Skip to content
Part 6 of 9 in the Series Munafukin Miji by Nimcyluv sarauta

Idanun Ustaz ya sauka akan abin da ba zai taɓa mantawa da shi ba a rayuwarsa, ya yi zaton wani a cikin kitchen ɗin, amma mummunan ganin da ya yi ya sanya ya ɗan yi baya a tsora ce tare da rufe idanunsa can ƙasan zuciya Ustaz Bilal ya ce

“Ya subuhanallahi! Asstagafirullah” Ridayya ya gani da Zameer kwance a ƙasan kitchen ɗin, turmi da taɓarya, ya saka hannu ya shaƙe mata wuya sai shure shure take tana kakari tamkar na fitar hayyaci ko zarar rai.

Ustaz da ƙyar ya ja ƙafafuwansa da nufin barin wajan domin jiri ne ya ji ƙoƙarin yasar da shi a ƙasa, al’amari Ridayya kullum girmama yake yana sake lalacewa.

Karo suka ci da Baba ƙarami daya fito hakan ya sa Ustaz tsayawa tunda ya ga lokacin assalatu bai yi ba, balle ya yi zaton Baba ƙarami sallah ya fito yi.

“Ustaz ba dai ya zo kake dawowa ba?” Ustaz ya kalli baban nasa a hankali ya ce “E, dawowar kenan” Cikin gamsuwa ya jinjina kai yana mai faɗin.

“Ai tun ɗazo nake jiranka mu yi magana, har dare ya yi shiru ka jira ni a parlo zan duba naga ta’addin me nake ji tun a shashin baya har hanyar kitchen” Kafin Ustaz ya yi magana Baba ƙarami ya nufi hanyar kitchen ganin da gaske can ya nufa, kuma baya fatan ace mahaifinsa yaga abinda nasa idanun ya gani da ɗan saurin harshe ya ce

“Abba, ni ne fa”

Baba ƙarami ya tsahirta da tafiya ya ce “Kai ne me?” Kan Ustaz a ƙasa

“Ruwan zafi na haɗa, na ɗan zaga baya ne”

“Ruwan zafi a daren nan Mai babban suna? Kamar wani ƙaramin yaro kake suntiri da ɓuruntu?” Shi dai Bilal bai ce komai ba, domin baya buƙatar sake shimfiɗa wata ƙaryar akan kare Ridayya, ya nufi hanyar parlour. Yana zama Baba ƙarami ya zauna yana ƙarewa ɗan nasa kallo a nutse ya ce

“Bilal?” Da Idanu kawai Ustaz ya amsa Baba ƙarami ya ɗora da faɗin

“Ridayya tana gidan nan, na ɗakkota daga asibiti rayuwar yarinyar nan abar dubawa ce, bai kamata a ƙarancin shekarunta a ce tana fuskantar ƙalubalen gidan aure da matsalar miji ba, kasan rayuwar Ridayya ka fi kowa sani da halin data tsinci kanta a baya, me ya sa ba zaka aureta ba?”

“Aure Abba?”

Baba ƙarami ya yi murmushi ya ce “Shi fa, naga ba haramun bane” Ganin Ustaz na shirin miƙewa ya saka cikin bada umarni Baba ƙarami ya ce “Kar ka kuskura ga tashi, ko baka son Ridayya zaka aureta”

“Mahaifi da auren ƴarsa ina aka taɓa haka? Asstagafirullah Allah ka ya fewa Abbana” Baba ƙarami ya saki baki kafin ya ce “Zan sassaɓa maka yanzu, idan ranka ya yi dubu to zai ɓaci, ka kuma gaggauta cire abin da ke yawo a zuciyarka ka daina haramtawa kan ka abinda yake halak ne zaka iya jahadi ne” Ustaz ya miƙe tsaye idanunsa jajur ya ce 

“Abba kai na ciwo yake nikam ciwo kai na ke mini, Matar auren kake jingina mata auren wani Abba haza haramun Ya Rasulullah Asstagafirullah!” Yana faɗin hakan ya fice shi kansa bashi da tabbaci akan maganganun da yake furtawa.

