Skip to content
Part 34 of 64 in the Series Mutum Da Kaddararsa by Maryam Ibrahim Litee

Kamar in yi banza da shi sai kuma na ga rashin dacewar yin hakan na gaishe shi ya amsa sau ɗaya kamar yadda ya saba jim na yi rashin sanin abin yi “In ba za ki ba in kama gabana, ina da abin yi.”

Ajiyar zuciya ta ƙwace min na kama ƙofar baya zan buɗe, wani wawan tsaki ya ja da ya sa na janye hannuna, ya zagaya ya buɗe mazaunin direba ya zauna.

“To za ki ne ko in kama gaba na?”

Muryar shi ta ratsa dodon kunnena gabaɗaya sai na kuma ruɗewa na kai hannu na buɗe na shiga na zauna hannun ko in ce jikina gabaɗaya rawa yake.

“Ya Allah! Na fadi a raina zama na yi kamar me koyon zaman mota, ban taɓa tunanin na taɓa haɗa ido da shi ba wani kwarjini yake min, gam na runtse idanuna hancina na shaƙar daddaɗan turarensa wanda ya haɗu da sanyin AC ya bada wani daddaɗan yanayi me saka nishaɗi.

Wayata ta shiga ƙara take gabana ya tsananta bugu har ta tsinke ban samu kuzarin ciro ta ba ta ƙara ɗaukar ƙara a karo na biyu satar kallon shi na yi tuƙin shi yake cike da burgewa na san shi akwai basarwa don haka na yi ƙarfin halin ciro ta ganin sunan mai kiran ya sa na sa ta Silent Hassan ne. Tunani mai zurfi na faɗa har ban san an iso ba sai miskilallar muryarsa na ji yana faɗin mu ga wayarki gabana ya tsinke me zai yi da wayata jin na yi shiru ban kuma miƙo mishi ba ya ce

“Zan ga in shi ne ya kira ki.” Ai sai na ƙara ruɗewa hannunsa ya miƙo min ba shiri na sanya mishi ya fara duba kiran da aka yi min aljihu ya cusa ta “Daga ke ba ki san girman aure ba da kike waya da wani ƙato shi ya kamata a ce ya sani Sim din duka biyu ya ciro ya jefa a aljihunsa ya kira sojan da ke tsaron get din ya yi mishi kyautar wayata ai kam na manta da komai da nake ji game da shi na fara mishi kuka.

Ya ce kuma in sauka na ƙi sauka sai ya yi horn mai gadin ya wangale get din ya cusa hancin motar ciki sai da ya yi parking ya ce in fita yana da wurin zuwa nan ma ki na yi ya fita ya shiga ciki.

Sai na sauko na bi shi a baya Mami da ke zaune a falo da ta ga yanayin da nake ciki ta ce lafiya ban yi magana ba na fara kuka don ni Sim dina sun fi komai ƙona min rai

Ta ƙara tambayar lafiya na ce “Wayata ya karɓe wani kallo ta mishi “Saboda wane dalili za ka karɓe mata waya.”

Kamar ba zai yi magana cikin miskilallar muryarsa ya ce “Waya take da saurayinta.

Mami ta yi ɗan jim “Ke Bilkisu da wa kike waya?

Na share fuskata da hijab ɗi na “Hassan ne ya kira ni Mami kuma ni ban ma ɗauka ko ya kira.”

To ka ji ba ta wayarta.” “Ni na bayar da ita Mami.

Ta dube shi cikin takaicin abin da ya yin ya za ka bayar mata da waya? To kana fita ka kawo mata wata.”

Ya ce “To Mamina, amma ba yanzu za ta ƙara riƙe waya ba.

Baki ta kama “Ba yanzu ba sai yaushe?
Ƙin magana ya yi ta dube ni daga inda nake tsaye

Shige Bilkisu kin ji ki fito ki zo ki ci abinci.

Na bi umarnin ta na wuce san da na fito ya tafi har kuma a ka kwana biyu bai kawo min wata wayar ba bai kuma ba ni Sim din ba Mami ma da ta gaji ƙyale shi ta yi ta ce in yi haƙuri dole aka daura auren ya bani wata, in duba drawer ɗinta akwai wata waya da aka kawo mata tun farkon fitowar ta ba ta yi amfani da ita ba in riƙe kafin ya ba ni wata.

Na sayi sabon sim na sanya na kira duk waɗanda zan kira don su samu sabuwar lambar.

