Skip to content
Part 29 of 64 in the Series Mutum Da Kaddararsa by Maryam Ibrahim Litee

Da safe da na tashi na samu wayar Hassan, ya ce ya shigo gari da daddare in jira shi da yamma yana nan shigowa.

Sai na samu kaina da son in yi kwalliya don in burge shi.

Ina dawowa makaranta na ce wa Mami za ni Sallon.

Direba na ajiye ni ya wuce da cewar idan na kusa gamawa sai in kira shi. Kitso aka yarfa min ƙanana da ƙunshi da na ci uban zama har takaici ya rufe ni kar Hassan ɗin ma ya zo ina nan.

Ilai kuwa sai ga kiran shi na ce ina Sallon, address ɗin wurin kawai ya nema a mintocin da ba su wuce talatin ba kuma sai ga shi ya iso, hakan kuma ya yi daidai da kammala min, na biya kudin na fita ina takawa a hankali don gajiyar da na yi ina duban ƙunshin da aka rangaɗa min da irin kyan da ya yi.

Na ɗora idona inda yake cikin wata tsaleliyar mota da ban taɓa ganin shi cikin ta ba shigar ƙananan kaya ya yi da suka yi matuƙar amsar shi.

Na ɓalle murfin motar na shiga na zauna ina faɗin “Barka da isowa.”

Yawwa mai gadon zinare.”

Ya tashi motar yana kallon ƙunshin hannuna, “Ƙunshin nan ya yi kyau mai gadon zinare, sai na tuna wani lokaci can da ya wuce.”

“Uhmmm kawai na ce ina jingina kaina a kujerar motar sai na dube shi ni yake kallo gaba na ya faɗi kai da ke tuƙi mai ya kaika kallon wani wuri ba gabanka ba? A raina na fadi a fili kuma baki na turo “Allah kar ka yarda mu.”

Murmushi ya yi sai ya kalli titi.
Maganganu yake faɗa min waɗanda tun sake haɗuwar mu bai taɓa faɗa min su ba.

Gabadaya ni da shi wani abu ya taɓa zukatan mu.

Da muka isa ya shigar da motar na sauka zan shiga ciki in samo mishi dan abin maraba ya ce “A’a in bari kawai mu yi hirar mu.”
Jikin motar muka tsaya mun soma hira get man ya wangale get ya Safwan bisa dokinsa ya bayyana cikin kayan wasa.

A tare muka kai kallon mu wurin, ya wuce can ciki inda yake ɗaure dokin ya wuce cikin takun shi na namijin duniya ya kusa shigewa ya ƙwala kiran sunan Bilkisu abin sai ya zo min kamar daga sama don ban taɓa ji ya ambaci sunana ba.

Na dai amsa a hankali na nufi inda yake tsaye gabana na dokawa “Wuce ciki.”
Abin da ya ce kenan cikin daure fuska na wuce har ina tuntube ya biyo bayana.

Na wuce Mami tana min maganar kitso da ƙunshin da aka yi min, ban tsaya ba ina tafiya ina amsawa.

Na shige ɗaki na ruho ƙofar.

Kayan jikina na sauya da wata doguwar riga mai guntun hannu da kwalliya a ƙirji na hau gado da wayata a hannu ganin sakon Hassan sai na ba shi haƙuri na ce ya Safwan ya kora ni ciki ka yi haƙuri ya ce “Ni ban ga yaya anan ba ya fi min kama da abokin takara a yanayin shi shi ma yana ciki.

Na ji wani banbaraƙwai to ta ina shi kuma ya samo wannan tunanin?

Sai na kasa ce mishi komai ya turo “Allah ya sa kar su Mami su yi mana son kai, daga yau zan fara addu’a mai gadon zinare.”

Na ce “Ikon Allah.” Kiran Mami ya shigo na ɗaga ta ce in zo hakan ya cece ni daga titsiyen Hassan na ce mishi Mami na kira na.

Gyalen rigar na rufe jikina na ajiye wayar a kan gado na sanya takalmi na fita ina mai addu’ar Allah ya sa Ya Safwan ya tafi, sai dai addu’ata ba ta ci ba don da shi na fara tozali zaune kan kujerar da ke kallon ƙofar da na fito Mami kuma ta ba ƙofar baya na tsinkayi muryarta tana faɗin “Ikon Allah ya za a yi ka hana ta tsayuwa da wani? Kamar bai so ya ce “Ba karatu take ba? In karatun take fa sai ta ƙi sauraren masu son ta? Shiru ya yi na ƙaraso na ce “Ga ni Mami “An dawo an shige ɗaki ba a nuna min kitson da ƙunshi ba, ashe Sadauki ya firgito ki.”

