Rana ɗaya da tsautsayi ya gifta sai na amsa mishi don raina ya yi ƙololuwar ɓaci da zagin cin mutuncin da yake min. Ya ce da safe in wuce gidanmu ya sake ni!Ɗif!
Na ɗauke wuta na koma ɗaki na haɗa kai da gwiwa, Amir na kuka ni ma ina nawa kukan. Ni kuma tawa ƙaddarar kenan ta mutuwar aure, kwata kwata shekaruna nawa har na yi aure biyu? Duk da ba daɗin zaman nake ji ba, ban kuma sha’awar komawa zawarci. Kafin wayewar gari na ci kukana ya ishe ni.
Garin na wayewa kuma na aika aka kira min wanda ya saro min itace na faɗa mishi abin da ya faru na roƙe shi ya mayar musu ya yi musu bayanin matsalar da aka samu, sosai ya nuna baƙin cikinsa don ɗan ɗakina ne. Ba musu suka karɓa aka ba shi kuɗaɗena ya kawo min na jefa a jaka da ma na kintsa yan kayana na goya Amir na bar gidan.
Ka sa nufar gidan iya na yi wato uwar goyona na nufi gidanmu, babana ya ba ni matuƙar tausayi kan halin da ya shiga a dalilin mutuwar aurena, na yi sa’a matar babana ta bar ni na zauna a gidan.
Watana ɗaya kacal sai ga ƙanwar babana Gwoggo Maryama ta zo daga Malumfashi inda take aure can jihar Katsina. Ta yi baƙin ciki ƙwarai da mutuwar aurena a karo na biyu ta ce in shirya in bi ta ban yi musu ba haka ma babana sai ma daɗi da na ji zan yi nesa da Dukku. Sati guda za ta yi, kwananta uku sai ga Aminu mijina na farko baban Amir wai ya zo karɓar dansa daga ya ji labarin na yi aure. Hankalina ba ƙaramin tashi ya yi ba na shiga ɗaki na yi ta kuka don babana ya ce in yi haƙuri in ba shi ɗan shi, aka ba shi suka juya.
Gwoggo Maryama ke ta rarrashina da kalamai masu daɗi. Kafin mu tafi na je na yi wa Iya sallama sai ga kayan ɗakina Malam ya sanya a mota ya aiko min da su, Gwoggo ta ce a sayar kawai kuɗaɗen za ta bayar a juya min. Sai da aka sayar muka kama hanya. Yamma liƙis muka sauka a unguwar Tudun Bala gidan Gwoggo Maryama yake, gidan gida ne babba kuma mai kyau daga ita sai yaranta sai maigidanta mijinta mutum ne mai rufin asiri tana ji da ni gami da tarairaya ta, kafin ta ba yaranta abu ta bani, ta amso min Form na shiga makarantar islamiyyar da take zuwa nan da nan na gyagije na yi kyan gani ga Islamiyyar ba ƙaramar karuwa nake samu ba.
Abu ɗaya ke haɗa ni da ita maza da suka fara sallama da ni, ni kuma ba na son fita yadda nake ce mata na gama aure ta yi ta min faɗa. Watana takwas garin na yi matuƙar canzawa saboda na samu jin daɗi da kwanciyar hankalin da tsawon rayuwata ban taɓa samu ba. Wani dare ina kwance a ɗakina ni kaɗai karatun islamiya nake yi yarinyar Gwoggota mai shekaru goma ta yi sallama ta ce min “Aunty Bilki ki zo babanmu na kira.” Gabana na ji ya buga don abin da bai taɓa faruwa ba kenan, tsakani na da shi gaisuwa ce.
Na ce “Me aka yi Bilkisu? Don sunan mu ɗaya da ita. Hannunta ɗaya ta buga kan ɗaya ta ce ba ta sani ba. Hijab na janyo na sanya sai na fito daga ƙofar falonsa na tsaya na yi sallama su biyu suka amsa ya ce in shigo, na shiga na zauna a ƙasa na ƙara gaishe shi ya amsa sannan ya ce “Na aika a kira ki ne Bilkisu wani yaro Hassan a nan bayan mu yake ya aiko a shaida min yana neman izinin fara neman ki.