Na kammala Exam ɗi ta Mami da Daddy suka shirya min sha tara ta arziki in kai wa mahaifiyata ya Safwan bai taɓa ɗaga ido ko kallon arziƙi ya yi min ba daga ina kwana ko ina wuni da nake ce mishi shi ma Mami ce ta yi min magana ya kika daina gaishe da Yayanki Bilkisu?

Har na kai Taraba kukan zuci nake bayan na gaji da share hawaye duk da na yarda da son da Mami take min amma me zai sa ta zaɓa min wannan rayuwar? Ko da ba ta san komai game da rayuwata ta baya ba tunda dai aka ce mata na taɓa aure kuma ya mutu ai ta san ba daɗi zai fito da ni ba.

Ban gane gidan Mamana da na taɓa zuwa ba ta waya na kira ashe ma sun canza unguwa mai motan da na dauko shi na miƙa ma wayar aka yi mishi kwatance.

Wani gida madaidaici shafaffe da siminti su kaɗai na same su a ciki. Murna sosai na yi ganin canjin rayuwar da suka samu na ba Mamana labarin yadda rayuwa ta yi ta juya min, na haɗa ta da Mami ta yi mata godiyar ruƙon da suke min.

Na ziyarci yan’uwan ta da wancan zuwan ban samu na yi ba.

Na ba ta kuɗaɗen da na ruƙo mata ta yi jari daki daya da bangon shi ke ƙofar gida aka fasa window ta waje, aka zuba kayan masarufi da yake unguwar sabuwa ce ba Wasu shaguna ciniki ake sosai ranar da na yi kwana bakwai da yake kwana goma zan yi na ga kira da lambar da ba suna na daga jin muryar Hassan na katse ya kuma kira ban daga ba sai ya turo saƙon kar ta kwana.
Na shigo Taraba Mai gadon zinare, na taho takanas saboda ke, ki bani address da zan iso gare ki idan kuma kin zaɓi ki wulaƙanta ni to zan koma.”

Wani irin sanyi na ji jikina ya yi. Babbar yarinyar mamana mai suna Amina da ta zama budurwa ita na tambaya ta faɗa min na rubuta na tura mishi.

Muna nan zaune a tsakar gida inda muke shan iska ni da ƙannena sai ga wayar shi ya iso.
Hijab na dauko kawai na sanya na fita mamakin inda ya samu sabuwar lambata bai bar ni ba

Tsaye na hango shi da alama mashin ya sauke shi na ƙarasa kusa da shi ina mishi sannu da zuwa komai bai ce min ba sai ido da ya sanya min kafin ya ƙare ya ce

“Kin yi min adalci kenan mai gadon zinare? Ka zo mu shiga daga ciki ka sha ruwa daga zuwa ba ka bari ka huta ba.”

“Kin yi daidai kenan abin da kika yi min , ko ba za ki aure ni ba irin rabuwar da ta kamata mu yi kenan?

Saurin kallon shi na yi muka haɗa ido kafin wani cikin mu ya ƙara magana ƙanena ya iso da sallama ya gaida Hassan sai ya ce Mama ta ce ace baƙon ya shigo ya sha ruwa.

Na ce “To. Tare da daban shi ka zo mu shiga.

“Biyo ki na yi mu yi bankwana in miki fatan alheri da na yi ta kiran ki ki ka ƙi ɗaga wayata, daga karshe ko na kira sai in ji ta a kashe, Kaduna na nufa wurin ɗan’uwan mahaifinki na nemi auren ki ya ce har ya karɓi sadakinki, Zainab da na samu a gidan ta zo muka gaisa ita ta bani sabuwar lambarki kira ta bani sabuwar lambarki.

Allah bai yi zan kara zama da ke a ƙarƙashin inuwar aure ba duk da na kwaɗaitu da hakan.”

Ya yi shiru yayin da yaron ya dawo da kujeru biyu ya ajiye karkashin bishiyar da ke ƙofar gidan, mai bi ma shi na biye da shi dauke da ruwa da lemo.

Muka je muka zauna ni na fara magana “Inna ba ta so na Hassan, ga kuma Ummu Hani da muka ƙulla aminta ba tare da mun san dangantakar mu ba, na hakura da kai ba don raina ya so ba sai don nema wa kaina zaman lafiya.”

