Skip to content
Part 1 of 64 in the Series Mutum Da Kaddararsa by Maryam Ibrahim Litee

Ƙarfe takwas na safiya ranar da ta zam saura kwanaki bakwai ne a ɗaura auren Malam.
Kwance nake a ɗakina lamo, Amir na bisa jikina wani zazzaɓi nake ji yana shirin rufe ni a haka yaron kishiyata Hajja mai suna Adamu ya shigo ya riske ni.

“Baba yana kiranki a ɗakinsa.”

Kai na ɗaga ban yi magana ba sai miƙewa da na yi, hijab ɗi na da ban daɗe da cirewa ba na sanya nan na bar Amir don ya yi barci.

Na isa ɗakin Malam da ke jikin nawa, yana zaune kan katifarsa da ke tsakar ɗakin kan darduma da na gani shimfiɗe na kai mazaunaina ina ƙara gaishe shi ba mu ƙare gaisuwar ba uwargida Hajja ta shigo ita ma ɗan nesa da ni ta zauna a ƙasa.

Turamen zannuwa biyu ya gabatar mana da kuɗi dubu goma goma ya ce na faɗar kishiya, tare da bayanin yau zai kwashe kayan ɗakinsa za a mayar mishi bene inda amarya za ta zauna don haka mai son shi ta biyo shi sama.

Hajja da da ma ta tsara min ko ya bamu kar mu karɓa ita ta fara miƙewa ta ce ta gode, ni ma na bi bayanta.

Ɗakina na shiga na faɗi kwajab kamar tsohuwar jaka!

Na dubi kujeruna da duk suka sukurkuce saboda dabdala da ake kansu, sai gadona na jan katako.

Rub da ciki na yi kamar kuma an tsikare ni na tashi zaune labulaina na duba wanda rabona da wanke shi tun wani zuwa da wata yar’uwata fannin babana ta yi ta ga ya yi datti ta cire ta wanke min, ta ce wa Hajja “Ku ko labulan ma ba ku iya wankewa sai Malam ya auro muku yar gayu, ku zo ku kama salli ilah salatittanjina, dubi wata dussa da kuka shanya.”

Hajja da ba a kada ita a magana ta ce”Ya yi auren mana ai mu mun ci dubu, mun wuce da iyawar duk wadda zai auro.”

Suka yi ta bugawa da yar’uwar tawa har ta tafi.

Wucewar ta babbar ɗiyar Malam da ba ta wuce sa’a ta ba mahaifiyarta ta rasu ta ga labulaina fes a wanke ita ma ta cire na babanta ta wanke, sai Hajja ta ce “Ni ce ba ni da gata ban da mai wanke min ta cire nata ita ma ta wanke.

Tun wannan wankin bai kuma ganin ruwa ba ina can shashancin biye wa kishiya.
Na cire su na fita na sanya a bokiti na bi da omo na jiƙa zan fara wankewa na ji wata sabuwar mutuwar jikin na bari na koma daki na kuma kwanciya.

Hankalin mu bai kuma ɗagawa ba sai da aka fara shigo da kayan amarya kai da gani ka san yaro da ganin birni ya san ya fi garin su.

Cikin satin nan idan ka shigo gidanmu ba za ka sha mu ba ne.

Mun daina wanke gida da daddare safe da yamma muke wankewa, almajirai da muke bari suna mana dabdala duk mun tsaida su mai mana wanke wanke da an bata za mu ce ta wanke, mun fito da kayanmu na ƙarƙashin akwati muna ta zuba ado wanda ban tunanin Malam ya ma san muna yi ba hankalin shi na ga tarar amaryarsa don sa’adda yake so mu yin ba mu yi ba.

Ranar ɗaurin aure garada suka kwashe mishi kayansa bai kwashe ranar da ya ce ba dama daga katifa ne sai wardrobe dinsa ko labulai bai dauka ba.

Ana gama shigewa da kayan Hajja ta ce min “In aure shi tun muna gidan haya, shi ne yau ya yi gidan da zai ɗaura wata sama in biyo shi dakin da ko flaster ƙasa bai mishi ba bai sanya labulai ba har in mutu ban taka ƙafar benen.

Ni dai na yi shiru wani abu na min yawo a ƙirji.

Ƙarfe takwas daidai ina zaune a ɗakina Amir na kwance jikina, muka ji dirin motoci da guɗa da ta karaɗe filin tsakar gidan.

