Skip to content
Part 27 of 64 in the Series Mutum Da Kaddararsa by Maryam Ibrahim Litee

Kan cinyata na ɗora ta na ɓare mata su Mami suka bi mu da kallon mamaki.

Da na mike zuwa kitchen sai ta bi ni a baya, haka ma da za ni ɗaki sai muka yi zaman mu a dakin, na bata wayata tana game.

Bini bini Safwan yake duban kofar da ya ga sun bi don yana so a kawo mishi yar shi su tafi gida, ganin ba alamar fitowar su ya dubi matarsa “Oya karɓo Afnan mu wuce.”
Har ta miƙe Mami ta ce “Ku bar min ita tunda sai wani satin za ku sanya ta makaranta, idan kun koma ki ba direba kayanta ya kawo min.”
Daga uban har uwar kan ba yadda za su yi da Mamin suka amsa umarnin ta.

Sama ya hau don yi wa daddy sallama ta take mishi baya, da suka sauko ta ce “Bari in yi wa Nana sallama.”

Samun mu da ta yi mun bararraje a gado kan Afnan na bisa cinyata tana game da fara’a na dube ta “Ba dai har za ku wuce ba?

Ai kuwa tafiya za mu yi.”
Na bi bayanta bayan na saɓa Afnan a kafaɗa duk da ƙibar ta, sai da na raka Aunty Farha har mota ina mata su huta gajiya.

Ranar gidan mun ƙara samun walwala saboda zuwan Afnan duk inda na sanya ƙafata nan za ta mayar da ta ta, tare muka kwana.

Da safe ma ni na yi mata wanka, mun yi barcin rana mun tashi da muka fito na ga su Farha sun zo yarinyar ta kama tsalle ta ruga wurin babanta ya cafe ta yana murmushi mai bayyana haƙora.

Kusa da Aunty Farha na zauna na gaishe su, sun daɗe don sai dare suka tafi.

Abin da ya dinga faruwa kenan duk yamma za su zo a yi hira har satin ya kare suka dauki ɗiyarsu.

Washegarin da suka dauke ta ba su zo ba.

Zuwa lokacin mun yi matuƙar sabawa da Ummu hani ta yawan chatting da muke har ma da waya.

Wani dare na gama komai na al’adar rayuwata na hau gado wayata ta soma ɓurari na buɗe idanuwana da na soma rufewa na kai hannu kan wayar nomber ce ba suna na yi picking cike da mamakin me kira na a daidai wannan lokaci, sai dariyar Farha na ji, gyara zama na yi “Aunty Farha.” Ta amsa “Na’am.” Na ce “Shi ne yau ku ka ƙi zuwa ina my Afnan?

“Ga ta nan ta yi barci.”

Yau ai mun sha labarin ki Auntyn Afnan, tunda ba mu zo ba ai ke gobe sai ki zo.”

Shiru na yi kafin ta ɗora”Goben za ki zo ko? Saurin cewa A’a” na yi na ce “Don Allah ni dai ku zo ku kawo min Afnan.”

“Ba tabbas zuwan mu Nana kin ga Dear ya koma harkokin shi, Afnan ta shiga Sch sai dai zuwa Weekend.

Sai da na yi saving din nombarta sai na kwanta.

Da safe da muka yi break fast ban koma barci ba kitchen na shiga wurin masu aiki inda suke kacaniyar haɗa abincin rana suna girkin su na haɗa milk shake wanda ya yi min daɗi don haka na sanya a glass cup na ɗora kan wani madaidaicin tray na nufi dakin Mami don ina yawan yin dan abun marmari in kai musu ita da Daddy, na murɗa handle ɗin kofar bedroom ɗin Mami sai dai abin da na gani ya sani saurin sunkuyar da kaina hannuna ya ɗauki rawa Sadaukin Mami ne kishingiɗe a gadon Mamin yana fuskantar ƙofa.

Mutum ne shi wanda Allah ya yi wa baiwar kwarjini dogo ne da ke tafe da jikinshi ma’ana Giant ne ba shi da hasken fata ƙaƙƙarfa ne wanda daga yadda yake taka ƙasa ma idan yana tafiya za ka tabbatar da hakan.
Jama’a na bala’in shakkar shi ba kuma don yana musu komai ba sai dan baiwar kwarjini da ubangijin halittu ya yi masa.

