"Innalillahi Wa Innaa ilaihirraji un..."
Addu'ar da M.Y yake furtawa kenan. Tabbas bai mance kowane tsanani yana tare da sauƙi ba. A hankali ya tashi yana jin jiri na ɗibarsa, sai dai ba zai iya zama a cikin gidan nan ba. Har ya kai farfajiyar gidan ya tsugunna yana jin kansa yana sara masa. A hannu ya ji ansa andafa shi, bai waiwayo ba dan bai da buƙatar yin hakan.
"M.Y mahaifiyarka tana nan a raye. Ina zaka je?"
Wani farin ciki ya lulluɓe shi, ya tashi yana duban Dakta Salim, da kuma su. . .