Da isar Gwaggo gidan Dakta Salim matarsa mai kirki ta karɓe su hannu bibbiyu. Ɗaki ɗaya suka ajiye Gwaggo a ciki. Sai dai ta kasa cin komai, ta kasa magana. Da zarar zata buɗa baki ta yi magana sai hawaye. Dole ta dinga jan carbi tana girgiza kai.
Cikin dare kowa na barci amma banda Gwaggo. Ta ɗaga hannu yafi a ƙirga da nufin la'antar ɗanta, amma hakan ya gagara. Don haka ta fashe da kuka mai cin rai.
"Mu'azzamu ya tozartani ya cuceni ya cutar da ni. Na bashi nono mai cike da tsafta. . .