ÀMami na zaune saman sallayarta, daburcewar da na yi ta sa tray din suɓucewa a hannuna cup da tray suka watse milk shake din ya samu matsuguni a tattausan carpet ɗin da ke malale yayin da Mami ke faɗin,

“Subhanallah garin yaya Bilkisu?
Safwan tsawa ya daka min yana faɗin “Wane irin shashanci ne haka?

Juyawa na yi sai na bar dakin don samo abin da zan gyara wurin da shi, na tsuguna Mami ta ce in bar shi in turo cikin masu aikinta ta gyara.

Na fice jikina a mace na isa ɗakina ina tunanin ƙorafin da Farha take mini na na ki zuwa gidanta, ni kam tsoron ya Safwan nake yi ban ma je gidan shi ba yana min irin wannan tsawar ina ga na kai kaina?

Muryar Mami da na ji kaina ta sa ni daga kai kira na ta yi in zo in taya ta kwance kanta.
Da na fito ya Safwan ya fita san da na gama mata na koma daki missed call din Ummu hani na tarar tururu cikin mamaki na zauna bakin gado sai na kiran ta “Don Allah ina kika shiga kika bar wayar?

Abin da ta ce min kenan daga ɗagawar ta “Ki bari kawai ni kin ɗaga min hankali me ya faru?

“Albishir zan miki Habibi ya kankaro min girma danƙareren gida ya saya min a Abuja, Abujar ma a Maitama karshen satin nan zan dawo.”

Na ce “Ina taya murna, ga shi kuma unguwarmu ɗaya.

Shi ne ai daɗi ya ƙara kama ni muna unguwa daya.

“Na yi murna kwarai Allah ya sa alheri.”
Ta ce “Amin, bari in je habibi na kira.”
Ta ce “Hmmm Habibi zama yake? Kullum ba shi can ba shi nan jiya ya zo gobe zai wuce Lagos, ko dawowar ma ni kaɗai zan dawo sai yan’uwana da za su yi min rakiya.”

Na ce “Allah ya kawo ku lfy ina gaida Habibi.”
Na katse kiran ina murmushi ita dai kullum korafinta daya mijinta ba ya zama, da na fito na shaida wa Mami dawowar Ummu hani Abuja muka ɗan yi maganar.

Ranar da za ta dawo suna shigowa garin ta kira ni sai da ta ba ni tabbacin sun isa gidan na ce mata gani nan Na sanya abincin da na yi musu a mota na yi ma Mami sallama muka fita da direba duk da Mami ta sanya an koya min mota tun farkon dawowa ta ina bin address ɗin da ta ba ni muka isa gidan.

Ita da yan’uwanta su biyar suka zo.
Muka gaggaisa da su na ba su abincin da na kawo masu.

Ta ja ni bedroom ɗin da ta zaɓar ma kanta domin an shirya ko’ina tsaf, sai da muka zauna bakin gadon ta ce “Kin ga gidan da Habibi ya tamfatsa min ko Billy? Ya yi biyun na mu na Kano a kyau, wai waɗancan tarkacen su ma za su zo na taka musu burki.”

Cikin rashin fahimta na ce “Su wa ye? Sai da ta gatsina baki ta ce ” Yanuwan Habibi da uwar shi mana.”

Na bude ido ”

Ke har uwar za ki yi wa rashin mutunci? Ta ce “Cab? Ni idan ban mata ba ita za ta fara yi min.”

Na jinjina kai ina tuna zama na da uwar Hassan da yan’uwansa ni so nake ma a zauna lafiya amma sai da aka tunɓuke ni na bar gidan.

“Ki bar wani kaɗa kai uwar mijin nan tawa ba ta da daɗi kamar aiki take, kafin ni mata biyu ya yi, ta farko da yake ita ta nema mishi ita bai kuma wani maida hankali kanta ba ba ta tsangwame ta ba, mutuwa ta yi.

Ta biyun kuwa ita ta sa na ɗauki matakin da nake akai. An ce ta yi mata biyayya kamar ta yi mata sujjada amma matar nan ta tasa ta a gaba sai da ta kore ta, shi ɗin ma har yau yana son ta na yi na yi in yakice mashi ita a ran shi ,abin ya gagara.

