Skip to content
Part 15 of 64 in the Series Mutum Da Kaddararsa by Maryam Ibrahim Litee

Tun safe da muka tafi ba mu samu mun dawo ba sai sha biyu na rana.

Gwaji dai ya tabbatar da lafiyar Aminu ƙalau.
Muna dawowa aka shiga shirin ɗaurin aure, yan’uwan Aminu sun zo da sadaki dubu ɗari da kuma kayan lefe akwati uku, ana kammala ɗaurin aure babana ya gana da waliyan Aminu kan cewa bai saya min kayan daki ba saboda nisa ɗaukar su zai zama wahala, dubu ɗari uku ya ba su aka haɗa da sadakin suka zama ɗari huɗu, ya ce in sun isa a saya min kayan gado da kayan amfani.

Wajejen La’asar muka baro Dukku tare da mutane goma waɗanda za su yi min rakiya.
Rashin tasowa da wuri da kuma tsananin nisan da ke tsakanin Dukku zuwa Kaduna ya sa ba mu iso ba sai cikin dare sosai.

A kurmin mashi gidan su Aminu yake kusa da gidan mahaifiyarsa ya kama ɗaki room and parlor, mata uku ne sai ni ta huɗu.

Mu dai ba mu samu ganin inda muka zo ba sai da safe, daga gidan mahaifiyarsa aka kawo mana abin karyawa muka yi wanka sai dangin Aminu ke ta tirirrishin gani na.

A ranar kuma suke nasu taron, waliyan Aminu sun miƙa kuɗaɗen da babana ya ba su ga mahaifiyarsa, sun ta juya kudin karshe yayyen Aminu biyu mata daya bazawara dayar ce matar aure su aka
ba kuɗin suka shiga kasuwa suka sawo min kayan daki daidai da kudin da babana ya bayar ba a samu shirya min daki ba sai washegari yan rakiyata suka yi sammako suka kama hanya.

Yan’uwan Aminu suka gyara min ɗaki suka kuma kai ni wurin mahaifiyarsa da gidan kawun shi da ke kusa kafin suka dawo da ni ɗakina, su suka sanya ni na yi wanka na canza kwalliya.

Magribar fari sai ga anguna ni dai na rufe ido duk hirar da suke da dararraku da tafawa ban buɗe fuska ba.

Sun daɗe sosai kafin suka tafi bai fita rakiyar su ba wanda shaƙiyanci sosai suka yi mishi maganganun da suke yi suka yi min banbaraƙwai don ban ji alamar tarbiyya ba a cikin su.

Gabana ya taso ya tsaya ya fara sauke lilliɓin da ke kaina ganin ya raba ni da lilliɓin ya sa na kai hannayena na rufe
fuskata sai na shi hannayen na ji saman nawa na yi ƙoƙarin janyewa sai ya rungume ni gabaɗaya, duk da ban yi yunƙurin ƙwacewa ba gabana ya shiga dokawa daga abu ne wanda ba a taɓa yi min ba.

Sosai ya murje ni kafin ya bar ni ya ɗauko naman da suka shigo da shi, ni dai kasa ci na yi saboda nauyin shi da nake ji, da ya gama ci ya janyo ni zuwa gado amma na ce ban yi Isha’i ba, ɓata fuska na ga ya yi sai dai bai yi magana ba da haka na sauka na fita na yi alwala na shigo na yi sallah ina addu’a sau biyu yana ce min har yanzu ba ki gama ba?

Na miƙe na ɗauko rigar barci cikin kayan akwatina na koma falo na sauya, na juya zan shiga dakin sai na gan shi tsaye kaina sunkuyar da kaina na yi don daga shi sai guntun wando kuma har auren bai sa ya cire daadar da ke kan shi ba, ya ja ni zuwa gado.
Wata irin wahala da ban taɓa jin irin ta ba zan ce na sha a wannan dare sam bai saurara min ba, tun kuma da na samu ya sarara min ya shiga barci ni kuma ganin har an idar da sallah a masallatai ya sa dole duk da halin da nake ciki ban iya komawa na kwanta ba sabuwar Kettle ɗina na jona da na yi sa’a akwai wuta tana tafasa na juye na je na yi wanka na yi alwala na zo na yi sallah.

A inda na yi sallar nan na ɓingire ban tashi ba sai dai na ji Aminu na tashi na, abin karyawa ya bani umarni in yi ruwan zafi na tafasa na soya ƙwan da ya fita ya sawo muka sha da bread.