Ni dai na tsaya sororo kamar na kada suruka “Mu ga kitson.”

Ta kuma ce min na durƙusa gaban ta sai dai na gaza cire mayafin da na rufe har kaina sanin ya Safwan yana nan.

Ta ɗaura kaina bisa cinyarta ta buɗe kan tana yamutsa kitson “Ma sha Allah, wadda ta yi ba ƙaramar gwana ba ce ya yi matuƙar kyau.”
Ta kama hannun “Ƙunshin ma ya yi kyau Nanata.” Murmushi na yi ina jan mayafina na rufe kan sai na miƙe kitchen na shiga girki na ɗora na kuma zauna a kitchen ɗin har sai da na gama na shirya komai na ba mai aikin Mami ta fitar mishi da shi ni kuma na zuba ma Mami dama na mutum biyu na yi sai na bi bayanta wani ɗan stool na janyo na ɗora ma Mami na koma na kawo mata ruwa ta ce

“Sannu ɗiyata.”

Ban zauna ba daki na wuce na yi sallah sai na yi wanka don kwanciya nake so in yi da wuri, sai dai kiran Hassan bai bar ni na samu na yi barcin ba mun daɗe har na ce “Madam fa yanzu lokacin ta ne kar a shiga hakkinta, ga shi gobe za ka yi wata tafiyar.”

Murmushi mai sauti ya yi ya ƙi maganar, magana na ji ana yi masa sai ya ce min sai da safe.

Yana katse kiran ni ma na ajiye wayar na gyara kwanciya.

Washegari sai 2pm nake da lacture don haka barcina na sha sai tara na tashi na yi wanka kenan na shirya na fita ina shan Tea kiran Hassan ya shigo in fito mu yi sallama zai wuce Kano.

A gurguje na ƙarasa na fita bai shigo da mota ba na fita zuwa get, tsaye yake jikin motarsa na ƙarasa na tsaya kusa da shi ina mishi sannu da zuwa haɗe da gaishe shi na ɗora da faɗin “Ba ka wuce ba ina ce tuni ka yi nisa? “Ba zan iya wucewa ba ban gan ki ba mai gadon zinare, na so gwada hakan sai na kasa samun jarumtar yin hakan.

Na dan yi murmushi ina gyara tsayuwa “Idan Allah ya dawo da ni akwai magana mai muhimmanci da za mu yi.”

Na ce “Allah ya dawo da kai lafiya ” “Bari in wuce.” Ya faɗi yana buɗe motarsa na shiga jera masa addu’o’i na fatan sauka lafiya ya lumshe idonsa ya buɗe yana yi ma motar key “Na gode mai gadon zinare, suna cikin abin da nake matuƙar kewa a rashin kasancewar mu tare.”

Na murmusa ina ɗaga mishi hannu ya ja motar ni kuma kamar wadda aka dasa haka na kasa cira ƙafata in koma ciki idona na kan motar Hassan har ta ɓace ma ganina.

Zan juya wata motar ta tsaya gabana, mace ce ke ciki wadda ban tantance wace ce ba abin da dai na yi wa kallon tsanaki motar da ta yi matuƙar burge ni don na yi imani ba a ji tausayin Naira ba wurin mallakar ta.

Na tura kofa zan shige na ji an kira sunana na tsaya cak kafin na waiwayo Ummu hani ce na dawo ina famar murmushi “Carkwaɗi, ki ce ke ce a wannan arniyar motar?

Ba ta maida min martanin murmushina ba ballantana ba’ar da nake mata maimakon haka ƙara tamke fuskarta ta yi ta kamo hannuna “Na bani Bilkisu, wallahi habibi aure zai yi kishiya zai yi min.”

Gabana na ji ya faɗi “Ki kwantar da hankalinki don Allah, gaya miki ya yi zai yi aure?
“Sai ya gaya min ni doluwa ce? Jiya ya sawo motar nan ya kuma mallaka min ita, kuma da muka kwanta yake faɗa min idan ya dawo tafiyar nan za mu je Dubai mu yi sati biyu, daga can mu wuce China, shi ma sati biyu, sai mu yi karshe da kasar Saudiyya mu yi Umara.

Na ce “Iye gaskiya na taya ki murna.”
Na bigi kafaɗarta ta goce tana ƙara ɓata rai,
“Tun farkon aurenmu nake rokon ya kai ni Dubai ina son ganin garin ya ƙi, sai yanzu kawai na cire rai. Gara China dama can yake sawo kayan gine-ginen shi.”

