Rana ɗaya da tsautsayi ya gifta sai na amsa mishi don raina ya yi ƙololuwar ɓaci da zagin cin mutuncin da yake min. Ya ce da safe in wuce gidanmu ya sake ni!Ɗif!
Na ɗauke wuta na koma ɗaki na haɗa kai da gwiwa, Amir na kuka ni ma ina nawa kukan. Ni kuma tawa ƙaddarar kenan ta mutuwar aure, kwata kwata shekaruna nawa har na yi aure biyu? Duk da ba daɗin zaman nake ji ba, ban kuma sha'awar komawa zawarci. Kafin wayewar gari na ci kukana ya ishe ni.
Garin na wayewa kuma na. . .