Ayya Bilkisu Inna kuma ai yanzu ba wanda ya fi ta son ki dawo tun randa ta gan ki ta ruɗe da in je mu daidaita in dawo da ke da na je kuma na dawo mata da sakamakon zuwan nawa tun ranar take kuka har hawan jininta ya tashi da ta samu a baya bayan nan, don yanzu ba wata lafiya ta cika ba saboda matsalar yaran nan da duk ba wadda ke zaune ɗakinta.

Ta ƙi barin Abuja duk da ba daɗin zama take ji da ɗiyar dan’uwan nata ba wai sai kin dawo ta je ta roƙe ki ki dawo wurina.

Na yi tagumi idanuna suka fara kawo ruwa na tausayin kauna, na rasa mai sona na faɗa wa wanda ko da wasa bai taɓa kallona da sunan so ba.

Take mikin auren ya Safwan da zuwa na nan haɗuwa ta da uwata da yan’uwana ta sa ya kwanta min ya tashi,

Na kwantar da kaina bisa cinyata kuka na yi sosai bai hana ni ba sai da na share hawayena don kaina sai ya miƙo min hankacif na share fuskata.

Murmushi ya yi min na mayar mishi na ce “Bari in shiga in yi maka girki.”

Ya girgiza kai “Ba zan ci komai ba mai gadon zinare, tun jiya na shigo garin nan zan koma masauki ki dai yi ma Mama magana zan shigo in gaishe ta na ce to ciki na shiga na shaida mata ta sha lulluɓi ta tsuguna daga bakin kofa ya shiga ciki suka gaisa ta koma ciki.

Muka koma inda muke muka yi ta hira “Na san na rasa ki kuma na ɗauki ƙaddara akwai wata da muka fara magana a Abuja kwatsam sai kika bayyana hakan ya janyo taɓarɓarewar taren namu, zan koma mata in sha Allah kuma zan aure ta tana da hankali kamar ke ɗabi’unta suna tuna min ke hakan ya ja na ƙara son aurenta duniya ba ta dame ta ba babanta babba ne a Abuja gidan su gidan tarbiyya ne budurwa ce sai dai ta daɗe ba ta yi aure ba saboda karatu yanzu kuma tana aiki a National assembly.

Na so in haɗa ku ku yi zumunci sai dai ban ji kamar mutumin nan zai bar hakan ta faru ba, ina miki fatan alheri mai gadon zinare Allah ya sa albarka a aurenki.

Na share hawayen da ke ta gudu kan fuskata magana ma na kasa har ya tare mai mashin ya dare sai da na daina ganin shi na shiga zaure na sha kukana sannan na shiga dakin ƙannena da muke kwana tare na kwanta kan katifarsu jin shigowar saƙo a wayata bai sa na ɗago ba sai da Amina ta shigo ta ce “Mamanmu ta ce ta duba ni na tashi zaune na ce yanzu zan fito.

Ina duba wayar Alert na gani har guda biyu sai sakon text message daga Hassan ya ce sako na farko gudummawa ta ce, na biyun in bai wa ƙannena.
Na tura mishi saƙon godiya ko nan ma sai da na yi kuka.

Kwanakin da suka biyo baya damuwa na shiga mamana ta yi ta ba ni haƙuri, mun yi maganar Inna keso da ita ta ce kwanakin baya dai ta ji labarinta tana nan a Dukku.

Ranar da zan tafi ni kuka ƙannena kuka haka muka rabu da alƙawarin da Mamana ta yi za ta zo ta yi ma duk waɗanda suka tallafi rayuwata godiya.

Dare sosai na shiga Abuja amma bai sa Mami ta kwanta ba sai da ta jira isowa ta ba dai mu yi wata magana ba sai da safe muka yi kowa ya adana haƙarƙarinsa a makwanci.

Da safe barcin gajiya na yi sai sha daya na fito su Mami sun riga sun karya na haɗo abin da zan ci na dawo kusa da ita na zauna ina karyawa tana tambaya ta yadda na baro su.

Ina kammalawa wani Cup ta miƙo min ta ce shanye gabaɗaya na karɓa na shanye na miƙa mata cup ɗin.

“Maganin sanyi ne.” Ta yi min bayani “Za mu gidan Haj Yar Shuwa mai gyaran amare ta fara gyara ki Bilkisu.”

