Dukkansu suna durƙushe a gaban Gwaggo tana yi masu nasiha mai ratsa jiki, daga bisani tasa masu albarka suka kama hanya.

Dukkansu babu wanda ya ce da ɗan uwansa ci kanka, ita dai Qur’aninta kawai ta buɗe tana karantawa a zuciyarta. Shi kuwa tunani ne fal a cikinsa na yadda zai ƙare da matansa.

Juyowa ya yi domin ya ga a yanayin da take, sai yaga tana kuka, hakan ya sa ya sake kauda kansa.

Ganin dare ya yi masu a hanya ya nufi wani hotel da ninyar su kwana, gaba ɗaya baya son abin da ya faru da Husna wancan karon ya sake faruwa da ita. Har ya je ya kama wuri ya dawo tana zaune shiru. Wani irin haushinta ya kama shi, (Taurin kai kamar mai sunan.)

“Fito muje.”

Babu musu ta fito suka shiga ciki. Sai a lokacin ta fahimci me yake nufi. Ta dinga kallon ɗakin tana son ganin ta yadda za ayi ta iya kwana ɗaki ɗaya da wani ƙato.

<< Mu’azzam 12Mu’azzam 14  >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×