Shi ne ta wani zo wurin Babana tana roƙo a ba ɗanta ni su yi tuwon su man su.

Na ƙara gwalo ido ina buɗe baki “Kina nufin akwai dangantaka a tsakanin ku ? Ta juya ido “Ƙwarai ƙanwar babana ce ubansu guda, ko me ɗan nata zai mata sai ya biyo ta hannuna in mata yadda na ga dama in zai hukunta ni ta hana tana tsoron idanun dangi da ke kanta duk da ban mata akan idon shi.

Na ce “Allah ki ji tsoron Allah ni ya za a yi in fara ma Gwoggona haka?

Ta ce “Tana da kirki ne amma ban da yan’uwan Habibi da uwar su.”

Na haɗiye miyau ina shirin yin magana wayarta ta ɗauki ƙara ganin sunan mai kiran ta tamke fuska kamar mai kiran na ganin ta sannan ta amsa Allah ya sa alheri ake mata tana amsawa a yatsine, da ta gama ta ce “Kin san su waye ? Na kaɗa kai “Maman Habibi ce da ya’yanta suna can duk an sako mata su sun haɗa kai suna famar sharri sai daya ke gidan aure, amma ƙaramar yanzu auren ta uku da ta yi ake sako ta to abin da uwar su ta ƙulla wa yar wasu.”

Na ce “Allah ya kyauta ina miƙewa
“To za mu samu ganin Habibin in mishi murna ko in yi tafiyata?

Ta ce “Habibi baya ma garin kin manta na faɗa miki baya nan zan dawo ina dai ta mishi addu’a kar wadda ta gan shi ta ƙyasa, don ni yawan yawon Habibi na kasuwanci yana damuna kullum ba ma tare.”

Na yi ɗan murmushi “Hajiyar kishi.”
Ta ce “Bar ni in yi kishina Habibina ya haɗe duk wacce ta gan shi sai ta haɗiyi miyau.

Na jinjina kai “Watarana dai ma ga Habibin nan da ko a waya ba a yarda a ajiye hoton shi ba.”

Ta yi dariya “Gobe zai dawo.”

Muka fita wurin yan’uwanta sai da na dan zauna na miƙe na ce zan koma gida
Ta ce haba in bari in mata wuni mana.
Na ce idan na cika daɗewa za ki ga kiran Mami.

Ta rako ni muka rabu a sai ta zo.

Ba ta zo ɗin ba har sai da suka yi sati biyu da dawowa sai dai chatting da muke.

Da yamma suka zo ina daki aka rako ta ta same ni ta zauna kenan ta ce “Tare da Habibi muke na ce “To mu je mu gaisa.”

Ta miƙe wayarta ta yi ƙara sai da ta gama amsawa ta dube ni “Wai Habibi wucewa zai yi in zo in karɓi key na motar da muka zo ciki.”

Na ce “Ok mu je to.

Mun zo falo kiran Baba ya shigo wayata na ce ta je kar ya yi ta jira zan amsa waya a falon na zauna ina amsa wayar a natse karatuna ya tambaye ni da ba wata matsala muna zaune lafiya? Na amsa da duk lafiya lau.

Mun ƙare wayar na bi bayan Ummu hani ganin ta na yi tana shigowa na jira ta ta ƙaraso “Ina Habibin naki”

“Habibi kuma ai kamar ƙamshi yake har ya ƙara gaba wai sauri yake wani fili aka kira shi ya gani.

Na ce “Allah ya tabbatar da alheri. Muka wuce ciki.

Na raka ta ta gaida Mami muka yi ta hira har yamma na ce ba za ta yi girki ba ta ce an kawo mata mai aiki daga Kano.

Na yi mata rakiya ta yi wa Mami sallama sai da ta shiga motar ta bar wurin na koma ciki.

Zainab ta haihu muna tsakiyar karatu ta samu ya mace dole na haƙura da zuwa har sai mun samu hutu san da aka yi hutun tuni ta yi arba’in.

Farha ta zo da kanta ta roƙi Daddy in raka ta garin su Zaria, zan wuce Malumfashi in kwana ɗaya sai in dawo Kaduna in yi kwana biyu.

