Babu natsuwa cikin ransa a lokacin da wata kira ta shigo cikin wayarsa. Ya jima yana duban fuskar wayar yana jujjuyata, daga bisani ya fice tare da amsawa kamar ransa a ɓace.
A lokacin Husna ta miƙe ta nufi tsakar gidan domin ta kwashe kayan shanyar da ta yi. Ta rasa dalilin tsayawarta tana sauraren maganganun da yake yi cikin zafin rai,
"Sau nawa zan gaya maku idan ina tare da Gwaggo ku daina kirana? Me kuke nema? Me zanyi maku don Allah? Wannan ne karo na ƙarshe da zan sake ɗaga kiran da wani daga cikinku ya yi. . .