Kai na juyar ban ce komai ba

Sai yamma muna yin ta don wani magani da ta bani na shafa cikina “Allah Mami magungunan nan sun ishe ni.” Ta ce “Sha dai daga wannan kuma sai gobe.

Na buɗe ido “Au wai da saura?

Ta ce “Sha dai wannan ɗin tukuna ina ɓata rai ban karɓa ba na hango ya Safwan tsaye da ba mu san isowar shi ba ya harɗe hannaye a ƙirji ya sha kwalliyar wani yadi ɗinkin half jamfa me guntun hannu kanshi ba hula.

Mami da ta ga na dubi wurin ta juya “Kai kuma fa za ka iso ka tsaya mana ba sallama?

Ya tako zuwa inda muke sai na sulale na yi daki Mami ba ta ankara ba sai da na kusa shigewa ta ce “Ka ga ka ɗauke min hankali ta gudu.

Ya zauna kusa da ita “Maganin me kike ba ta Mami? Ta ce “Ban sani ba. “Allah ya ba ki hakuri Mamina.”

Ban fito ba sai dare da na gane ya bar gidan.

Washegari da yamma ina cin abinci Mami na taɓa wayarta labarin yadda al’amari ya kasance mana da Ummu hani nake ba ta labari mai aikin Mami ta iso ta ce wata tsohuwa na son ganina.
Mami ta ce “Bilkisu kuma wace tsohuwa ta sani shigo da ita.

Wace tsohuwa zan gani Inna ce Maman Hassan ta zauna tana gaida Mami kamar za ta kifa ta juyo za ta gaishe ni na yi saurin ce mata ina wuni?

Ta amsa tana ta jan gaisuwar kafin ta zarce da roƙona Allah Annabi da darajar iyayena in yi hakuri in dawo ma Hassan.

Mami dai sai kallon ta take cike da ƙullewar kai.

Ganin ta yi rokon ta yi magiya ban yi ko motsi ba ta kama kuka “Ki yi haƙuri ki manta da komai na ga jarabawa na ga sakamako daga ƙuntatawar da na yi miki tun daga ke ban ƙara samun surukar da ta yi min biyayya ba.

Matar Gambo kamar jira take ki tafi rashin kunya sai wadda ta manta yara idan suka tanka ta mijinta ya dawo ya musu rashin mutunci kamar bai taɓa sanin su ba, sai da Hassan ya yi mana gida a birnin Kano muka koma shi ma zama da tashi matar ɗiyar ɗan’uwana gara ma matar Gambon ita har horon yunwa take yi idan na biye mata sai ta raba mana zumunci yadda take yi min kamar ba ta taɓa sanin daga inda na fito ba ni ke hana shi idan zai dauki mataki kanta.

Ki taimake ni ki dawo rayuwar Hassan ga dai kudi da na ya yi amma abin da zai ba mu don mu yi bukatun mu sai sun biyo ta hannunta sai abin da ta ga dama ta bamu ina gudun yin magana ace diyar dan’uwan nawa ma ban bar ta ba.

Ta rushe da kuka “Tunda kika tafi lafiya ta yi min karanci saboda na rasa kwanciyar hankalin iyalina.

Jin ta yi shiru tana rairaya kukanta na ce Inna ki yi haƙuri.”

Ta yi shiru tana share hawaye na dubi Mami duba irin na neman agaji sai ta amsa

“Ki yi haƙuri Baba Bilkisu dai an riga an karɓi sadakinta aurenta saura sati biyu in sha Allah. Allah ya haɗa ɗanki da wata tagari.”

Kamar ba ta gane ba ta shiga magiya wa Mami Mamin ta mike mai aikinta ta iso ta dubi Inna “Baba wannan baiwar Allah da kike wa magiya ɗanta ne zai auri Bilkisun.”

Cak Inna ta tsaya da kuka da magiyar ta mike dama Mami har ta kusa shigewa ciki Inna ta yi waje tana goge fuska.

Ni dai nan inda nake na daskare ina ƙara girmama kudirar Ubangiji yau duniya ce ta koya wa Inna karatunta da ma Inna za ta yi nadama?

Lallai abin da ya ba ka tsoro watarana shi zai ba ka tausayi.

Kiran da Mami ke yi min na mike na nufi ciki magungunan da ta saba ba ni ta haɗa sai kuma da na shanye a gaban ta ta bar ni na tafi.

<< Mutum Da Kaddararsa 33Mutum Da Kaddararsa 35 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.