Skip to content
Part 28 of 64 in the Series Mutum Da Kaddararsa by Maryam Ibrahim Litee

Ina kika shiga na kasa ganin ki? Gwoggo ta ƙi yarda in ƙara haɗuwa da ke.”

Na ɗan harare shi “Ya za a yi ta yarda ka haɗu da ni bayan ta san na yi aure.”

Ƙarya kenan mai gadon zinare, ko da Gwoggo ta ƙi in ji komai game da ke na tambayi Bilkisu ta kuma ce min ba ki yi aure ba kina Kaduna kina karatu.”

Kafin in yi magana Zainab ta ƙaraso tana zabga min masifa, sai dai suna haɗa ido da Hassan ta yi turus ta dube ni ni kuma na dube shi “Za mu tafi sai anjima.

Ya buɗe ido “Ki wuce ki bar ni kike nufi? Ai ƙafata ƙafarki mai gadon zinari.”

Ya sa hannu ya karɓi Samha Zainab ta ce “Hassan ko? Na dube ta da mamaki yadda ta gane shi duk da farkon zuwa na akwai hotunan shi sosai a wayata ko kuma jin da ta yi ya ambaci mai gadon zinare da na faɗa mata shi da Babana ke kira na haka.

Shi murmushi ya yi “Ya gida ya yara ? Ta ce “Lafiya lau.” Abokinsa da suke tare ya iso “Malam shanyar da ka yi ta bushe.”

“Yau na ga mai gadon zinare Mustapha.” Ya ce wa abokin na shi Mustaphan ya kara matsowa “Don Allah fa mutumina, yau ranar ta musamman ce gaskiya.”

Muka gaisa.

Na faɗa motar don mu bar wurin ya buɗe ya shiga kusa da ni “Ai ƙafata ƙafarki mai gadon zinare.”

Zainab ta buɗe baya ta shiga abokin ya matso “To ni ya za ka yi da ni? Key ya ciro ya miƙa mishi “Ka biyo mu Mustapha, zan je in ga masaukin mai gadon zinare. Sai kuma ya ce “Mu je dai mu bi su a baya.”

Ya fita Zainab ta shigo na ce “Ni fa da inda zan biya.” Ya dubi kyakkyawan agogon da ke daure a hannunsa “Ba ki da matsala.”

Kurmin mashi muka fara zuwa wannan karon har gidan muka je muka shiga ni da Zainab, suka yi ta ɓarin jiki da mu Maman na faman washe baki ta ce “Yau kam Aminu yana nan, kai ku kira shi yana gida.

A hankali nake magana da Amir wanda yanzu ya san ni ce mahaifiyarsa, karatunsa nake tambayar shi shi kuma yana cewa zai bi ni.”

Abu da na samu a gidan ita ta sheƙa ta kira shi yana zuwa sai na ga jikin shi ya yi sanyi ba kamar yadda a waya yake zaƙewa yana damu na don ko da na rufe shi wasu lambobin ya koma sakewa yana kira na.

Muka gaisa sai na miƙe na ce za mu tafi Zainab ta ba Amir abin da na kawo mishi har da na ta Aminun na biye da mu su Maman shi ne suka tsaya daga kofar gida suna ta godiya ina buɗe murfin motar ya ce “To Haj Bilkisu Allah ya kiyaye hanya sai an kwana biyu.”

Yana riƙe da hannun Amir da ke kukan sai ya bi ni.

Muka tafi su Hassan na biye da mu kamar yadda muka zo.

Gidan Khadijah muka nufa ba mu zauna ba don magrib da ta gabato muka wuce muka sauke Zainab.

Dole na shiga motar Hassan zuwa gida a hanya ya yi min gaisuwar Babana da ya ce ya ji da ya je nema na a Dukku.

Na ce mishi na bar Kaduna yanzu ina Abuja.
Ya ce shi ma abujar yake zaune yaushe zan koma abujar? Na ce “Gobe. Suna sauke ni gida na shiga don sallah da ake ta yi a masallatai.