Washegari wajan shi da na safe Baba ƙarami ya saka a haɗa abin karyawa zai kaiwa Ridayya ta sha, ta ci abinci ta ƙara hutawa sai a sauya mata asibiti domin wani abun da yake damun Ridayya hadda sakacin iyaye da rashin kula da al’amarin yaran su. Da sallama ya shiga ɗakin amma shiru ba amsa ya dinga bin ko’ina da kallo ba Ridayya babu mai kama da ita, yana shirin fita idanunsa ya a kan takardar da aka ajjiye saman gado ya saka hannu ya ɗauka, saƙon daya gani ya gigita shi tare da sauya masa lissafi da jin komai zai yi a rayuwa dole ya kashe auren Ridayya Ustaz ya aura, Ubangiji shi ne shaida bai aikata hakan domin ya ci mutuncin wani ba, ko ya lalata mata auren ta ba, zai yi ne domin taimakon rayuwar ƴar ɗan’uwansa. Ya sake ware farar faifa ɗin idanunsa ya sauka a kan rubutun nata.

_Ni na san ban kasance alheri a zuri’armu Abba zan so ka cire hannu a cikin al’amarina kamar yadda Baffana ya cire, na gode da taimako daga yanzu har zuwa ƙarshen rayuwa bana buƙatar ko wanne taimako mijina ya tsaya mini, ya share mini kukana, daman kune baku fahimta ba amma nasan ba wata mace da Zameer ke so kamar mata ni Ridayya, zan yi nisa daku domin na fahimci za ku iya raba aurena, Abba kar ka yi mini kuskuren fahimta Zameer ya zo na bi mijina gidan aurena na sunna ya ce muddin ban bisa ba to zai sake ni, ba zan iya zawarci ba, ba zan iya barin Zameer ya rayu da wata mace bayan ni ba, wallahi ina son mijina shi ne rayuwata_

Murmushin takaici kawai Baba ƙarami ya yi tare da yaga saƙon, ƙiri-ƙiri Ridayya ta watsa masa ƙasa a ido? Allah ya sa banda Bilal babu wanda ya san da zuwanta nan daman mahaifiyarsa Bilal bata nan ɗin. Ya juya yana kiran ɗan’uwansa a waya domin akwai buƙatar ya baro Rano zuwa Kano. 

Ustaz a gida ya bar motarsa kasancewar aljihunsa da ɗan nauyi tunda an yi albashi ya biya kuɗin jirgi daga Kano zuwa Lagos ɗin. Suna tafe a mota zuwa airport Junaid na driving Ustaz na zaune idanunsa rufe ya ce “Baku daidaita da Batool ba?”

Damuwar Junaid ta bayyana ya ce “Kowa da ƙaddarar shi, itama Batool an yi Genotype jikinta AS ne dole za mu haƙura da juna ne, idan ban manta ba Batool ita ce mace ta shida”

Ustaz ya ce “Ikon Allah, to Allah ya shiga lamarin”

Junaid ya ce “Amin, yaushe zaka dawo Kano idan ka tafi?” Ustaz ya yi shiru can ya ce “Shekara war haka” Jinjina kai kawai Junaid ya yi domin shi na zai so ace Bilal ɗin bai dawo ba balle ya ci-gaba da taimakawa Ridayya.

“Na manta wayata ɗan bani a ron wayarka”

Kamar Ustaz ba zai bayar ba sai kuma ya miƙa masa, Junaid ya matsa can gefe ya shiga lalubar number Ridayya da ƙyar ya gano ta yaga an yi saved da _Ustaza_ Number ya saka a black list ya yi blocking gabaɗaya kana ya dawo yana cewa.

“Nama tuna inda na ajjiye wayar tawa, daman ita zan kira na bar ta a parlon Mami wajan Zainura” Bilal bai ce komai ba har aka kira su ya shiga jirgi kana Junaid ya juya zuwa gida zuciyarsa cike da tausayin Ridayya amma dole ta gane kuskurenta yanzu zata fahimci muhimmancin Ustaz a cikin rayuwarta.

Ridayya na kwance tun cikin dare da Zameer ya je ya biya buƙatarsa wanda a lokacin ta ɗauka mutuwa za ta yi saboda wahala amma shi ko a jikinsa, tunda ya fita bai dawo gidan ba har gari ya waye, ko ƙwayar abinci bata kai bakinta ba balle kuma a yi batun maganinta ga ɗinkin da akai mata yana neman farke wa dalilin abinda Zameer ya yi mata a asibiti da kuma gida sai ruwa wajan yake. Kai ta ɗaga ta kalli lokaci ƙarfe 1:56 so take ta tashi ta gabatar da sallar zhur wato azahar amma ta kasa jikinta duka ciwo yake mata jijiyar bayanta ta riƙe sosai, ta ci kuka son ranta har ta ga ji. Khairy ce ta shigo daga ita sai ɗaurin ƙirji da towel ya tsaya iya cinya, kamar daga sama kuma taga Zameer ya shigo shima gajeren wando ne a jikinsa ruwa na zuba alamar wanka ya yi ko kuma sukai tare da Khairy ɗin.