Da na faɗa wa uwar taku sai ta ce ai duk wanda ya zo ba ki so, to gaskiya Hassan yaron kirki ne kowa ya san shi anan ɗin, ina miki sha’awar samun shi in sha Allah daga shi kin gama wannan aure auren da na san shi ne ya ishe ki, matarsa mutuwa ta yi ba ta taɓa haihuwa ba, zai zo ku ga juna don Allah ki kwantar da hankalinki in har ya yi miki to kin yi miji.Na yi mishi godiya ya sallame ni na tashi na tafi.
Da na koma ɗaki kasa ci-gaba da karatun da nake kafin kiran na yi na kafa tagumi hannu bi biyu, aure ya fita raina duka biyun da na yi ba wanda na ji daɗin shi, a ƙananun shekaruna da ni wata mai gata ce da karatu na koma na inganta rayuwata na fita batun maza to amma ya zan yi ya zan yi da wannan ƙaddara? Na raba tsawon dare idona biyu kafin in samu barcin da ya ja min makara.
Ƙarfe huɗu da minti biyar na yammaci na fito cikin kwalliya ina fitar da ƙamshi ɗakin Gwoggo Maryama na shiga da na samu tana gyara kayan wardrobe ɗinta ta bi ni da murmushi ni ma ina murmushin na zauna bakin gadonta.
Ta ce min “Za ku je ke da Bilkisu gidan telata ku karɓo min ɗinkunana.” Na ɗaga mata kai sai na miƙe don nemo Bilkisun. Na samu tana wanka na ce idan ta idar ta same ni ɗakin Gwoggo inda na tashi na koma na zauna har Bilkisun ta shirya ta zo ta same ni sai muka fito jikin gidan maza ne zazzune an yi shinfiɗa suna ta shan shayi da cin nama ba tun yau ba ba na son fita ranakun Asabar da Lahadi saboda jikin gidan su Gwoggo akwai ɗan gidan ɗan majalisar jiha duk weekend yake shigowa Malumfashi da kuma ya zo ba ka raba ƙofar gidan da jama’a, ni dai har ina harɗewa muka samu muka shiga lungu.
Layi ɗaya ne tsakanin mu da gidan mai ɗinkin, mun shiga mun amso mun fito mun fara tafiya wani yaro ya tsayar da mu wata baƙar leda ya miƙo min ya ce in ji Hassan mai shago. Dan jim na yi kafin na ce “Ina Hassan mai shagon? Da hannunsa ya nuna min shagon ƙwarai na san shagon har ma na gane Hassan ɗin da ake magana katangarsu ɗaya da gidan telar da muka je har sayayya na sha zuwa yi wa Gwoggo idan ba yara gidan.Kamar kar in karɓa sai na tuna maganganun da babansu Bilkisu ya faɗa min kan shi na amsa na ce ka ce mishi na gode.
Na ba Bilkisu ta riƙe.Muna zuwa dab da gidan mazan suna nan sai ma ƙaruwa da suka yi na ƙara riƙe hannun Bilkisu tamau kaina na ƙasa muka samu muka shige gida.Da muka ba ta sakon na karɓe ta girkin duk da ba cika son wani ya yi mata girki in har har da mijinta a abincin.Muka zauna a wani falo ni da yaranta hudu,don biyun na farko mata ne kuma sun yi aure, nan yaran gidan ke taruwa don ban da nata falon akwai kuma wannan. Muna cin abincin dare ta shigo wayarta ta miƙo min na sa hannu na karɓa ta ce, “Ki yi amfani da ita.”
Cikin matuƙar jin daɗi na shiga mata godiya, Salim yaronta na uku ya ce “Amma Mama na fa riga, na ce miki idan an canza miki wata za ki bani ita.” Ta ɗaure fuska “To ban yi niyya ba.” Ta juya sai ya taso ya dawo kusa da ni “Kin more Aunty Bilkisu, don wayar Mama ba ta yi komai ba ta fi tawa.”Na ce “Kai da ka so kar a bani a ba ka.”Murmushi ya yi ya miƙo hannu na ba shi wayar ya haɗa ta da tsohuwar tawa wai zai buɗe min whatsapp da facebook.Miƙewa na yi don na ƙare cin abincin na kai flate ɗin kitchen na ɗauraye na kife sai na fito ina shiga ɗaki Gwoggo Maryama ta shigo “Yau fa Hassan zai zo Bilkisu, ki samu ki yi wanka ki gyara jikinki kafin isowar shi.
