Husna ta kalmashe hannunta ta zura mata idanu tana son ganin iya gudun ruwanta.
"Sunana Salima. Ko kin ganeni?"
Salima ta furta da izza. Husna ta yi murmushin takaici ta ce,
"Baki buƙatan sake sanar da ni ko wacece ke. Mutanen banza kamarki ba lallai a iya mance su cikin sauri ba. Me ke tafe da ke? Ina da abubuwan yi."
A gadon ta yi wa kanta mazauni tana kallon ko ina, sannan ta ce,
"Nazo insanar da ke zancen kome da zan yi ne. Ina nufin kayan da na baki aro zaki maido min."
Husna ta ƙaƙalo. . .