Farar fatar Khairy sai ɗaukan idanu take a barka da kyakkawa kuma mai diri da kyan fuska, hakan ya ƙara sawa Zameer jin komai ya dawo masa sabo fil dan gane da abinda yake ji game da Khairy. Ridayya ta dinga kallon su tana haɗiye yawun daya taro a bakinta ƙirjinta na bugawa numfashinta na ƙoƙarin tsayawa, kallon Khairiyya take kamar bata taɓa ganinta ba tana ƙoƙarin magana Khairy ta saka hannu ta ja gajeren wandon Zameer ta ce

“Kai Yaya tun safe nake nemanka zani wajan Mama yau zuwa dare na dawo” Zameer ya kasa kallon Khairy duk yar da zuciyarsa ke kwaɗaituwa da son haka, haka kuma ya kasa kallon Ridayya ganin yar da take binsu da kallo sai kuma ya haɗe fuska ya ce

“Ridayya jikin ne ya sa ba ki iya sannu ba? Sai bina kike da idanu da kuma dogon baki?”

A hankali ta ce “Ka yi haƙuri” Niyyar ƙorafi take amma ganin fushinsa ya saka ta haƙura da nata domin ko da wasa bata ƙaunar taka sauyi a fuskarsa. Khairiyya ta ce

“Laa matar taka kake cewa mai dogon baki? Daman gashi duk ta zama tsohuwa” Caraf ya saka hannu da nufin make Khairy sai ya hau yi mata cakulkuli ta shiga dariya tana guduwa yana binta suka shiga tsere a parlon Ridayya suna zagayeta ba kunya da tsoran Allah. Suna cikin gudun towel ɗin Khairy na faɗuwa ƙasa, sarai Khairy ta san towel ɗin ya faɗi ta rufe idanunta tare da juyowa inda Zameer yake tana girgiza ƙirji da banƙaro ƙirji haɗe da faɗin “Hooo bai kamani ba, a yi masa gwalo wulwul bai kamani ba” Ta sake faɗa tana tura ƙirji gashi daman ba komai a jikin nata sai towel kuma ya faɗi.

“Kau!” Ridayya ta ɗauke Khairy da mari tana shirin ƙara mata wani kamar daga sama ta ji an ɗauketa da wasu tawayen maruka wanda sai da taga wuta ta gilma ta tsakanin idanunta, daman ba ƙwari gare ta ta yi bata zata faɗi ta yi Khairy cike da makirci ta tare Ridayya ta ce

“Haba yaya me ya sa zaka mata wannan jahilin marin? Ka manta bata lafiya? Ya kake abu kamar baka damu da matarka ba”

Zameer ya yi mitsi mitsi da Idanu ya ce “Shiru a nan Khairiyya, shiru na ce, ke me kika yi mata da zata saka hannu ta daki lafiyayyiyar farar fuskarki? An faɗa mata ko wacce fuska ake mari?” Khairy rai fes ta ce “Babu mamaki tana da hujjar marina ko na yi mata laifi ban sani ba.”

Ridayya kishi ya turnuƙe ta kenan suna nufin daga Khairy har Zameer ba wanda ya fahimci me sukai? Idanunta ya rine jiri na ɗaukan ta ga ɗinkin jikinta dake amsawa ta ce “Rayuwata mari na ka yi? Mari har biyu?” Ya juya yana kallonta ya ce “Zan miki mahaukacin duka ba mari ba muddin za ki taɓa jinina bana wasa da ƴan’uwana.”

Ta runtse idanunta ta yi tana kiran sunan Allah kafin ta ce “Yanzu ya dace ka dinga bin baligar mace da cakulkuli a gabana Meer? Har towel ɗin jikinta na faɗuwa kai hakan duk bai dameka ba? Tsaraicinta shi ne abin kallo Meer?”

Zameer ya yi kan Ridayya zai daka Khairy ta yi saurin tare shi tana haɗe jikinsu waje guda ta ce

“Haba yaya Anti Ridayya gaskiya ta faɗa ɗan miƙo mini towel ɗin na rufe jikina” Zameer ya juya tare da ficewa yabar wajan, Khairy ta ce

“Ki yi haƙuri ban san towel ɗina ya faɗi ba, bada gangan na yi hakan ba, amma kar ki sake gangancin marina domin amana Mama ta bawa Zameer ni zai iya komai a kaina.”

