Ridayya ta ɗauka kunnenta ne ya sa mu matsala, cikin sauri ta zame wayar daga jikinta tare da saka hannu ta shiga bubbuga kunnen a fili ta ce "Babu mamaki ruwa ne ya shiga ciki, ya toshe ƴar ƙofar ɗaukan sautin har take naɗo mini masifa da bala'i"
Ta mayar da wayar a hankali duk da ƙirjinta dake bugawa da muryarta ke rawa bai hana ta tattaro jarumta kamar jinin Iliya ɗan mai-ƙarfi ba ta ce "Rayuwata, ni ce matarka Ridayya ka na ji na?" Ta yi maganar cike da ƙarfafawa kanta qiwwa, da share gurɓataccen. . .