Gabana ya yanke ya ce ras! Na shiga maimaita Hasbunallahu wani’imal wakil.Ni da Hajja yau kowa tashi ta fisshe shi don tuni kowacce ta yi ta kanta.

Ni dai tunda na shige ɗaki ba wanda ya kuma ganina a filin tsakar gidan.

Wannan dare ya zame min dare ma fi tsawo kuma mai tsanani ƙwarai da na ƙagara gari ya waye.

Ina jin ladan ya fara sallah na ce “Alhamdulillah. Ɓurum na buɗe ƙofa na fito na ɗauro alwala na zo na fara doka sallah har aka yi sallar asuba, ina idar da sallar na fita na shiga kitchen na haɗa itace na ɗora ruwan kunu, sai na koma kan wake na gyara shi na bayar aka miƙa min markaɗe.

Ina dama kunu na leƙa ɗakin Hajja sai da muka gaisa na ce mata “Na da ma kunu ne shi ne na ce za a zuba wa Malam da amarya ne na ga har Flacks ɗin na shi yana sama?

Ta ce “Share su, su da za su sha Tea da ƙwai.”

Na koma na kama suyar ƙosai yara suna ta zuwa suna karɓa, su sha su wuce makaranta.

Sai da na sallami kowa na wanke gidan ina daɗa share kitchen na ji ƙamshin turare ya daki hancina, na ɗaga kai Malam ne ya sha farar shadda yar ciki da wando da malum malum,ga hular nan sai sheƙi take ya ajiye ta a sha tara agogon hannunsa ma sheƙin yake.

Ya tattare malum malum ɗin ya raɓe ni ya wuce ko kafin in dawo nutsuwa ta in gaishe shi ya ɓace ma ganina.

Na haɗiyi wani yawu mai ɗaci na juye ruwa na je na yi wanka atamfata sabuwa da ya yi mana wannan sallar na sanya na tsaya gaban mirror ina duban kaina ba ƙaramar fyaɗewa na yi ba don fargabar yadda za ta kaya mana da wannan amarya da aka gingimo mana.

Kan dole na shiga kitchen da sabuwar atamfata kar amarya ta fito ta gan ni kaca kaca ta raina ni.

Ina haɗa itace na ji wani fitinannen ƙamshi ya ziyarci hancina,ba shiri na haɗiyi yawun da ya taru a bakina na ƙara buɗe hancina da kyau ina shaƙar ƙamshin don tabbatar daga inda yake fitowa, ba shakka daga saman amarya ne ƙamshin girkin nan mai sanya haɗiyar miyau ke fitowa.

Jikina har rawa ya kama tuna makomar mu da wannan amarya.

Na gama abincin rana na ɗaura miyar dare na fita tsakar gida na ji wani fitinannen ƙamshin amma wannan karon na turare ne na ɗaga kaina take gabana ya ce ras! Da muka haɗa ido da hamshaƙiyar matar cikin less take da ya amsa sunan shi daga kunnuwanta zuwa wuyanta da yan yatsunta sheƙi kawai suke don an ƙayata su.
Tana zaune a wata farar kujera ta ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya, mace mai matsakaicin jiki da tsawo haskenta ma matsakaici ne.

“Ina wuni?

Na jiyo muryarta daga inda nake tsaye na daga ido muka ƙara haɗa ido na ce “Lafiya lau.” Ta ce Ya yara? Na ce “Ya baƙunta? A sanyaye gabana na harbawa na koma na ci-gaba da aikina.

Da na kammala aikin ɗakin Hajja yau na shiga muka haɗu da yaranta ita ɗin ma yau ba ta labari, ni ma zama na yi shiru sai yara ke labarin ɗakin amarya suna zuzuta abin da ke ciki.

Hajja ta gaji da ji ta make wanda ke kusa da ita sai kowanne ya shiga nutsuwarsa.

Amarya ta kare kwanaki ukunta aiki ya faɗa kan Hajja ta yi aiki ta aika wa Malam abinci waje kamar yadda aka saba na safiya kuma sai ta aiki yara su kai masa ba ta taka saman ba kamar yadda ta yi alƙawari har ta gama girkinta.

Ranar da na karɓa da na yi girki na ɗauki na Malam zuwa sama na wuce falon amarya da ƙamshi ke fitowa labulen ma kaɗai ka duba ka san ta’adi mai yawa aka yi wa naira kafin a mallake su.