Ridayya ta kasa furta komai takaici ya mamaye ta, kenan ita data bar kowa nata saboda miji hankali ne bata da shi kome? Yau Zameer ita ya mara a kan ƙanwarsa? Saboda suna aikata abinda bai dace ba? Ko kuma laifi ne don ta nuna kishi akan abinda take mutuwar so?.

Kuka ta dinga yi ita kaɗai domin hakan sabon abu ne a wajanta, ga yunwa ga ciwo ga takaicin da miji ya ƙunsa mata, ga matsalar ciwon zuciyarta na soyayyar Zameer.

Da ƙyar ta miƙe ta gabatar da sallah ta haɗa azahar da la’asar, Zameer na fita ya shige ɗaki Khairy ta bi bayansa suka kulle ƙofa bata tare da yin shiru. Ridayya bata san meke faruwa sai jin sautin waƙa ta ji yana tashi daga ɗakin Zameer ta rufe ido tana jiran taga ta ina mala’ika azara’ilu zai fito? Domin mutuwa ita ce abar da take fata ta risketa. Sallamar Zainaba da yar da take bubbuga kafaɗar Ridayya ya fahimtar da ita ce ita da rayuwa sun ƙalla aminci ne, haƙarta sam bata cimma ruwa ba, ta bi Zainaba da jimammen idanunta ta kasa cewa komai.

“Mai ƴar tsala tunanin me kike haka? Ashe da gaske daman Usman yake kin dawo cikin dare ke da Zameer?” Ridayya ta jinjina gulmar Zainaba da mijinta ta ce,

“E, an wuni lafiya Maman Hajjo?” Zainaba ta ce

“Lafiya ba lafiya ba, ina can ƴar nan da tunaninki, to Masha Allah jiki ya samu” Ridayya ta ɗan yi yaƙe haƙora suka bayyana muninta ya sake fiddowa fili.

“Abinci na kawo miki, sai kuma kika ji daga tafiyarki Mai ƙosai ta fara yin ƴar tsala? Mutane babu ko kara” Ridayya ta ce “Allah sarki kowa rabonsa zai samu ai, ni ina tunanin ba zan sake ƴar tsalar ba”

Zainaba ta riƙe baki ta ce

“Ke kowa saboda me? A’a wallahi ai jama’a nata cigiyar mai ƴar tsala”

“Ba kuɗi a wajena, ba jari” Zainaba ta yi ƙasa da murya ta ce “Ina adashin da kike yi to? Ki karɓa bayan ƴar tsala sai ki fara siyar da kayan miya ma ai zama haka ba naki bane tunda kalar naki ƙaddarar kenan”

Ridayya ta yi murmushi ta ce “Ai na amshi kuɗin yau da safe har sun ƙare a magani” Baki sake Zainaba ke kallon Ridayya zata iya rantsewa da Allah mijinta mai zaman banza ta ba wa kuɗin.

“Shikenan akwai wata dubu biyar waje na sai na ara miki ki ɗora jarin idan kin manshe da kuɗin kya bani ko?” Ridayya ta ce “Na gode sosai Maman Hajjo Allah ya saka” Ta kunce bakin zani ta ba wa Ridayya kuɗin kana ta yi mata sallama ta ce

“Zan aiko hajjo ta amshi kwanon abincin”

Da sauri Zameer ya koma ɗaki jin Zainaba ta fito, daman ya fito da nufin karɓar hakƙinsa wajan Ridayya tunda duk nacinsa da Khairiyya ya kasa samun nutsuwa da ita. Ridayya ta jawo kwanon abincin kenan Zameer ya shigo yana ƙamshi ya sha shadda daman ba dai iya ɗaukan wanka ba, ya san takan gayu sosai.

Ridayya bata kalle shi ba ba kuma ta saka hannu cikin abincin ba. Meer ya tausasa murya cikin salo na makirci kamar mace ya ce “Fushi kike dani mai sona? Idan kikai fushi dani ai na shiga uku bani da wani sauran gata” ko tari ba ta yi ba.

Sai kawai ta ji ya fashe mata da kuka yana kifa kansa a cinyarta a hankali kuma ya toshe hanci gudun kar ƙarnin ruwan ciwonta ya saka shi a mai. Ya dinga kuka kamar amaryar da aka ɗaurawa lallai.