Da na shiga Mama ta ce “Sai yanzu Bilkisu?
Na ce “Wallahi Mama.”

Da su Ihsan muka zauna muka yi sallah muka ci abinci na je na gaishe da Baba.
A gadona na kwanta tare da Asma’u don sun dawo ɗakin.

Da safe da na fahimci girkin Mama ne na shiga kitchen muka gaisa da Baba Talatu na yi ma Baba da Mama abin karyawa.

Da na je gaishe shi nasiha ya yi min sosai ƙarshe ya sanya min albarka ya kawo kuɗi ya ba ni na koma ɗaki na shiga wanka sai da na gama kwalliya na kunna wayata.
Kamar jira ina sanya ɗankunne bayan sanya kaya kiran Hassan ya shigo ina ɗagawa ƙorafi ya fara min me ya sa na kashe waya?

Na ce “Ba komai.” Ya ce “To ba ya so.” Na ce “An bari.”

“Yaushe za ki tafi?

Na ce “Yanzu haka na kusa kammala shiri.”
“Da zan ɓullo in sake ganin ki mai gadon zinare.”

Na dan murmusa “To ni kam na yi harama, Mamita ta Abuja tana ta jaddada min in taho da wuri.”

Da sai jibi zan bar garin nan, amma saboda ke zan kammala komai a gobe in dawo Abuja.”

Na ce “Allah ya kaimu.” Na sauke wayar na janyo jakata Ihsan da ta shigo ta taya ni daukar jakata muka sauka ƙasa na yi wa Mama sallama duka yaran suka yi min rakiya har wurin motar da Baba ya bayar ya ce a mayar da ni.

Cikakkun awanni biyu suka kai mu Abuja.
Ina shiga falon Mami Ya Safwan na zaune da iyalansa Afnan ta taho da gudu ta maƙale ni na ɗaga ta sama na bata peck muna dariya na isa gaban Mami na tsuguna gaban ta ta shafa kaina “Oyoyo ɗiyata.”

Na gaishe ta na juya na gaishe da ya Safwan sai Farha da ke ta min murmushi.

Tare da Afnan na shiga ɗaki sai da za su tafi uwar ta zo ta ɗauke ta. Zainab Khadijah da Maman su duk a lokacin suka kira ni Najib ne ya kira ni ƙarshe yana min tsiyar in shigo Kaduna in kasa neman shi ko in je gidan shi sai yanzu yake ji.

Na ba shi haƙuri.

Na kira Gwoggona ina son yi mata zancen Hassan da yadda na ga ya kuɗance amma na kasa samun jarumtar yin hakan, don ko su Rahina ina ganin ita ta hana su ba ni labarin shi.

A yammacin washegari sai ga Hassan na shigar da shi har falon Mami ya gaishe ta muka fito harabar gidan muka zauna wani wuri da aka dasa kujeru, na ajiye mishi ruwa da lemo da danbun naman da na yi wa Mami da Daddy.

Ya kafa min ido na ɓata fuska ina karewa da hannuna “Kallon fa? Mamaki nake wai yau ga ni ga mai gadon zinare, har na soma fitar da rai, na cigaba da samun canjin rayuwa bayan rabuwar mu Bilkisu, harkoki sun yi ta buɗe min har na zama yadda kike gani na yanzu, na yi aure sai dai ba mu haihu ba. Ke ma kuma na ga taki rayuwar ta canza, na yi murna ƙwarai da na gan ki cikin kyakkyawan yanayi.

Mun daɗe muna hira har magrib ta kusa wayarsa da ya ajiye kan teburin da ya shiga tsakanin mu ta shiga ƙara a tare muka dube ta, sunan da na gani na sweet heart ya sa da ta katse bai ɗaga ba har kara ɗaukar ƙara ya ɗaga “Ga ni nan zuwa.”

Kawai ya ce ya sauke wayar na ce “Sweet heart ta gaji da jira ta biyo sawu.” Bai ce min komai ba hira muka cigaba har sai da aka kira sallah ya sallame ni ya wuce.