“Baki na kama “Har da wanka Gwoggo? Ta ɓata rai na yi saurin cewa “Yi haƙuri Gwoggo.” Na fara tuɓe riga Bilkisu ta shigo “Aunty Bilki ana kiran ki a waje.” Gwoggo ta ce min.
“Kin gani ko? Dole ta haƙura da zancen wanka na gyara fuskata na fesa turare na zura hijab tana ta min nasiha da nuna min in faɗa mishi kalamai masu daɗi aure shi ne mutuncin ya mace. Na fita a hankali nake takawa har ƙaton filin tsakar gidan daidai jikin motar babansu Bilkisu na hange shi tsaye yana ganina shi ma ya taho ya tarye ni “Barka da fitowa sarauniya Bilkisu, mai gadon zinari.” Dole na murmusa duk da takaici gami da fargaba da na fito da su.
Jikin motar muka koma na gaishe shi ta gefen hijab ɗina nake satar kallon shi. Cikakken namiji da duk mace za ta yi ma kanta sha’awar samun shi sai dai rashin cikakkiyar wadata ta masu gidan rana ta rage armashin fitowar kamalar ta sa, ko da yake ba wasu tsadaddun tufafi ya sanya ba yan kadaran kadahan din da ya sa sun sha wanki da guga ga ƙamshi yana ta yi.Ya shaida min ya yi karatu har zuwa matakin digiri inda ya karanci fannin zane zane rashin samun aiki ya sa ya mayar da hankali a shagonsa da yake sana’ar sayar da kayan masarufi yana kula da kanshi da Mahaifiyarsa.
Mun daɗe duk da ban wani saki jiki da shi ba kalamansa masu cike da nutsuwa da hankali sun tsaya a zuciyata.Da na kwanta daɗewa na yi ban yi barci ba.Bayan zuwan shi na farko kwana biyu aka ƙara sai ga shi ya dawo.Sannu-sannu sai na yi sabo da shi ya kuma shiga zuciyata kamar yadda na gane ƙauna ba ta wasa ba yake min.Duk bayan kwana biyu zai aiko min da kayan shayi da sabulai na wanka, sai da baban su Bilkisu ya yi tsawa kan hakan.
Watan mu biyu wanda duk da tsoron maza da nake da kuma yin wani auren zuciyata ta amince da Hassan, a makaranta na sanya a taya ni addu’a na samu malamarmu a keɓe na faɗa mata kullum kuma aka tashi ba ta taɓa fashin sanyawa a yi addu’ar ba. Ni ma na dage da tsayuwar dare ina yi ma kaina addu’a.Kwatsam! Sai ga saƙo daga wannan ɗan majalisar jihar yana neman izni zai shigo neman aurena, baban su Bilkisu ya yi mishi izni.
Ranar farko da ya fara zuwa na ga hidimar arziƙi Boot ne aka ciko da suturu na kece raini bayan kayan maƙulashe da aka yi wa naira ta’adi mai yawa wurin mallakar su.A falon baban Bilkisu aka sauke shi an yi mishi soye soye na kaji da cincin har da cake, Gwoggo Maryama kuma ta sanya ni yin kwalliya wadda har na yi ta kallon kaina a madubi don na yi kyau ba kaɗan ba.
Da zai wuce rafar ɗari biyar ya ajiye min.Tun daga ranar kuma duk ƙarshen mako idan ya shigo gari sai ya zo wajena kyauta kuma ta girma yake min zuwan shi huɗu kawai ya nemi zai kawo kayan aure a yadda na ji matansa biyu wasu sun tafi yana da yara sun kai ashirin ya min alƙawarin sai garin da na zaɓa zai ajiye ni.
Hankalina ya ƙi kwanciya da shi duk da ra’ayin da Gwoggo Maryama ke cusa min in ce ya turo kawai wa ke son wahala, ga ƙawayenta da abokan arziki da ke zuwa mata murna da wannan babban mutumi da na samu.Ranar da ya aiko sai ga Hassan da daddare cikin damuwa yake ƙwarai, kalamai ya yi ta faɗa min cikin rauni na cewa yana ji a jikinsa ya rasa ni don ba zai iya karawa da Yallaɓai Hashim Bello ba.