Skip to content
Part 22 of 36 in the Series Mu'azzam by Fatima Dan Borno

Da isar Gwaggo gidan Dakta Salim matarsa mai kirki ta karɓe su hannu bibbiyu. Ɗaki ɗaya suka ajiye Gwaggo a ciki. Sai dai ta kasa cin komai, ta kasa magana. Da zarar zata buɗa baki ta yi magana sai hawaye. Dole ta dinga jan carbi tana girgiza kai. 

Cikin dare kowa na barci amma banda Gwaggo. Ta ɗaga hannu yafi a ƙirga da nufin la’antar ɗanta, amma hakan ya gagara. Don haka ta fashe da kuka mai cin rai.

“Mu’azzamu ya tozartani ya cuceni ya cutar da ni. Na bashi nono mai cike da tsafta, shi kuwa ya ciyar da ni da haram, ya shayar da ni da haram. Yusuf ka gode Allah da baka raye bare har ka ga irin wannan baƙin cikin.”

Ta sake gocewa da kuka.  Sannu a hankali ta fara rawar sanyi kafin wani lokaci jikin ya rikice mata.

*****

A wannan dare ‘yan sanda suka zagaye gidan M.Y jin bayaniya yasa gaba ɗaya matan suka firfito. Ganin gawa da kuma ‘yan sanda a tsaye a falon yasa duk suka ruɗe suka kama kuka. Wani daga cikin su ya cusa kai ɗakunan yana neman Mu’azzam. 

“Ku gaya mana gaskiya ina mijinku?”

Kowacce ta hau rantsuwar bata san inda yake ba. Babu abin da suka samu a ɗakin da zai nuna masu wani abu da suke nema. Dole suka ɗauki hotunan Jamilu Sannan aka ɗauke shi. 

Tun a cikin daren gari ya ɗauka M.Y ya yi kisa. Salima da ke zaune shiru ta dubi sauran ta ce,

“Idan zaku zauna ni gidanmu zanje. Domin kuwa na gama zama da M.Y. Dama haƙuri nake yi, babu haihuwa babu wani abin kirki da na tsinanawa kaina.”

Bilki ta janye taguminta ta ce,

“Ni damuwata igiyoyin aurenmu da ya tafi da su. Ko yayane ni ya sakemu sai ya kama gabansa. Yanzu shiga jama’a dole ya yi mana wahala. Ga shi duk inda muka bi idanun ‘yan sanda yana kanmu. M.Y ya cuci kansa ya zalunci kansa. Allah ne ya kama uwarsa, da komai sai ta nunawa mutane iyayi wai ita mai addini mai iya tarbiyya. Gashi ta haifo annoba.”

Amina ta yi ajiyar zuciya ta ce,

“Kunsan me ya fi bani mamaki ne? Da ya tashi guduwa sai ya ɗauki ‘yar uwarsa ya gudu da ita, wato mu idan za a kamamu ko a jikinsa. Ni dama na gaji da zaman rashin biyan buƙata, don haka ba zan sake kwana a gidan nan ba, gidanmu zanje. Kuma Wallahi ko a waya na same shi sai ya sakeni.”

Anan suka yi ta tattaunawa. Daga ƙarshe suka tattara kayan su kowacce ta wuce gidan iyayenta.

*****

Sun yi nisa a cikin dajin suna gudu. Husna ta fi bashi mamaki, yadda ko da wasa bata ce masa ta gaji ba. Dole ya dakata da gudun ya dubeta.

“Husna kingani ko? Na gaya maki zaki sha wahala.”

Ta yi baya kamar zata faɗi, ya yi saurin tarota. Duk da duhun dajin hakan bai hana shi neman wuri ya zauna ba. Shiru suka yi zuwa wani ɗan lokaci sannan ya ce,

“Allah gani gareka.”

Husna dai bata iya ko motsawa ba. Suna nan zaune har barci ya kwasheta. Shi dai yana riƙe da ita har zuwa asuba.

A hankali ya tasheta ta buɗe idanun tana sake lumshe su, daga bisani ta ƙudundune a jikinsa tana wani irin cusa kanta cikin jikinsa. 

“Husna tashi kiyi Sallah.”

Sai a lokacin ta ji wani irin ciwon jiki, ta buɗe idanunta tana Salati. 

“Me ya kawo mu nan?”