Da yake na yi wanka kwalliya kawai na yi na canza kaya.

Wunin ranar Aminu na gida bai fita ba muna amarci duk da yan’uwansa da ke ta shigowa.
Haka washegari ma bai fita ba kwana na uku ya fita kan aikinsa yana aiki da wani kamfani ne na sarrafa man gyaɗa.

Aikin na shi daga safe ne zuwa Azahar sai ya dawo gida ya yi barci har sai La’asar zai tashi ya fesa wanka ya dau ado ya fice, duk inda aka yi Isha’i kuma zai dawo, gidan mamansa nake tafiya idan ya fita har sai ya dawo ya je mu dawo tare.

Wata uku muka ɗauka muna zaune lafiya cikin soyayya har sai da na faɗa cikin laulayi mai tsanani wanda muka je asibiti da yayarsa mai zaman gida Abu tun daga nan Aminu ya canza idan ya dawo ya yi barcinsa ya yi wanka ya fita ba zai dawo ba sai goma na dare idan na yi magana sai ya hau zagina.

Ni kaɗai nake wahalar laulayina ba wani nuna kulawa ko tausayi da nake samu,idan na yi mishi magana ko ya zazzage ni ko ya faɗa wa mahaifiyarsa, ita kuma idan na je ta yi ta min faɗa.

Sai ta kai yana kwance kan gadona zan ji yana waya da yammata, nan na fara gane bakin zaren, ko yana kwancen aka kira shi zai tsallake ni ya tafi.

Ranar da wata ta kira shi ya kuma fesa wanka ya wuce ya tafi ban da daadar da ke kansa har ɗankunne guda ya maƙala ga sarƙa da da ma duk gayun da zai yi sai ya sanya ta.

Ban fita zuwa gidan mahaifiyarsa ba don ban jin daɗi tun wani ɗan wake da na ci zuciyata ke ta tashi yana tafiya na fara amai, na yi ya yi sau huɗu jikina ya saki na kwanta ina mayar da numfashi.

A daddafe na tashi na yi sallah ban ƙara cin komai ba, sai goma da rabi ya dawo, cikin halin galabaita na ce “Saboda Allah Aminu sai ka tsallake ni ka yi tafiyarka wurin yan iska ina kwance ina fama da kaina? Ka duba agogo yanzu ya kamata ka dawo?

Ya yi kaina yana ɗura min zagi na ce “Ba dai iyayena ba.”

Ai kam sai zagi da duka ko ta ina na shiga kuka ya zare belt ɗin jikinsa yana lafta min har saida mijin matar kusa da dakina ya shigo ya fita da shi. kwanciya kawai na yi ina kuka.
Da safe da ma sammako yake yi yana tashi ya yi tafiyarsa ya bar ni cikin wani irin ciwon kai da jiki ga fuskata da ta kumbure saboda marukan da ya yi ta kifa min.

Yinin ranar a ɗaki na yi shi da ya dawo kuma ko inda nake bai kalla ba wankan shi ya fesa ya kuma ficewa.

Sai washegari da na ga fuskata ta ɗan yi sauƙi sai na fita zuwa gidan mamansa, ina zama Abu ta riƙe baki “Wai! Haka kika ja wa kanki?
Uwar ma ta fito “Ba ki jin magana Bilkisu, ina za ki ce za ki hana namiji yin yammata?

A raina na cika da mamakin su musamman mahaifiyar ta su yammata ba dai irin na Aminu ba don yanzu na gane bakin zaren sarai na san yammatan na watsewa ne.
Suka yi ta maganganun su ina jin su har sai magrib na tashi na yi tafiyata ban tsaya jiran sai ya zo ba.

Sai ga shi da wuri ya dawo sai na gane buƙatata ta dawo da shi na kuma yi mursisi na ƙi yarda dambe sosai muka yi duk da dukan da yake min waje ya tura ni ya ce ya sake ni! Na fita zuwa gidan mahaifiyarsa anan na kwana da safe ita da aminiyarta da aka yi min uwarɗaki da ita suka je suka ba shi haƙuri da roƙon ya mayar da ni da ya mayar da ni sai suka dawo suka yi ta min faɗa in bi mijina, uwarɗakin tawa ta mayar da ni dakin ta ƙara min nasiha,tana wucewa kuma yana kwance gado ya ce in zo dole ina matse ido na amsa kiran shi.

