Da safe da na tashi na samu wayar Hassan, ya ce ya shigo gari da daddare in jira shi da yamma yana nan shigowa.
Sai na samu kaina da son in yi kwalliya don in burge shi.
Ina dawowa makaranta na ce wa Mami za ni Sallon.
Direba na ajiye ni ya wuce da cewar idan na kusa gamawa sai in kira shi. Kitso aka yarfa min ƙanana da ƙunshi da na ci uban zama har takaici ya rufe ni kar Hassan ɗin ma ya zo ina nan.
Ilai kuwa sai ga kiran shi na ce ina Sallon, address ɗin. . .