Ƙarfe takwas na safiya ranar da ta zam saura kwanaki bakwai ne a ɗaura auren Malam.Kwance nake a ɗakina lamo, Amir na bisa jikina wani zazzaɓi nake ji yana shirin rufe ni a haka yaron kishiyata Hajja mai suna Adamu ya shigo ya riske ni.
"Baba yana kiranki a ɗakinsa."
Kai na ɗaga ban yi magana ba sai miƙewa da na yi, hijab ɗi na da ban daɗe da cirewa ba na sanya nan na bar Amir don ya yi barci.
Na isa ɗakin Malam da ke jikin nawa, yana zaune kan katifarsa da ke tsakar. . .