Da na koma ciki sallah na yi sai na iske Mami a ɗakinta ta ce “Waye wannan ɗin? Na ce “Hassan ne.” “To to Hassan daga ina?

Murmushi na yi ina jin nauyin ce mata tsohon mijina ne jin na yi shiru ta ce “Uhumm wane Hassan?

Na ce “Shi ne na zauna da shi a Malumfashi Maman shi ta hana ya zauna da ni.”
Ta yi ɗan murmushi “Allah ya shiryi Bilkisu, ki ce tsohon mijinki, to yanzu mahaifiyar ta shi ta amince tana son ki ya dawo?

Na tabe baki “Wallahi ban san mi shi ba Mami a Kaduna muka haɗu shekaranjiya.”

Ta gyada kai muka fita zuwa falo muka ci abinci.

Tun sake haɗuwa ta da Hassan sai ya zam kowane lokaci yana tare da ni idan baya garin za mu yi waya mutum ne mai yawan tafiye-tafiye yana takura kan shi ya dawo Abuja wani lokacin ma makaranta yake bi na mu dawo tare.

Ina tare da Ummu hani wadda zaman mu gari daya ya sa abotar mu ta ƙara ƙarfi, tana zuwa wuri na ina zuwa gidanta ina iya cewa daga makaranta ba ni da wani wurin zuwa in ba gidanta ba.

Farha ta gaji ta ƙyale ni da nacin rashin son zuwa gidanta ni kuma rashin sakin fuskar ya Safwan Sadaukin Mami ke hana ni zuwa.

Yau ma tun ina hanyar dawowa gida daga makaranta take kira na jin matsalar ta ta kan habibinta ne da Allah bai taɓa haɗa ni da shi ba ya sa na ce ta bari in ci abinci zan zagayo.

Ina kuma gamawa na ce wa Mami zan je gidan Ummu hani.

A bedroom ɗinta na same ta cikin damuwa ina tsaye kanta na ce “Wai me ya faru? Ta ɗago tana duba na “Habibi ya yi budurwa a garin nan Bilkisu, hankalinsa gabaɗaya yana wurin ta na yi imani yanzu saboda ita yake yawan zama garin nan.”

Na zauna kusa da ita na dafa ta “Ki kwantar da hankalinki kar ki sa ma kanki zargi ya hargitsa ki kasa zama lafiya.

Ya aka yi kika gane hakan?

Ta girgiza kai “Wayarsa na bibiya na gane hakan, ta shiga rantsuwa wallahi ba zan bari ba kuma ba zan yarda wata can ta ɗauke min hankalin miji ba.”

Zan yi maganin ta.

Hakuri na yi ta ba ta da ƙyar na samu ta nutsu, na fita na samo mata abinci wurin mai mata aiki ruwa na fara ba ta ta shanye shi tas, ina kawo mata ƙabli da ba’adi ta ci abincin.

Sai yamma na ƙara ba ta haƙuri na koma gida.

Ranar wata Alhamis ban shiga makaranta ba Mami ta ce in shiga kitchen in yi wa ya Safwan girkin sauka don sun je Ibadan ganin likita kan batun haihuwa da har yau shiru babu labarin ta wurin Aunty Farha.

Na fito daga ɗaki don yi mishi sannu da zuwa shi kaɗai ya sauka nan Aunty Farha gidanta ta wuce.

Mai aikin Mami tana shirya mishi abincin da na girka suna zaune a 2 Sitter shi da Mamin.
Na mashi Barka da isowa kafin na samu kujerar nesa da su na zauna ina duba laptop ɗina don gobe muna da gwaji, sai dai kunnena yana kansu ina sauraren labarin da yake ba ta na matsalar su ta rashin haihuwa.

Wai matsala mahaifar Farha ta samu tun a haihuwar ta ta farko amma da taimakon likitocin suna sa ran daga yanzu zuwa kowane lokaci za ta iya samun ciki.

