A yanzu kam an kai gaɓar da na ma daina firgita da al'amarin shi, abin sai hum da hum wai uwar gulma ta yi cikin shege."
"Za mu fita ki shaƙata amma don Allah ki bar wannan ƙauyancin kina wani kama jiki." Ya cigaba jin na yi shiru ban kuma tsinka mishi ba hammar ƙarya na yi ta jerawa dole ya sallame ni na shiga da ledar zan haye gadon Zainab ta ce "Barii dai in kaiki gadon nan." Ta kamo ni kamar wata yar yarinya ta kai ni gadon.
Khadijan da ta wuto mu muna zaune. . .