Haka rayuwar aurenmu ta cigaba duka nake sha ba na wasa ba hannun Aminu saboda shiga al’amarin shi da yammatansa da na kasa kawar da ido.

Cikina na da watanni bakwai ya yi min wani duka da na kasa jurewa na ɗauki wani murfin kwano na rafka mashi a goshi take goshin ya fashe jini kuma ya shiga gudu.

To ranar kam na ga fushin mahaifiyarsa ta zage ni tas.

Tun kuma ranar da ya fara duka na samun abu nake in ƙwala mishi, hakan ya ja mahaifiyarsa ta ce ya dawo ɗakinta ya bar min dakin kar in sabauta shi.

Aka bar ni ni kaɗai da tsohon cikina sai da ya yi sati biyu ya dawo kwana ɗaya kawai ya yi da dawowa na haihu Maman Amina wadda aka yi min uwar ɗaki da ita ita ya kira ta yi min komai, ita kuma ke zuwa kullum tana yi min wanka ni da jaririna.

Ranar suna ba wanda ya zo ta fannina daga Dukku mun dai yi waya.

Duk sha’ani idan ya tashi na yan’uwan Aminu haɗuwa ake duka a tafi Aminu ke bani kuɗin mota ranar da yake jin tsiya sai ya hana ni dole in zauna ina kallo a tafi a bar ni ganin haka ya sa uwar ɗakina ta shawarce ni in fara sana’a na ciro zannuwan da na samu haihuwar Sulaiman da ya ci sunan mahaifin su Aminu muna kiran shi Amir in sayar in yi jari na kayan kwalliya da na ga matan yan’uwansa na yawan saye, da na yi mishi magana ya ce ba dai gidan shi ba.

Har mamansa na fada ma wa ko za ta yi masa magana ta ce ba gidansa ba ne daga ya ce ba ya so ba shi kenan ba.

Dole yawancin hidimata ta koma kan babana shi ke turo min kuɗaɗe in yi yan lalurorina.

Sai da Amir ya yi wata biyar na tafi Dukku, satina biyu na dawo kamar yadda ya bani.
Innakeso yanzu mutunci ne a tsakanin mu tunda ta san ba zan dawo in zauna mata gida ba, hakanan za ka ga ta kira ni a waya.

Ranar da Aminu ya min saki na biyu babban abokinsa ya zo yana wata fara’a gabaɗaya haushin shi nake ji, sai da na ɗaure na ce mishi Ina kwana a daƙile sai na ci-gaba da ayyukana, ya yi ta yi wa Amir wasa har Aminun ya gama shirin shi suka bar gidan.

Ya dawo ina kaye-kaye zan kwanta ya ce “Ke don uwarki me ya sa ba ki gaishe da Ɗan Alh ba? Na dube shi “Ya kake zagina? Na gaishe shi mana.”

An zage ki don uwarki, ya ƙara zuwa gidan nan ba ki gaishe shi ba in ban ci uwarki ba.”
Na ce “A’a wai me na yi maka za ka yi ta zagin uwata ka bari.”

“In ban bari ba fa? Kafin in ce wani abu sai duka duka sosai ya yi min ya ce ya sake ni, na bar gidan ina kuka zuwa gidan Mamansa na faɗi mata abin da ya faru na kuma roƙe ta ta haɗa ni da wani ya yi min rakiya in ɗauko kayana da Amir.

Ta ce in kwanta Abu ta je ta dauko Amir ɗin.
Da safe suka hana ni tafiya suka haɗu har Maman Amina suka je suka yi ta lallashin shi ya buɗe min ƙofa sai da na kuma kwana suka ciyo kanshi ya buɗe min ɗaki, na koma ɗakina na yi wanka na gyara jikina sai na kira babana a waya ina kuka na ba shi labarin halin da na shiga ya ce in yi hakuri, don ko ya ce in taho nan ɗin ma meye? Allah na sane da mu zai kuma kawo mana mafita.

Ya kira Aminu ya ce mishi bai son duka, waɗanda aka yi baya sun isa, amma ya kuma dukana zai ɗauki mataki.

Kwana bakwai tsakani ya min dukan tsiya ya ce in gaya ma duk uban da zan gaya mawa ya daɗe bai kashe auren ba.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Mutum Da Kaddararsa 14Mutum Da Kaddararsa 16 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×