Kamar in yi banza da shi sai kuma na ga rashin dacewar yin hakan na gaishe shi ya amsa sau ɗaya kamar yadda ya saba jim na yi rashin sanin abin yi "In ba za ki ba in kama gabana, ina da abin yi."
Ajiyar zuciya ta ƙwace min na kama ƙofar baya zan buɗe, wani wawan tsaki ya ja da ya sa na janye hannuna, ya zagaya ya buɗe mazaunin direba ya zauna.
"To za ki ne ko in kama gaba na?"
Muryar shi ta ratsa dodon kunnena gabaɗaya sai na kuma ruɗewa na kai. . .