Ta faɗa cikin ruɗewa. Sai kuma ta tuna da komai, don haka idanunta suka kawo ruwa,

“Gwaggo. Na shiga uku Gwaggona tana cikin wani hali. Don Allah mu koma wurinta.”

Hankalinsa ya ƙara tashi. Duk irin cikin tashin hankalin da yake, hankalinsa yana kan mahaifiyarsa. Ko yaya ya nausa tunani sai kalamanta sun fara yi masa kuuwa. Shi kansa ya sani bai kyautawa Gwaggo ba, bai kyauta mata ba.

A hankali ya miƙe ba tare da ya ce komai ba ya tafi can wani wuri sai gashi ya dawo da ruwa ya miƙa mata. Karɓa kawai ta yi, tana share hawayenta ta zagaya sannan ta samu ta yo alwala. Mamaki kawai take yi ta yadda akayi ya samo ruwa. Tare suka yi Sallah, sannan suka zauna shiru. 

Husna ta sake sa kuka ta ce

“Don Allah ka tashi mu tafi wurin Gwaggo.”

Wannan karon tana neman ta ƙure shi, bai san da wanne zai ji ba.

“Ke kada ki dameni. Idan kina son tafiya ki tashi ki kama hanya ban hanaki ba. Ki barni inji da abin da yake damuna.”

Husna ta dube shi ranta a ɓace ta ce,

“Ka fi kowa sanin wannan ranar zata zo me ya sa baka yi tunani ba? Ko a tunaninka zaka yi ta saɓawa Allah ne ba tare da ya hukuntaka ba?”

Shiru ya yi mata, yana sake jin muryar Jamilu a lokacin da rai yake ƙoƙarin yin halinsa. Shi kenan Jamilu bai tsinana komai a duniyarsa ba. Ya mutu ta dalilinsa, ya mutu saboda ya kare lafiyarsa. Shi kuwa ina zai iya mance Jamilu?

Tsoron Allah ya ƙara ratsa shi. Kalaman mahaifinsa suka dawo masa cikin kai,

“Duk rintsi kada ka ci haram, kada ka kusanci zina, kada ka cutar da ɗan uwanka musulmi.”

M.Y ya rintse idanu yana jin tarin damuwa yana sake lulluɓe shi. Wani irin kunya ya lulluɓe shi. Ya ƙurawa Husna idanu babu ko ƙyaftawa. Da gaske tana son ganin Gwaggo, ya hango damuwa ƙarara a cikin idanunta. Abin da har yanzu ya kasa fahimta akan Husna yake kuma tambayar kansa shi ne me ya sa Husna ta zaɓi ta biyo shi? A saninsa ta fi kowa tsanarsa, me ya sa zata kusanto shi a daidai lokacin da ya kamata ta guje shi? Ya sani babu abin da Husna take nema kamar hanyar da za su rabu, me ya sa ta sami daman ta yi watsi da shi?

Tambayoyi ne rututu a cikin zuciyarsa, kamar yadda yake a danƙare a zuciyar Husna.

Sai da haske ya yi sosai sannan ya juya kawai ya fara tafiya, jiki a sanyaye ta bi bayansa. Don bata san dalilin da yasa yake yawan kallonta ba, sai gani take yi kamar so yake shima ya mutu.

Waya ta ji yana yi, can sai ga wani matashi ya zo suka ci gaba da tafiya. Wani wuri suka samu mai fili, ya nuna mata gefe ya ce ta zauna. Matashin ya miƙa masa ledar da ya zo da shi, shi kuma ya miƙawa Husna. Buɗewa ta yi chips ne don haka ta fara ci ba dan tana jin daɗinsa ba, sai dan yadda yunwa yake shirin yi mata illa. Tana kallonsu suka shiga haɗa bukka irin na fulani. Kafin wani lokaci sau ga bukka. Ya dubi matashin ya ce,

“Zaka koma cikin gari ka samo min ƙaramin katifa da zai iya shiga wurin nan. Kai zaka dinga kawo mana abinci. Amma sai kayi takatsantsar. Duk rintsi kada ka bayar da wannan layin nawa, domin babu mai lambar sai kai.”

Yunusa ya rissina Yana jin babu abin da ba zai yi dan ya ba ogansa kariya ba,

“Insha Allah ba za a sami kuskure ba.”

Sai a lokacin shima ya ɗauki nasa ya fara turawa yana haɗawa da ruwa.

