Mu'azzam ya yi murmushi. A ganinsa manyan mata irin su Salima sun kasa bare kuma ita? Ba zai iya barin Husna ta tafi gidan Alhaji Mu'azu ba. Gani yake itama idan ta tafi ba zata dawo ba. A yanzu kuwa bashi da wacce yake gani yake jin daɗi kamarta. Kamo hannunta ya yi yana dubanta,
"Husna ba zan iya yin kasadan rasaki ba. Ke yarinya ce ƙarama ba zan so kema ki zama tarihi ba. Ki duba ki gani, sunan ina raye ne, amma bani da maraba da matacce, tunda har mahaifiyata take kwana da baƙin. . .