Gidan nasu yana nan a Kusfa a rukunin tsofaffin gine-gine irin na da, gidan su Farha yake sai dai an gyara shiyyar iyayenta don gida ne na yawa babanta da yan’uwan shi.

Dakin mahaifiyarta muka sauka muka yi kwana ɗaya daga kwana biyun da ta ce za mu yi sai da direban ya kai ni Malumfashi idan ya dawo su wuce Abuja don haka sammako na yi na kwana ma Gwoggona daya na shiga motar haya na tafi Kaduna.

Ban hakura aka kwana ba, a ranar na dangana da gidan Zainab na wuni sai na dawo da na je gaishe da Baba nasiha ya yi ta yi min game da rayuwa, Maman su Ahmad ba ta nan ban same ta ba.

Washegari ma da na tashi shirin na yi ina gaido Baba ya fita kasuwa ni ma na yi ma Mama sallama na koma gidan Zainab yarinyarta Samha ta yi girma muka zauna zaman hira girki ma tare muka shiga kitchen muka yi a ranar na ba ta kayan da na sawo ma Samha, ta buɗe tana dubawa tana faɗin “Ba su yi yawa ba Billy? Na ce “Ɗiyata na saya ma wa.”

Ta ɗaga tirmin atamfa guda da shi kadai ne na ta sauran duk tarkacen Samha ne ta ce “Ni ma ga nawa.”

Na faɗa mata zan je gidan Khadija da wurin Amir. Ta ce gidan ya Najib fa? Na ce ba zan je ba ta yi dariya.

Sai da muka yi la’asar muka fito cikin shiri jin Zainab na ta yabon shiga ta riga da wando irin wanda na sanya ran da muka zo bikin Najib sai farin glass. Na ce “Ina samun kuɗaɗe zan sawo maki irin su my Zee.”

Ta ce “Suna matuƙar yi miki kyau.

Inda Najib ke zaune yana aiki a System ta tsaya ta ce “Mun shirya.”
Ya ce “Ni kam aiki nake.” Ya nuna mata key ta ce “Lallai ma ka san har yau ban gama gwanancewa da hawa titi ba.”

Daga inda nake na ce “Ɗauko mu je.”
Ta ɗauko tana cewa “Allah billy kin koyi driving kin bar ni?

Na ɗauki Samha na yi wa Najib sallama na fita.

Mun ɗauki hanya na ce zan ɗan samu wuri in ɗan duba wa Amir da Khadija wani abu.

Wata Flaza na shiga muka fita bayan wata danƙareriyar mota na parker ta mu ina ce ma Zainab “Motar nan tana bala’in burge ni za a ji dai miliyoyi.”

Ta dubi motar “Baba ya taɓa zuwa da irin ta.”

Na saya ma Amir riguna biyu da takalmi Khadija na daukar mata turare Zainab na duba wani takalmi daga cikin masu gadin wurin wani ya zo ya ce min mu zo mu janye motarmu, mun kare motar wani yana son fita da motar, na ce “Subhanallah.

Na fita da samhat a hannuna ajiye ta na yi na janye motar na fito sai na dauke ta matasa biyu ke tsaye jikin motar da na ce tana burge ni kuma wadda na rufe.

Ina ɗaga Samhat sama na ji an sha gaba na na cira ido don ganin wanda ya min wannan aikin daya daga cikin mazan da ke tsaye jikin motar ne wanda ya bada baya ƙara buɗe idona na yi don tabbatar da wanda nake gani tsaye gaba na “Hassan! Na kira sunan cikin maɗaukakin mamaki “Mai gadon zinare.”

Ya fadi yana sakin wani lallausan murmushi duk da mugun sauyin da na ga ya samu ba ta hanani gane shi ba, Hassan ya canza ya cika ya zama cikakken namiji mai kamala da haiba ga hutu da ya ratsa shi.

Cikin wata ubansun shadda yake wando da riga da malum malum ga wata hula da ta zauna a kan shi take ta sheƙi ƙafarsa baƙin cover ce “Yau wace rana Allah ya kuma haɗa ni da mai gadon zinare ya fadi yana jifa ta da wani irin kallo.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 3.5 / 5. Rating: 2

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Mutum Da Kaddararsa 26Mutum Da Kaddararsa 28 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×