Sai tambayoyi take mishi shi kuma ya yi shiru yana ta aika loma har dai ya ƙare ya ce “Haba mana Mami, kin haɗa ni da daddaɗan abinci kuma kina so in yi magana in dai ba santi kike so in karanta maki ba.”

Mami ta kama dariya ya ce Allah ba zancen dariya ba ne Mamina kin yi sabuwar mai aiki ne?

Mami dai dariyarta take ta yi ya ci gaba da cin abincin shi da ya ƙare ya gogebakin shi ya mike “Zan je gida Mami, don Allah zan riƙa samun abincin nan in riƙa zuwa? Mami ta ce “Hakanan, mutum da matarsa.”

Ya ɓata fuska “Can ɗin ma fa mai aiki ke yi da daddare fa kawai haba mana Mamina.”

Jin ta yi shiru ya san ta amince ya wuce ta bi shi a baya sai da suka wuce ni na saci kallon su.

Wani dare ina ɗakina suka shigo shi da Farha ganin ba ni a falo ta isko ni zaune nake gaban dressing mirror ina goge fuskata, Afnan na kwance kan gadona don dama tana gidan shigowa ta yi tana faɗin “Shi kenan mutum kullum yana ɗaka kamar garar kunya.”

Murmushi na mata ina tambayar ta saukar yaushe? Jingina ta yi jikin mirror tana bin kayan wurin da kallo wata irin dariya ta yi “Saboda Allah Nana kayan kwalliyarki kenan?
Ta fadi cike da nuna gadara a fuskarta.

Fita ta yi a dakin tana ci gaba da da dariyarta mijinta ne ya dube ta “Ke kuma dariyar me kike wa mutane? Wata sabuwar dariyar ta dauka tana faɗa mishi kayan kwalliyata ne suka ba ta dariya.

Daidai tana fadi na fito sai na ji duk na muzanta.

Mami ba ta yi magana ba illa tagumi da ta rafsa, shi kam gogan kamar ma bai ji ba ya yi sai cin abincin shi yake Spoon ta dauka ta sanya a flate din da yake cin abincin ta ɗebo abinci ta kai baki lumshe ido ta yi “Delishious, gaskiya dole honey ka zo gidan Mami cin abinci Ni ma Mami ki riƙa ba shi yana kawo min.”

Mami wadda har yanzu da nuna rashin jin dadi a fuskarta ta ɗaga kai .

Juyawa na yi na koma ɗaki cikin tunanin wai kayan kwalliyata sune abin dariya.

Na daɗe zaune cikin rashin jin dadi a halayen Aunty Farha shi ne bai min ba tana da rainin arziki da ganin kowa bai isa ba duk da ban ga laifin ta ba tana da damar da za ta dauki kanta isassa.

Uban mijinta ya tara kuma komai na shi na mijinta ne shi ma kuma mijin nata yanzu yake kan ganiyar shi bayan harkar wasan polo da yake yi yana kasuwanci na shigo da na’urori na zamani.

Ban mancewa akwai ranar da ta yi min izgilanci kan laptop da ta gani a hannuna “Saboda Allah wannan laptop din kike amfani da ita har ki ce kina da laptop?

Wani takaici da ya turnuƙe ni ban samu ce mata komai ba ban kuma san Mami ta ji ba sai wani dare da ya Safwan ya shigo Daddy ya ce ka zo min da laptop zan bai wa ya ta.

Ya ce ba su da su a ƙasa akwai kayan su masu zuwa za a duba mata ɗaya. Ɗaga mishi hannu Daddy ya yi “Ba kyauta nake so ba saye zan yi don haka duk san da kika shirya Nana Bilkisu, direba ya kai ki ki wurin na su ki zaɓi wadda ta yi miki, na ce to har yau dai ban je ba koyaushe Mami ta min magana sai in ce za ni.
Miƙewa na yi na kwanta kusa da Afnan wadda ta yi nisa cikin barcinta.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Mutum Da Kaddararsa 27Mutum Da Kaddararsa 29 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×