Gabana na ji ya buga jin sana’ar mijinta ko dai ko dai?

Na tambayi kaina sai kuma na yi saurin saita kaina ganin tana kallona.

“Uhmm Saudiyya ma ba zan ce don wani abu ba don ko bara mun je har da mahaifiyarsa.”

“Shi kenan, Ummu hani don mijinki ya yi miki alheri sai ki ce aure zai yi, to dama bai kyautata miki sai yanzu?

“Yana kyautata min zaman mu saboda tsananin son da nake gwada mishi da kasancewar shi mutumin kirki mai tsananin biyayya ga mahaifiyarsa ya sa yake kyautata min iya bakin ƙoƙari.”

Shi ne kike mata wulaƙanci matar da ta gwada miki irin wannan son?

Ta yatsina fuska “Ƙyale ta ba don Allah ta yi ba, ina sane don kudin mahaifina ne, don duk cikin su shi ne mai hali shi ma Habibi shi ya jawo shi ya koya mishi sana’arsa har ya kai haka.

Wata faɗuwar gaba na ji ko dai ɗiyar kawun Hassan ce? Sai dai kuma ai ta ce min uwar mijinta tana Kano Hassan kuma maman shi a Malumfashi take am…

Ta katse min tunanin ta hanyar tambaya ta “Tunanin me kike ina magana kin yi shiru?

Na yi saurin wayancewa “Ke ce Ummu hani kike ba ni mamaki…

“Zan tafi Kano yau Bilkisu, jiya na nemi izni ya hana ni, ko bai bari ba ni yau zan tafi.”
Hannunta na kamo da karfi na ce “Zo mu je ciki.”

Na tura ƙofar da dayan hannuna muka shiga ina riƙe da hannun nata har ɗakina cikin sa’a ba mu haɗu da kowa ba.

Da shiga gadona ta haye ta yi ɗaiɗai can tsakiyar gadon.

“Dole in tafi Kano Bilkisu in je in taimaki kaina.

Duk da ban san wane irin taimako take nufi za ta yi wa kan nata ba Ni dai na dage ba ta haƙuri kar ta biye wa zuciya ita kuma tana faɗin ta kuskura ta gane ko wace ce sai ta gwammaci uwarta ba ta haife ta ba.

Jin shigowar saƙo a wayata na kai hannu na ɗauka ina dubawa kuɗi aka turo min yawan kuɗin ya bani mamaki na kira Hassan don daga gare shi ne sai dai bai ɗaga kiran ba, na ajiye wayar na juya kan Ummu hani na cigaba da bata baki har ta ɗan nutsu na fita na samo mata abinci.

Bata tafi ba sai da na yi shirin makaranta muka fita tare.

Ina bisa hanya kiran Hassan ya shigo na ɗaga ina mishi ƙorafin kuɗin da ya turo sun yi yawa, don karo na uku kenan yana turo min su masu yawa haka tunda ya samu nasarar samun acc no ɗi na.

Dariya kawai ya yi “Ki sayi kayan kwalliya yammatana.”

Na yi masa godiya sai na koma tunanina na ko Hassan shi ne mijin Ummu hani, ni matsalar ita ba za ta taɓa fadin sunan mijinta ba haka dangin shi don rashin matsayin da take ba su.
A wayarta ma ba hotonsa ko daya don kishin kar wata ta gane mata shi.

Da na gaji da tunanin watsarwa na yi.

Sai dai ba fama kaɗan na yi da ita ba kan ta haƙura da tafiya Kano sai dai ta waya ya faɗa mata Maman shi da yan’uwan shi da ke zaune gida za su zo gidanta su zauna har su je su dawo.

Ta yi tsalle ta dire ta ce ba su zuwa su zauna mata gida abin da ya ja suka yi kaca kaca sai dai na samu sakon ta ta Whatsapp ita ta wuce gidansu.

Hassan ma daga Kano ya ce min zai wuce Umara.

Ummu hani kuma ta ce min babanta ya sasanta su har ma daga can za su wuce Dubai.
Sosai na ji sanyi gane ba shi ne mijinta ba don shi ya ce Saudiyya ita ta ce Dubai na yi ma kowannen su fatan alheri.

Ni kam shiri nake ta yi na tafiya Taraba in gano mahaifiyata kuɗaɗen da Hassan ya turo min da waɗanda Daddy ke sanya min ya ce in sayi Recharge card nake so in je in ba ta ta ta yi sana’a.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Mutum Da Kaddararsa 28Mutum Da Kaddararsa 30 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×