“Ki yafe mini kada ki tarwatsa zuciyata da shirun nan naki, nasan na miki laifi Ridha amma kin san halin Khairy yarinya ce ita ba hankali kuma mun saɓa ƴar tsere da cakulkuli da ita, yanzu da kika mare ta da ban rama mata ba zuwa za ta yi ta faɗawa Mama kuma a kan Khairy Mama na iya tsine mini.”

Ridayya dai bata ce komai ba ya ce “To shikenan rama marin tunda ba za ki yafe mini ba” A hankali ta ce 

“Ina zaka?” 

“Ke na yi wa kwalliya, nikam ke na yi wa ki yi ta kallon rayuwarki ki na jin daɗi, ina tsananin son ki matata farin cikin rai na, mayyar Zameer i love you!” Nan da nan Ridayya ta mance komai daya faru ta ce “Ka ci abinci?”

Ya ce “Ta ya zan ci na hanaki bani kuɗi, nema dai zani” Ta tura masa kwanon abincin da Zainaba ta kawo mata ta ce “Ga abinci nan, kuma ka bawa ƙanwarmu Khairy haƙuri kishinka da son ka ya sa na yi abinda na yi” “Uhm” ya ce yana jan kwanon.

Shinkafa da miya ce da kuma yankan nama guda huɗu ga haɗin salak, Ridayya sai haɗiyar yawu take sai daya cinye tas sannan ya ce “To ke kin ci?” Ta yi murmushi ta ce “E” Ya dinga kallonta gabaɗaya ta zama tsohuwa ya ce 

“Mai sona aron kuɗi nake so zan biya a yi mini printing na wasu takardu zan kaiwa Alhaji Muttaƙa ya nema mini aiki, da zarar na samu aikin zan fashe gidan nan na yi miki sabo ke da yaranmu, domin har miliyan biyu za a fara bani cikin satin nan muddin yau na kai takardun nan”

Daɗin ya kama Ridayya domin da zarar Zameer ya samu aiki zata fita daga wannan wahalar kuma zai siya mata kayan ɗaki “Har nawa kake so?” Ya ce “Dubu goma haka” Ta ware ido ta ce “Tab sai dai dubu biyar yanzu aka bani aronta na ɗora jarin ƴar tsala, kuma ka san na faɗa maka yar da mukai da Baba ƙarami na cewa Bilal kuma kar ya sake turo mini kuɗi bana buƙatar taimakon shi” Zameer ya zare ido ya ce “Amma ba ki da hankali ai ban hanaki kar ɓar kuɗi wajan shi ba, taimako ne maza ki bashi haƙuri ya dinga tura miki” Da mamaki ta ce “To tunda bana son shi me zan yi da kuɗinsa? Duk wanda zai wulaƙanta ka wallahi bana son shi” Zameer ya ce “Ai ana iya zuciya da komai ban da kuɗi, matsalarku daban taimako daban, bani kuɗin” Ta ɗakko dubu biyar ɗin ta bashi. Daga nan kuma ya dinga kallonta can ya ce

“Ina buƙatar ki”

A tsorace ta ce “Bani da lafiya ka yi mini afuwa, wallahi wannan abun baya gabana” A ransa Zameer ya ce “Banda wannan dalilin ni ma ko inda kike ba zuwa zan yi ba, wannan shi ne kawai dalilin daya sa ba zan rabu dake ba”

A fili kuma ya ce 

“Shikenan na gode” Ta girgiza kai ta ce “Zameer ka yi mini uzuri, bani da lafiya ba cima mai kyau balle abin ƙara lafiya da kuzari” Ya ƙanƙance ido

“Ohho ƴan’uwanki za ki bi kenan Ridha, ni kike wa gori? Ridha ni mijinki aljannarki na tafin ƙafata? Kike cewa ba cima mai kyau sata zan yi na ba ki? Ko ni zan zo ki cinye ni, to wallahi hakƙina ko kina so ko bakya so sai kin bani ai sadaki na biya”

Kafin ta yi magana ya cimmata tana kuka da ihu saboda ba daɗin abin take ji ba tsananin a zaba kawai take sha, gashi kamar mahaukaci haka zai shaƙeta idan zai nutsu, wani ihu Ridayya ta yi wanda ya yi daidai da ƙarar ƙarar zagewar wani abu keeeetttt hakan ya yi daidai da ɗaukewar numfashi Ridayya tare da yin ƙaura daga jikinta wanda yake bayyana suman da ta yi.

<< Munafukin Miji 5Munafukin Miji 7 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.