Kan cinyata na ɗora ta na ɓare mata su Mami suka bi mu da kallon mamaki.
Da na mike zuwa kitchen sai ta bi ni a baya, haka ma da za ni ɗaki sai muka yi zaman mu a dakin, na bata wayata tana game.
Bini bini Safwan yake duban kofar da ya ga sun bi don yana so a kawo mishi yar shi su tafi gida, ganin ba alamar fitowar su ya dubi matarsa "Oya karɓo Afnan mu wuce."Har ta miƙe Mami ta ce "Ku bar min ita tunda sai wani satin za ku sanya ta. . .