*****

Gari ya ɗauka da maganar neman da ake yi wa M.Y. Don haka bayan Gwaggo ta farfaɗo da taimakon Dakta Salim, ya samu ya lallaɓata tasha ruwan tea, ya sa aka dawo da ita falo domin a dinga ɗebe mata kewa. Sai dai fitowarta falo bai amfana mata da komai ba sai danasani. Sakamakon ganin hoton M.Y a cikin t.v ana nemansa ko a mace ko a raye.

Duk yadda Gwaggo taso ta daure abin ya faskara. A karo na farko tausayin ɗanta ya karyo zuciyarta, sai dai kuma har abada bata tare da rashin gaskiya. Shi kenan ya tabbata ta rasa ɗanta ɗaya jal! Da ya rage mata. Wanda har yanzu da ya girman nan bai wuce zuwa ya kwanta a jikinta ba, bai wuce tarairaya irin na uwa da ɗa ba. Bai wuce ta sa shi a ɗaki ta ji damuwarsa ba. A tunaninta bai taɓa ɓoye mata komai akan rayuwarsa ba.

Duƙar da kan da ta yi, daidai yake da janyewar numfashinta, wanda babu wanda ya kula babu numfashi a tare da ita.

*****

Suna zaune a cikin bukkan daga shi har ita babu mai magana. 

“Me ya sami Gwaggo? Gwaggo tana cikin matsala.”

Ya faɗa yana ƙoƙarin tashi ya fice jikinsa yana rawa. Husna ta kamo rigarshi tana girgiza masa kai,

“Kada kaje wurin Gwaggo a yanzu, domin zuwanka zai sake sa mata damuwa.”

Komawa ya yi ya zauna jiki a sanyaye. Duk suka sake yin shiru.

“Uncle baka da rabo.”

Ta furta masa tana sake nazarin fuskarsa. Dubanta ya yi sosai, sannan ya ɗan janyo murmushi a fuskarsa wanda rabon da ta ga murmushinsa har ta mance.

“Tambayoyin me kike son kiyi min naga bakinki yana motsi?”

Kallonsa kawai take yi tana jin Allah yasa ta sami dukkan amsoshinta,

“Matanka uku.”

Sai kuma ta yi shiru. Tana son sanin yadda mata uku dukka babu na ƙwarai. Shi kuwa wani irin laifi ya yi wa Ubangijinsa?

Murmushin ya sake yi ya dubeta sosai,

“Nasan abin da kike son cewa Husna. Bilki tana yi min sata ko? Bilki ɓarauniya ce ko? Na jima da sanin hakan tun kafin ki shigo gidana, har zuwa ranar da ta yi maki sharri duk na sani. Salima tana neman mata ‘yan uwanta ko? Na jima da sanin hakan, har lokacin da ta nemeki kika fasa mata kai ta yi maki sharri. Da farko na dakeki ne saboda babu tunani a cikin kaina. Salima tana amfani da wani kwalli mai tsananin ƙarfi wanda duk yadda zan so inkufce mata bata taɓa yarda, sai da ƙyar na samu na sace kwallin.”

Ya yi ajiyar zuciya, amma kuma murmushi bai ɓace masa a fuska ba, ya ci gaba da cewa,

“Amina kuma tana bin maza. Tana kawo min maza har cikin gidana. Nasani. Ranar da ta yi maki sharri kin kawo kwarto ni na gansu tare naga lokacin da ya shiga ɗakinki. Husna duk abin da ake aikatawa a gidana babu wanda ban sani ba.”

Husna ta buɗe baki tana kallonsa kamar wawiya. Duk yasan waɗannan abubuwan yake zaune da su? Shi kuwa wani irin mutum ne?

“Kasani fa ka ce.”

Ya gyaɗa kai,

“Tunda na zayyano maki abin da kike ta ɓoye min ai kinsan na sanin da gaske.”

Ta haɗiye wani irin miyau mai ɗaci, ta ce

“Wa… Waye ya ya min fyaɗe?”

Ta yi tambayar muryarta na rawa, ga dukkan alamu har yanzu abin yana mata ciwo.

“Ni ne nayi maki fyaɗe.”

Ya faɗa kansa tsaye. Ta dube shi tana zazzare idanu. Ya yi murmushi tare da gyaɗa mata kai alamun hakan yake nufi.

Muje zuwa dai.

<< Mu’azzam 21 Mu’azzam 23 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×