Idanun Ustaz ya sauka akan abin da ba zai taɓa mantawa da shi ba a rayuwarsa, ya yi zaton wani a cikin kitchen ɗin, amma mummunan ganin da ya yi ya sanya ya ɗan yi baya a tsora ce tare da rufe idanunsa can ƙasan zuciya Ustaz Bilal ya ce
"Ya subuhanallahi! Asstagafirullah" Ridayya ya gani da Zameer kwance a ƙasan kitchen ɗin, turmi da taɓarya, ya saka hannu ya shaƙe mata wuya sai shure shure take tana kakari tamkar na fitar hayyaci ko zarar rai.
Ustaz da ƙyar ya ja ƙafafuwansa da nufin barin wajan domin. . .