Haka zama na ya cigaba a gidan Aunty Farha, zan yi girki na safe da dare a kullum saboda ya Safwan, gyaran bedroom dinshi ne sai ranar kwana na nake gyarawa zan yi kwalliya irin wadda na ga dama in fito abu na, har na cika wata ɗaya.
Ranar da na cika watan ina zaune a ɗakina da daddare ina rubutu da wata Malama ta samu rubutun kuma yana da matuƙar yawa tunda na yi Isha'i nake zaune.
Ƙarar wayata da ke gefena na ji sai na kai hannu na ɗauko ta na kanga kunnena "Me kike yi. . .