Na shiga ɗakin nasa da aka janyo ƙofa ba labulai har lokacin sai katifarsa a ƙasa, na shimfida zanen gadon da na ruƙo, sai na koma ƙasa na shirya Amir na ɗauko shi muka dawo.

Sai goma da rabi ya shigo daga ƙofar gida. Fura da ya saba sawo ma yara da nama balangu ya ba ni na karɓa na sauka ƙasa yaran sun yi barci sai na ba Ummansu ta ajiye musu, na koma na ba Amir da bai barci sai ya sha yana sha kuwa ya yi barci ni ma na gyara na kwanta Malam ya ce min Sallah zai yi, ya fita daga ƙofar ɗaki ya tayar da kabbara.

Jin shi shiru na shiga barci, sai tsakiyar dare na farka na tashi na leƙa Malam ba Malam sai sallayarsa, na koma na kwanta sai dai na gaza barcin maimakon in fuskanci Ubangiji in faɗa mishi damuwata sai na ci-gaba da kwanciya cikin tunani.

Ƙarfe huɗu na ji muryarsa yana Sallah, jira na yi har aka kabbara sallah a masallatai na sanya ɗana a kafaɗa muka sauko na yi sallah sai na shiga kitchen.

Wata ɗaya kacal amarya ta yi gabaɗaya ta sanya mun shiga taitayin mu. Misali ƙosan da muke soyawa mu ci mu ƙoshi da yara ta cewa Malam tana jin tausayin shi kawai a dinga dama koko kaɗai idan an yi tuwon dare a dinga yin ɗumame da hantsi a ci.
Idan girkinmu ne za mu yi wadatacce mu ci ba mu da damuwa idan nata ne kuwa wanda za ta aiko mana bai fi yara huɗu su cinye shi ba haka za mu kasafta mu wuni da yunwa.

Kayan abinci kuwa tuni sun koma sama sai ranar girkinmu za mu hau mu ɗebo,
ita da ma Hajja aikawa take, hakanan dai muke zaune ga mu nan dai

Watanta uku aka saki Hajja ta tsallake tulin yaranta ta tafi ta bar ni cikin fitinar, sai ya zam amaryar ta janye ƙananan ya’yan idan ta rage abu sai ta kira su ta ba su, ta kitsa musu abu ta ce su ce wa baban su ni na yi musu, haka Malam zai kira ni ga shi ga amarya zaune ga yaron da aka ce na yi wa abu ya yi min tatas yana kira na tsohuwar banza.

A sannan ne Amir ya tsira kukan dare domin ya saba da shan fura da Malam ke shigowa da ita yanzu kam ya daina sai dai ya shigo musu shi da amarya idan an dama a juye mata madara peak.

Haka zai leƙo daga sama ya yi ta antaya min zagi wai zan hana shi jin daɗi saboda mugun halina.

Gabaɗaya na fita hayyacina na rame na fice, ana haka aka roƙi Malam da ƙyar ya maido Hajja.

Ita ma da ta dawo ba ta shiga harkata ban shiga ta ta, Malam kuma tsakanin mu sai dai mu hango shi daga sama ko in ya sauko zai fice.

Amarya kuma duk yamma za ta sanya kujera a caɓa adon nan wanda a wuni ta kan canza kaya sau huɗu ga gwal wuya da hannu da yan yatsu suna sheƙi.
Ta ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya tana kallo mu daga sama a haka za su riƙa hira da Hajja, ina furta daya za ta ɗanƙara min magana don haka ban fiye tsoma musu baki ba.

Ranar da Allah ya kawo ƙarshen zaman na je Dukku na yi kwana uku da zan dawo babana ya bani kuɗi ya ce ki samu ki ɗan sayi abin da kike so kuma ki kwantar da hankalinki mai gadon zinare.

Da na dawo sai na yanke yin sana’a saboda zaman haka yana damu na sai Naira goma ta gagare ni ba kamar da ba da Malam ke ninka kudin cefane yadda za ka samu.
Wani ɗan yayan Malam na kira na ba shi kuɗin na ce ya saro min itace ganin kullum sai mun sawo, ya sawo ya kawo min.

A daren Amir ya yi ta tsala kuka duk da ya wuce goyo hakanan na goya shi ina rarashin shi yana ihun zai sha fura, ga shi ban rage komai a kuɗin ba ballantana in sai mishi furar,kamar yadda ya saba Malam ya leƙo daga sama yana surfa min zagi.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 3.3 / 5. Rating: 4

As you found it interesting...

Follow us to see more!

Mutum Da Kaddararsa 2 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×